Daudar Gora Book 2 Page 24
Nanma shiru kamar bazai amsa ba, bayan shuɗewar wasu mintuna kuma sai ya motsa. “Kotu ta gamsu da roƙon, sai dai bazata iya bada belin wadda ake tuhuma ba har sai an samo wani haske koda ƙanƙani ne da ga abinda ta faɗa ɗin. Za’a iya sake nema a zama na gaba”.
Daga haka ya miƙe abinsa cike da ƙasaita yana takun nan nasa na izza da bajinta. Dole kowa yay ƙasa da kansa har sai da ya fice sannan kowa ya ɗago. Iffah da ke jin ana kallonta ta ɗan ɗago kanta, ilai kuwa idanun Miran Arshaan da Miran Jasim ta gani na kallonta kamar zasu faɗo. Wani irin shegen makirin murmushi da ya nema wantsalo zukatansu waje ta saki tana mai kanne musu ido ɗaya da musu wani irin salo da yatsunta uku ta ɗauke kanta. Dan jam’ian dake tsare da ita sun zo tafiya da ita za’a maidata kurkuku.
(Wannan ƴa ta Babiy dai to sai ta sa anyi farfesunta a daular ruman
Har karo suke da juna yayin tafiya tsabar fita a hayyaci. Da ƙyar suka iya ƙarasa kai kansu falon Miran Jasim da ya zamar musu mahaɗar tattauna matsalolin su.
“Tabbas kasheta zanyi, da hannuna kuma zan kashe matsiyaciyar yarinyar nan a yau”.
“Da hakan mizai hana kaje kace masa kai ne kawai ka bada madarar”. Miran Jasim ya faɗa cikin tsananin ɓacin rai yana wurgama Miran Arshaan da yay maganar farko harara. Shima a harzuƙe ya dubesa. “To mi kake so muyi ko jira? Kai a tunaninka wannan yarinyar mai kama da agwagwar ƙwa-ƙwa ta ƙi bayyana sunanmu ne danta rufa asirinmu? To ka dawo hankalinka idan ma ya suɓuce maka ne. Dan tarko ta kafa mana, tarko na talala garesa da bama mu ba hatta iyayen da suka haifemu sai munyi dana sanin zuwansu wannan masarautar. Ban taɓa sanin tsagerancin ƴar iskar yarinyar nan ya kai haka ba.”
Miran Jasim ya saki murmushi yana dafa kafaɗar Miran Arshaan. “Akwai abinda ta taka ne, amma zamu sauke mata shi ta yanda ya dace. Zamu tabbatar mata da mu iyayen iyayenta ne a wannan fanin na makirci. Ina son ka kwantar da hankalinka Akhi, ba ita ba, hatta shi mai yanke hukuncin anzo gaɓar da…..hhhhhh”. Ya ƙare da ƙyalkyalewa da dariya batare da ya ƙarasa ba.
Cikin kallon kai mahaukaci ne Miran Arshaan yaja guntun tsaki. “Na kwantar da hankali fa kace? A gaɓar da nake hango cikar 99days ɗina kake tunanin kwanciyar hankali a gareni. Jasim kanka kawai ka sani a hatsabibanci, dan haka kar kai sakaci da ɗan hakkin da ka raina, dan shike zama RAINA KAMA KAGA GAYYA. Da ganin idon wannan tsinanmiyar yarinyar kai ka san akwai abinda ta taka. Nama fara zargin shegen yaron nan ba yana tare da ita bane kuwa?”.
Kalaman Miran Arshaan sun sanyaya jikin Miran Jasim da alama, dama can ƙarfin haline kawai. Yaja numfashi mai nauyi yana jinjina kansa. “Hakane Arshaan, amma ina son ka fahimta kasheta ma kai tsaye ba abune mai sauƙi ba. Dan bazasu taɓa iya sakaci da bata kariya ba kamar yanda munafukan tsohuwar can ta ambata. Damar da ke garemu kawai a yanzu shine komawa wajen Barbushi. Shine ya kamata ya mana wannan aikin”.
Jiki a saɓule Miran Arshaan ya jinjina masa kai shima alamar gamsuwa…..
Duk yanda yake yaƙi da murmushin a karo na babu adadi ya gagara nasarar dakatar da shi bayyana a kan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. Akan dole dai ya sakeshi tare da lumshe idanunsa. “Fitinanniya”. Ya faɗa a hankali da sake nutsa kansa cikin lallausar kujerar da yake zaune.
*_(Kai malam baka san darajar mutane bane?….)_* Kalaman da suka zama na farko a haɗuwar farkon da bazai taɓa iya mantawa ba domin rubutattu ne a sashen da baya goge muhimman abubuwa suka dawo masa kamar yanzu take furtasu. *_(Ka kusan bige yaro amma tsabar kanka ba’a dai-dai yake ba shine koka fito kaga yaya yake ma saboda ku masu kuɗin nan ɗaukar talaka kuke baida banbanci da titin da kuke gurza tayoyin banzayen motocinku da kuka saya da kuɗinmu”). (“Anƙi a bakun, wlhy duk sai kun fito kun dubashi kun bama kakarsa haƙuri zan baku key ɗin nan, inba hakaba sai dai mu kwana anan.”)._*