Daudar Gora Book 2 Page 14
A mintinan da basu ƙarasa goma ba Sayyid Fayzul-haq ya iso. Cike da girmamawa ya miƙa gaisuwa. Kai kawai ya ɗaga masa batare da ya janye idanunsa da ga kan system ɗin gabansa da yake sarrafawa ba, dan tun shigowarsa ɗakin ita yay zaman sarrafawa. Ɗakin ya cigaba da ɗaukar shiru na tsawon wasu mintuna kamar bashi yasa ai kirasa ba. Sai da ya mula dan kansa kafin ya buɗe baki da ƙyar batare da ya bar abinda yake ɗin ba. “Ina buƙatar ruwan zam-zam, da waɗan nan abubuwan”. Yay maganar yana masa nuni da takardar da ke gefensa batare da ya ɗago ɗin ba dai. “An gama, umarninka shine abin jirana. ALLAH ya ƙara maka lafiya da rayuwa mai albarka”. Sayeed ya faɗa yana matsawa kansa a rissine ya ɗauka takardar. Sai kuma yay masa sallama duk da yasan ba amsa zai samu ba ya fice da hanzarinsa domin gaggauta cika umarnin shugabansa.
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa dukkan abinda ya buƙata aka kawosu..
Ya hana duk likitocin sake taɓata a wannan yinin, sai ma Daneen Ammarah da ya saka aka nemo masa. Tasha mamakin magungunan da ya nuna mata da ganin an cire duk wata na’urar da ke tare da Iffah’r, sai dai yanda ya tsuke fuska babu alamar wasa ya sata shanye duk abinda ke a ranta ta ɗauka abinda ya batan bisa umarnisa. Dan duk da kasancewarsa ɗan ɗan uwanta a yanzu shi ɗin shugaba ne, akwai gaɓar da kuma yake tafiyar da wasu al’amuran a tsakaninsu matsayin shugaba ɗin. Hakan baya damunta, dan kowa ya san ALLAH ne ya bashi, ba dan kuma ya kasƙantar da su a kansa bane ya fifitashi da jarabawar mulkin
Yanda ya umarcetan haka tayi akan Iffah, dan dole ta kasance a tare da ita har zuwa lokacin da ya bukaci ta kai tare da itan. Komai dake faruwa kuma akan idanunsa ne, sai bayan wucewar Daneen Ammarah da kusan mintuna talatin ya ɗauka Alkur’aninsa ya fito cike da takun nan nasa na izza da ƙasaita ya nufi ɗakin. Zama yay a kujerar da ke gaban gadon shanyayyun idanunsa a kanta, ya mata kallo na wasu mintuna tamkar mai nazari kafin ya fesar da ɗan huci ya ɗauke kansa. Alkur’anin ya buɗe yana mai ƙara tabbatar da nutsuwarsa gaba ɗaya garesa sannan ya fara raira karatu cikin daddaɗar muryarsa da bama kowane harafi hakkinsa cikin ƙwararren larabci yanda ya kamata.
Ya ɗauki tsahon lokaci yana karatun, kafin ya tsagaita ya rufe ya ajiye. Kujerar da yake zaunen ya sake matsarwa gab-gab da gadon, tamkar wanda baya so ya kai hanunsa kan bargon ya ɗan yaye kaɗan. Kauda idanunsa yay da ga kallon inda suka sauka ya maida a fuskarta, ɗan bakin tsiwar nan duk ya bushe. Ya ɗan ja wasu sakanni a kallon nata, sai kuma ya kaudar yana sake tsuke fuska ya fara karanto addu’oi yana tofa mata. Haka ya kasance tare da ita har gabannin asubahi, dan sai da katafaren agogon masarautar ya buga cikar ƙarfe uku dai-dai sannan ya bar ɗakin ya koma nasa. Dole ya kai kwance dan shima ba jikin nasa ya gama komawa normal bane, a yanzu hakan ma jiri-jirin da ya fara ji yana rinjayarsa ne ya sakashi haƙura ya dawo nan ɗin.
Ƙoƙarin rufe system ɗin gabansa yake dai-dai da shigowarta da sallama doctor Afif na take mata baya kasancewar hadimanta basu da hurin biyota har nan. A kallo ɗaya zaka fahimci ɓacin ran da ke shimfiɗe kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Doctor Afif ya gyara mata kujerar da ke gaban gadon jiyyar Tajwar Eshaan ɗin, sai da ta zauna ya juya ya fice tare da zuge musu ƙofar gilashin duk da wajene da bana shiga kowa da kowa ba.
A hankali ya ɗan risinar da idanunsa alamar girmamawarsa gareta, sai kuma ya motsa lips ɗinsa a tausashe ya furta “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki ya Ammie-na”.
Duk da ɓacin ran da ke zagaye da zuciyarta hakan bai hanata ɗan sakin murmushi ba, ta kai hannunta kan nasa ta riƙo, itama cikin sauƙaƙa harshe da nuna kulawa ta amsa. “Tare da kai Bin Haysam Abdul-majeed. Ya ƙarfin jikinka?”.
Suna mafi soyuwa da yakan so ji da ga bakin mahaifiyarsa, sai dai kuma a duk sanda ya jisa da ƙarfin izzar harshenta ya kan saurin gane ɓacin ranta a bayyane. Ganin damuwarta kam shine abu mafi ƙona zuciyarsa dan shi karan kansa bai san irin tarin ƙaunar da yake ma mahaifiyar tasa ba. Kaɗan ya gyara kishingiɗar da yay har lokacin idanunsa na kanta, ya juya yatsunsa da ke riƙe da nata ya maida nasa a ciki, a sannu yake tausa mata gaɓɓansu da kulawa da lallashi batare da ya sake cewa komai ba. Tsahon mintuna suna a haka har ta fara sauke ajiyar zuciya alamar saukar fushin nata. Ganin ta koma kamar yanda yafi buƙatar ganinta ya ɗan sake mata murmushi.