Daudar Gora Book 2 Page 47
Komai ya ƙara kwaɓema ta-ƙurya, ta rasa wace hanya ya kamata tabi dan ganin wannan aure ya ƙullu tsakanin Shahan-shan da yarinyar da sai a yau ta saka amintaccen bawanta bincike a kanta. A ɗan gefen ga jami’an gidan sun mugun duƙufa domin gano wanda yay tsaurin idon ɗaukar Zawjata-
almilk daga kurkuku zuwa cikin pool har da kashe jami’an dake tsaronta. Da zafi-zafi suke aiki a wannan yini dan Tajwar Eshaan ya basu kwana biyu ne kacal. Sunko duƙufan matuƙa, domin umarnin mai gayya mai aiki ba abin wasa bane a garesu.
Tasan amintaccen hadimin nata shi a karan kansa bai san ita ɗin wacece ba, dan bayan muryar da take masa magana da ita a duk sanda zata sakashi aiki babu abinda ya sani tattare da ita kuma. To ko muryar ma ai bada tata ta ainahi take masa maganar ba. Sai dai duk da wannan tsaron data tabbatar tana da shi bata kasa jin wani ɓurɓushin damuwa ba a ƙasan ranta game da tsananta binciken. Ga Uwa tai mata alƙawarin bazata taimaketa da komai ba a wannan gaɓar, acewarta shine hukuncinta. Ta tsani yarinyar nan, tsana irin wanda batajin ta taɓa yima wani mahaluki irinta a rayuwa. Bata taɓa fuskantar tangarɗa a aikinta ba sai da yarinyar ta shigo rayuwarta. Matsala bata taɓa shiga a aikinta ba sai da yarinyar ta shigo masarautar. Tabi hanyoyi da yawa domin ganin bayanta amma ko gezau. Ta rasa wane kalar shegen taurin kai yarinyar ke da shi. Ita zuciyarta ta fara bata ma anya yarinyar ba shugabar wata ƙungiyar asiri bace mai zaman kanta? Dan abubuwan da ke faruwa a kanta sun fara bata tsoro. Sai dai taci alwashin kota halin ƙaƙa ne sai ta shafe babin rayuwar yarinyar da kaf zuri’arta a duniya nan bada jimawa ba. Wannan alkawarin ta ne……
Fuska cike da murmushi yake duban kayan surkullen da boka Barbushi ya basu. Cikin ƴar dariya-dariya ya dubi Miran Arshaan da shima a kallo ɗaya zaka fahimci nasa nishaɗin. “Idan ya isa shi hatsabibi ne a wannan karon ya tsallake mana, ai idan yasan wata bai san wata ba damu yake labarin da ga shi har ƴar iskar yarinyar tashi”.
Ƴar dariyar shima Miran Arshaan ɗin yayi, cike da nishaɗi ya ce, “Sai dai uwarsa Bushirat kuwa ta haifi wani amma ba madadinsa ba. Tunda taƙamarsa taurin rai sai mu bisa ta hanyar da zai laushi ta dolen dole da ƙaniyarsa. Shegen yaro kamar jinin aljanu da ga shi har ƴar ƙaniyar yarinyar”.
“Kona ifiritai ne wannan karon dai tasu ta ƙare. Dan haka a daren nan na yau zamu saka komai a inda ya dace kamar yanda Barbushi ya bada umarni. Dan ubansu badai sunƙi mutuwa ta sauƙi ba, to ga rayuwar yayita sai dai a cikin ƙunci da baƙin ciki da ga shi har duk wani mai iya jin zai bashi kariyar.”
Dariya suka sheƙe da ita har da tafawa kamar wasu abokai. Kafin su miƙe cikin ɓadda kamar da suka gama shiryawa suka nufi fada yanda boka Barbushi ya basu umarni…..
Kamar yanda ta saba farkawa akan lokaci domin gudanar da sallar asubahi yau ma bata makara ba. Sai dai saɓanin ko yaushe yau a firgice ta farka. Da sauri-sauri ta ke karanto addu’ar tashi da ga barci tana faman waige-waige a ɗakin mummunan mafarkin da tai a daren jiya da ya sake maimaita kansa gareta yanzu na sake dawo mata. Sosai take jin zuciyarta na tsitstsinkewa, dole taja jikinta ta maƙure kanta a fuskar gadon tana mai naɗe jikinta da son riƙe rawar da yake yi bakinta na ambaton sunan ALLAH kamar yanda kaka ya horeta da daina ihu a duk sanda tai mafarki makamantan hakan saɓanin da da take ihun. Ta ɗauka tsahon mintuna shida kafin ta ɗan samu nutsuwa.