Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 6

Sponsored links

A safiyar basu sami damar barin masarautar ba zuwa ga Barbushi kamar yanda sukaso saboda zuwan baƙi. Sarakunan ƙasar ruman gaba ɗaya ne suka sake zuwa domin ƙara duba jikin Tajwar Eshaan. Inda wannan dubiya ta bama al’ummar ƙasar ruman damar sanin yanayin jikin Shahan-shan ɗin. Dan Alhamdullah har fitowa yay falon da akai musu masauki. Yayi zaman kusan mintuna talatin da su, lokacin da yake miƙewa domin komawa kunnensa ya riski matsananciyar hayaniyar da ke ɗan tashi sama-sama kamar daga wajen masarautar. Da farko baiyi mamaki ba, dan tunanisa har yanzu waccan zanga-zangar ba’a dainata ba. Sai dai ya ɗan dakata daga yunƙurin barin falon ya kai dubansa Sayeed Fayzul-haq daya jagorancin shigowar sarakunan garesa. Cikin sauri ya matso garesa kansa a risine cike da girmamawa.

“Amincin da kariyar UBANGIJI su cigaba da gadinka ya adalin shugabanmu ko ana bukatar wani abu ne?”.

Shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya nisa a hankali tare da ɗan lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kansa. A kan lips ɗinsa ya furta, “Akwai abinda ke faruwa ne bayan wanda na sani?”.

 

“A sani na dai babu wani sabon abu, sai dai idan akan waccan hayaniyar ne ƴan jarida ne ke cike da nacin son sanin yanayin jikinka kamar yanda al’ummar ƙasar ruman ke ƙulafuci suma. Duk da kullum cikin jeren zuwa suke ƙofar masarauta dama, amma yau ganin baƙi suke tunanin zasu sami abinda suke so shine suka taru fiye da kullum. Shine jami’ai ke ƙoƙarin hana dukkan hanƙoramsu ta hanyar sake tsaurara tsaro”.

“A tara taron manema labarai zanyi magana da su zuwa gobe Insha ALLAH”.

A firgice, a razane, a kuma ɗimauce Sayeed Fayzul-haq ya ɗago batare da ya farga da abinda yay ɗin ba. Dan wata irin saukar tarnatsa kalaman Tajwar Eshaan ɗin da suka fita a bazata sukai a cikin kunensa. Tabbas bashi kaɗai ba ga duk wanda zaiji dolene al’amarin ya firgitar da shi, dan abune da bai taɓa faruwa ba kai tsaye kamar haka a ƙasar ruman. Koda Shahan-shan nada buƙatar ganawa da manema labarai sai dai ya wakilta waninsa bisa umarninsa ya tattauna da su da yawunsa. Amma duk da Tajwar Eshaan ɗin bai fito yace shine zai tattauna da su ɗin ba a yanzu Sayeed Fayzul-haq ya girgiza ƙwarai matuƙa.

 

A cikin abinda bai wuce awa guda ba wannan saƙo na Tajwar Eshaan ya shiga karaɗe lungu da saƙo na ƙasar ruman da kewaye. Ko’ina ka leƙa zancen da ake kenan Tajwar Eshaan zai zauna da manema labarai a safiyar gobe insha ALLAHU. Kowa burinsa gari ya waye kawai, ba ƴan jaridar ba ba talakawan ba, hatta da manyan ƙasar ma masu manufofi daban-daban sun shiga jerin masu jiran.

A daren shugabannin ƴan jarida na ƙasar ruman suka buƙaci zama na gaggawa, dan dolene su tattauna abinda ya dace kasancewar akwai tambayoyi fal zukatan al’ummar ƙasar ruman da ke son a amsa musu, kuma daga bakin Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed suke buƙatar ji duk da basu da tabbacin samu saboda abune mai matuƙar wahalar gaske kowa ya sani……

Hankali a tashe suka iso ga Barbushi. Duk da tsalawar dare da na duhuwar jejin babu alamar tsoron abin cutarwar tattare da su saboda bushewar zukata. Hasalima su ba abinda zai basu tsoro anan bane damuwarsu. Wanda ya wuni basu tsoro da zama cikin wasi-wasi na rashin makamar riƙewa ne matsalarsu. Boka Barbushi da ƙazanta da dattin kafirci yay ma fuskarsa da gangar jikinsa ƙawanya ya tuntsire da wata irin mahaukaciyar dariya da sai da ta ƙular da Miran Arshaan da Miran Jasim. Sai dai basu nuna ba balle damar cewa wani abu. Sai da yay mai isarsa kafin ya tsagaita da maida hankalinsa garesu. Basu da matsala akan faɗin abinda ya kawosu, dan sunyi imanin ya san komai hatta gaibu (wa’iyazubillah 😭🙏), sakamakon idan sun zo wajensa tun kan su faɗi abinda ya kawosun shike zayyane musu. A yanzun ma dai yana rufe bakinsa daga dariyar tasa ya fara zayyano musu….

“Sarƙa-sarƙar sarƙaƙiya ce mai cike da mugun ƙullin dake ɗaure da kowa. Babu mai iya gane tushen farawarta balle kamo bakin zaren ƙarshenta kasanwar anyi komai a cikin duhun da idanun kowa bazai gani ba ko wanene shi a hatsabibanci. Ina mai tabbatar muku shi ɗin hatsabibi ne ƙwarai da gaske. Kuma tabbas a yanzu ne aka fara wasan hhhhhhhh!!!! Hahahahahahaha!!!!…”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button