Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 3

Sponsored links

Wata shegiyar dariya ya saki idanunsa kan takardar da aka aiko masa ta sake zaman shari’ar yau. Ya kai hannu ya yarce ruwan wankan dake kan goshinsa zuwa fuska. Tun safiyar jiya basa gidan shi da Miran Jasim. Sai yau ne shi yake dawowa Miran Jasim kuma da daddare.

 

 

 

Wayar landline dake gefe gadonsa ya dauka,yay yan danne-danne yana da ga tsayen da yake. Ana dauka ya kwashe da dariya, sai kuma ya kai zaune a bakin gado. “Yaya dai kawun mai sharia kaima an kawo maka takardar ne?”.

 

 

 

Wani irin shegen tsaki Miran Jasim yaja da ga can. Ya ce, “Bar wawa dan wahala mana. Shifa gani yake kamar ya wani kai anan. Muje zuwa idan ya isa sake zaman wata shari’ar da ga wannan. Zamuyi maganinsa ne shida shegiyar yarinyar nan mai bakin akkunaye”.

Sake kwashewa da dariya Miran Arshaan yayi, tare da fadin, “Ai boka dan gurguzu yayi,tunda muka fita muka dawo masarautar nan babu wani shege da yay magana shima bai isa

yinta ba yau”.

Yau kam a tare suka fito zuwa dining room. Amintaccensa ya zube kansa a kasa yana gaishesu cike da girmama. Iffah ce kawai ta amsa masa cikin kulawa. Gogan nata kam lips kawai ya motsa ya wuce abinsa. Da kansa ya ja mata kujera, itama sai ta ja masa tana kallonsa da murmushi. Shi dai bai murmushin ba, amma ya juya idanu cike da salon birgewa. Koda amintaccensa ya taso domin hada masa abinci kamar yanda ya saba dakatar da shi tai. Sai ma ta sallamesa akan yaje idan sun kammala sai ya dawo.

 

 

 

Sai da ta gama bubbude duk kwanikan wajen sannan ta kallesa alamar mi yake so? Kaifafan idanun nan nasa ya zuba mata, sai kuma ya daga yatsarsa manuniya a hankali ya nuna ta.Baki ta tura gaba tana wani kyaf-kyaf da idanu.”Ni abinci nace fa”. Yanda tai din sai ya bashi dariya. Amma sai ya gimtse abarsa ya dauke kai Itama sai ta tabe baki ta dauke nata kan dan ta fahimci yau kuma yan mislinacin ne da mulki a kansa. Zabar abinda taji tana so a ranta tai kawai ta zuba musu ta ajiye komai gabansa da fadin bismillah. Abincin kawai ya zubama ido yana jinsa wani daban yau din. A da sai daiamintaccensa ya hada masa, yau kuma gashimatarsa ce, abinda ya jima yana mafarki. Rayuwa kenan mai farko da karshe.

 

 

 

A nutse suka fara cin abincin, Iffah na satar kallonsa da jinjina mulki da kasaita. Yanda yake cin abincin ma kansa abin birgewa ne. Suna gab da kammalawa kanta yay wani irin sara mata. Da sauri ta kai hannu ta dafe tana ambaton sunan ALLAH. Kallonta yay shima da mamaki, sai kuma ya riko hanunta da ta dafe kan da shi. Dago idanunta da sukai wani irin jajaja cikin kankanin lokaci tai ta kallesa. Shi har sai da ma yaji tsigar jikinsa ya tashi, amma sai ya dake kasancewar shima akwai nasa abebadan a kansa. Da ido ya mata alamar minene? Dan da gaske yau miskilancin ne a kusa. Ji yake motsa lips din ma yay magana babban aiki ne.

Ya fada a fusge. “Da safen nan ne fa. Amma ba wani ya matsa bane karka damu. Dan ALLAH ka barni na fara tafiya kotun nan sai kai kuma ka taho da ga baya”.

 

 

 

Idanu kawai ya tsira mata. Ita kuma ta langabe kai gefe alamar roko. Dauke idonsa yay kawai da ga kanta batare da ya ce komai ba. Ya lima yana zargin akwai junnu a jikin yarinyar nan, yanzun ma kuma abinda yake zargin kenan. (Ya arrahaman, komai na yarinyar nan sake sakashi a rudani yake). Sai kuma maganar data fada masan yanzu ta shiga masa kaikawo a rai. Ya barta ta fara yin gaba kafin shi na nufin akwai wani abu kenan. Shikam yaga takansa da wadan nan ahali nashi. Wani abu kenan wani ya sake masa ko kuma dai aljanun nata ne ke neman raina masa hankali. Cikin rashin bama abin muhimmanci ya cigaba da cin abincinsa, sai dai kuma abinda ta fada kuma ya faru a wacan ranar na masa kaikawo. Iffah dake binsa da kallo kamar zatai magana sai kuma ta hadiye kayarta tana sakin nannauyar ajiyar zuciya da jan jikinta

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button