Daudar Gora Book 2 Page 169
“K! Babbar dakikiyar da ALLAH ya halitta domin zama makamashin wutar jahannama in har bata tuba ba!!!!'”. Iffah ta katseta a tsananin tsawacen da har sai da ta zabura acikin kujerar tsafin nata. Cikin rufewar ido da nunata da dan yatsa ta cigaba da fadin “La’ananniya gatalalliya butulu. K! Har wacece da kika isa samar da koda halittar kwarkwata tsinanniya mai kwana da tashi da tsinuwar UBANGIJI tattare da ita.Why wihy ina miki gargadi na karshe, da ga yau idan
kafarki ko wanna kujerar tsafin naki ta sake rabar inda nake sai na sabauta miki rayuwa. Sai na miki kisan gilla irin wanda ya kamata ama mushirikai batattu irinki a doron kasa”. Ta wani irin rarumi wani dunkulallen abun fulawa na tangaran irin mai tsananin kaurin nan bakinta da bismillah ta wulwula sai gashi ya tarwatse a saman fuskar Uwa. Yanda kasan ta jefa wuka mai kaifin masifa ko mayen karfe sai ga hancin uwa a kasa ya gundulo gaba daya namansa. Dama gashi katon gaske mara fasali. Wata irin gigitacciyar kara uwa ta fasa jikinta ya hau kakkarwa ta dafe fuskar da tai faca-faca da jini da duka hannayenta biyu. Wani Iffah ta sake rarumowa, tana ambatar bismillah kafin ta wulwula uwa ta bace kamar walkiya, sai hancinta da digo-digon jininta da ya faffalatsa kasan harma da bango. Bata fasa wulwulawa ta jefa ba sai ko a keyar uwa da ke kokarin ficewa ta jikin bango ta salon tsafinta.
“Karamar yanyan ki tsaya mana, ki tsaya kiga yanda ake jifan shedan a zahirin rayuwa”,. Ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ke kumbura da cika da batsewa ba da. Sai da tayi mai isarta harda fadawa gado. Sai kuma ta dan dafe kanta dake mata ciwo har yanzu. Dai-dai nan akai knocking kofar, damar shigowa ta bada dan tasan hadimarta ce. Ita dince kuwa dauke da madaran da ta saka a dafa mata. Cikin girmamawa ta ajiye a inda ta nuna mata. Kafin ta bata umarnin gyara wajen da jinin uwa ya faffalatsa, sai dai abun mamaki yanzu babu bantalen hancin uwar da alama dai ifiritan aljanunta sunzo sun dauke..
Kamar wadda aka wurwuro kwallo da ga nesa haka ta fado da ga ita har kujerar tsafin nata a tsakkiyar wasu irin bakaken bukkokin bamboo da ke a jajejin. Firgitaccen ihunta da gumzar azabar da take yasa dajin amsawa, kamar busa kaho wasu irin mutane marasa kyawun gani da mummunar suffa irrin tata suka fara tururuwar fitowa. Duk dinsu babu mai kaya a cikinsu, tsirara suke yara da manya maza da mata, sai dan ganyen da suke rufe iya al’aurarsu kawai. Matan ko da ga samansu ma duk a bude yake tun daga yammata har tsoffi. Cikin kankanin lokaci duk suka zagayeta, yayinda wasu tsoffi da bazasu kaita shekaru ba suka rufu a kanta su kusan biyar maza biyu mata uku. Dagata sukai gaba dayanta ita da kujerar, daya da ga ciki kuma yay saurin yafa mata jan kyalle a saman fuskar datai kaca-kaca da jini. Daya da ga cikin dakunan Bamboo din suka shiga da ita, shikam da yar sabuntarsa kuma babba ne, sai dai cike yake da da was irin tarkacen bakaken gumaka da akaima ado da ja. Kujerar suka ajiye tare da fara zagayata suna was irin surutai da dukawa da tashi kamar wanda zasuyi ruku’u. Tuni nacan waje ma sun tattaru a kofar dakin yara da manya a layi, idan wadan can suka fadi surkullen sai su kuma su amsa musu da ga waje suma suna dukawa da mikewa. Gaba daya jajejin babu wani sauti da kakeji sai wanna surkullen nasu. Haka suka dingayi tsahon lokaci kafin a ciki su fara dibo was ruwa dake a manya-manyan randunan kasa na cikin akin suna zubama Uwa da cigaba da zagayeta cikin surkullen. A haka suka wanke mata jinin fuskarta tsaf, hancin dai ya fita babu kyawun gani sai fuskar ta kara munancewa fiye da da can. Amma jinin ya tsaya. Magunguna suka sassaka mata a ciwukan dan duk ta yayyanke dan ba hancin kawai ba. Bayan sun nutsa itama ta daina mummunan nishin da takeyi sai dai har lokacin a wajige take. Cikin mummunar muryar nan tata ta shiga kwala kiran wasu irin sunaye, jif!! jif!! jif!!! Kakejin abubuwa na fadowa cikin dakin, babu alamar toro a tattare da su, sai dai duk suna gabanta a tsaye kawunansu a kasa alamar girmamawa a gareta, Da wani irin zafin rai ta shiga nuni da bakaken hallitun dake ta fadowa. Ta nuna na farko cikin karaji da fadin, “Keje jajjal, da ga yau na baka umarnin, karka sake barin ta-kurya barci lafiya, a zagaye jikinta da kuraje masu warin da babu wanda zai iya rabarta koda danta ne, a dinga firgitata a ido biyu da cikin barcinta”.