Daudar Gora Book 2 Page 59
“Bana bukatar sanin wanda ya ajiye su balle dalilin ajiye sun. Sai dai zan gargaɗi mai ajiyewar da abu uku. Eshaan a koda yaushe yana zagaye ne a cikin kariyar UBANGIJINSA insha ALLAHU. A komai na ina amfani da zuciya ne fiye da ƙwanji na da ƙwaƙwalwa. A kuma duk sanda maƙiyi ya sokeni ta baya sunansa matsoraci a wajena, jarumi gaba-da-gaba yake zuwa filin daga in har ya cika sunansa jarumi. Saboda haka, idan har ya shirya na bashi tabbaci ɗan Haysam bin Abdul-majeed Aliy Qutb a shirye yake shima”.
A take falon gaba ɗaya ya ɗauka kalmar neman afuwa da fatan hucewar zuciya ga Shahan-shan. A baɗini kam baka jin komai sai bugun zuciyoyi, yayinda ake ma juna ƴar kallon kallo, dan ba ƙaramin ratsasu kausasan kalaman Tajwar Eshaan ɗin suke ba, duk da a zahiri shi ya yisu ne cikin sanyin nan nasa mai amon nutsuwa da cikakkiyar ƙasaitar tabbatar da shi ɗin wanene.
Ƙananun maganganu ne suka nema fara tashi kowa na ƙoƙarin son ganin ya kare kansa. Yi yay kamar bama jinsu ya ke ba, sai da Sayeed Fayzul-haq ya fargar da su sannan falon yay tsitt. Wani ɗan ƙyamusashen tsoho da suke kira Sayeed Tasadduq-Husain da fuskarsa ke nuna alamun ɓacin rai ya dubesu cikin ɗacin murya, a karo na farko da tun shigowarsa falon yay magana. Shima ɗin kamar Uncle ya ke a wajen Tajwar Eshaan, mutum ne mai tsananin tsage gaskiya a duk yanda tazo shiyyasa bai cika farin jini a wajen su ba, alokuta da dama idan yaga an dabaibaye rayuwar Tajwar Eshaan da yawa yakan nuna ɓacin ransa har ya faffaɗi maganganu masu ɗaci, to a yau ɗin ma tin ganin waɗan nan kayan sirkullen ɗazun ya nuna takaicinsa, hasalima shine ya ingiza Sayeed Fayzul-haq kan Tajwar Eshaan ya tarasu ayi maganar kar a wani rufe, gara wanda ya ajiye abubuwan ya san an san ya ajiye ɗin…..
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (30)
……….“Ƙoƙarin kare kai bashi zai fidda kowanne mu ba, duk da bazai yiwu ace dukanmu anan ne muka aikata ɗin ba, sai dai dole duk ma wanda ya aikata a cikinmun yake dai. Shin wace irin rayuwa ce muke son ta cigaba da yaɗuwa a wannan zuri’ar tamu
ne bayan kasancewar mu jini ɗaya?. Shin mi muke nema wanda UBANGIJI baiyi mana shi ba? Mi muke buƙata da ga siffofin shugaba na gari da ALLAH bai azurta bawan ALLAHn nan da shi ba da a kullum muke son nuna bore da hukuncin ALLAH? Ni na rasa gane mi duk mai ƙoƙarin assasa fitine-finen nan ke buƙata ba ko san zuwa. Shin mulkin yake so ne? Ko kuwa rayuwar wannan bawan ALLAH da’a kullum alkairinsa ke zagaye da mu..” takaici ya saka hawaye ziraro masa. Handkherciff yasa ya share tare da sake dubansu ya cigaba da faɗin, “Shike nan babu mai hana koma waye yin yanda ya ke so, sai dai ya sani a duk randa yazo hanunmu wlhy ko shi waye a cikinmu sai yayi dana sani da nadamar kasancewarsa cikin zuri’ar mu. Sannan tarihi zai masa tanadin da bazai taɓa goge sunansa ba a matsayin azzalumi mai fuska biyu a cikin zuri’ar mu. Wannan faɗan ba nashi bane namu ne, dan mu nan da mu akeyi ba da shi ba, dan haka duk wanda ya shirya bismillah muma mun shirya”.
A zahirance duk nuna goyon baya a kan maganarsa sukai, sai dai a ransu ji suke kamar su shaƙo wuyan Sayeed Tasadduq-Husain ɗin. Yasan da hakan, shiyyasa ko kallo babu wanda ya ishesa a cikinsu, ya kuma ci dubu sai ceto. Miran Arshaan da gaba ɗaya ya ke jin kamar ya danne Sayeed Tasadduq-Husain a wajen ya masa yankan rago ya taushi zuciyarsa da ƙyar, dan wannan wata dama ce a garesa, rashin ganin Miran Jasim a wajen yay masa da ɗi, dan haka ya miƙe cike da dakewa da tsan-tsar iya makirci shima ya fuskancesu ya zuba kausasan kalamai, da ga ƙarshe ya rufe da faɗin, “In ma tsoro da kunya sun hana duk ma wanda ya aikata ɗin zuwa nan batare da mun farga ba to na tabbata akwai mabiyansa da irinsa anan ɗin, sai su isar da saƙonmu na tabbatar da duk randa mutum yazo hanunmu sai ya yabama aya zaƙinta a wannan masarauta kamar yanda Sayeed Tasadduq-Husain ya faɗa”.
Kalamansa kam tabbas sun saka wasu fara hasaso abinda yake son dama ai hasashen, sai dai babu wanda ya furta a zahirance aka cigaba da tattaunawa.
Ya ɗauka tsahon lokaci da su a falon suna tattaunawar, dan suna fitowa da ga zaman ma masallaci suka zarce sallar la’asar. Bayan an idar ya koma sashensa. Bai nema Iffah ba yanzun kam. Dan yana buƙatar ɗan hutawa saboda yau zai ɗanyi fitar dare ta sirri zuwa cikin gari. Sai dai koda ya shiga ɗakin ma sai yaji baida buƙatar kwanciyar saboda ransa a matuƙar ɓace ya ke har yanzun. Tashi yay ya canja kayansa cikin wasu fararen wando da riga tas na kamfanin *Nike* da sukai masa matuƙar ƙyau duk da ya sane badan kwalliya ba. Takalma ya ɗaura a ƙafarsa baƙaƙe ya ɗauka p-cap a hannu ya fito cikin takun nan nasa mai tabbatar da shi ɗinne dai ko da ga nesa. Cikin sauri amintaccensa ya miƙe ƙansa rissine, ba sai yace masa ga abinda yake buƙata ba, kai tsaye ya fahimci inda suka dosa. Kafin ya ƙaraso gareshi yay saurin ɗaga waya yay kiran sarkin barga. Ana ɗagawa yay saurin bashi umarnin shirya dokin amana da kowa ya san in ba shi ba Shahan-shan ɗin baya hawan kowanne doki a gidan. Wayar ya katse dan dai-dai da isowar Tajwar Eshaan ɗin, ganin ya nufi elevator batare da ko kallon inda yake yayi ba shima ya zabura. Cikin sauri ya danna floor 1 bayan ƙofar ta maida kanta ta zuge.