Daudar Gora Book 2 Page 127
Tunda aka shigo da Arshaan dakin kurkukun da ke makwaftaka da juna da na Miran Jasim sukema juna kallon kallo, duk da dai shi Jasim bai ko motsa da ga zaman takurewa waje dayan da yay ba, su dukansu dakin
babu yawaitar haske, sai dai ta dan hasken da ke lekowa sukan iya gain junansu. Sun kwashe awa guda a haka kafin Jasim ya mike cikin dan tangadi, dan baya cin abincin da ake bashi ga raunikan da ya jima kansa duk an masa tretiment dinsu. Jikin karfen da ya raba dakin nasu ya tsaya, sai kuma ya kece da wata irin dariya kamar wanda hauka ya kama. Cikin bacin rai da kunar zuciya Arshaan ke kallonsa, sai dai baice komai ba har yayi ya gama yay shiru dan kansa. “Oh!! Kai dama a tunaninka Jasim ne kawai ta karewa Arshaan? Lallai kai jaki ne bazan gaji da maimaita fada ba, why da ace uwarka na raye zuwa yanzu nayi imanin bakin cikin haihuwar wawa da tai irinka ne zai zama ajalinta. Kai anya ma kuwa bada cikinka ta shigo gidan nan namu ba
Arshaan ya fada cikin karaji da wani irin girgiza karfen tsakanin nasu kamar zai babbagesa,amma da yake a gine yake cikin kasa ko gezau shegen baiyi ba. Ka dan Jasim yay baya yana dage hannaye sama kamar wanda yay surrunder, sai kuma ya sake kwashewa da dariya kamar zai fadi ya sake dafe karfen yana fadin, “Shegen kaya ashe kasan abinda kake. To to naji uwarka anan ta haifeka, sai dai wlhy bazan daina tantama ba nikan kodan kasancewarka kasurgumin annamimi, butulu,sannan rago mai labewa a bayan mace domin kubutar da kai. Shin nawa ta siyeka ne har haka?”
“Yanda aka sayo uwarka a gidan karuwai. Why da ga yau idan ka sake kuskuren zagin uwata, sai na maka lahanin da sai ruhin uwarka ya dawo duniya yana mai cikin garari Jasim.Wawa jaki kawai maybe ma uwar takace ta shigo mana da cikinka da ga wajen dan tsautsayi kawai. Ko an fada maka bamusan tarihin tushenta bane a gidan.
“Amma kasan zan iva kasheka na binne gawarka a cikin kurkukun nan ko? Idan ka manta bari na tuna maka wanene Jasim in Abdul- majeed Aliy Qutb, domin ni a gareka sai dai kallo sai kuma hange daga nesa koda bakin cikina zai ajalinka. Ko an fada maka ban san kulle-kullen da ka jima kanayi a kaina bane?, Kana goyamun baya domin in mun kauda shi nima ka kaudani, sai dai kuma kayi kuskure, domin kafin kaga biri shi birin ya ganka dan hau. Da ido daya Jasim ke barci,sannan a tafin hannuna kake, zakuma ka tabbatar da hakan nan gaba jadan”. Ya kare maganar yana wata yar iskar dariya cikin rangaji harya koma wajen zamansa ya sake zama rigija yana dariyar har lokacin.
Shiru Miran Arshaan baice komai ba, sai dai yana tsaye kamar gunkin da aka ajiye dan tarihi idanunsa nabin Jasim din da kallo, da alama dai tattaro abin fada yake, ko kuma maganar Jasim din ce dai ke masa kaikawo dan bai taba tunanin yasan da wannan burin tattare da shi ba
Kwanaki biyar kenan da mika su Arshaan suma a makargama, Jasim kuwa sati guda. Sai dai kuma Tajwar Eshaan bai sake cewa komai ba game da su, hasalima a yau da ake saran ganin watan azumin ramadana ya dauka hutun fitowa fada har sai bayan salla. Tare da daura Sayeed Fayzul-haq akan komai dan zaije Umrah shi da iyalinsa kamar yanda ya sanar.Tabbas a wannan karon babu wasa a cikin al’amarin Tajwar Eshaan din, dan haka kowa ya shiga taitayinsa har su manyan masarautar. Duk da akwai abubuwan fada a bakinsu har game da karasa zaman shari’ar da aka fara amma sun gagara cewa komai har ya gama jawabin fara azumi da gamashi lafiya yay musu bankwana.
A lokacin da Tajwar Eshaan ke can yana bankwana da jama’ar fada anan Iffah ce cikin babban bitalmanin kasar ruman bisa jagorancin babban dan Sayeed Khairul-Bashar mai suna Abdul-Shakhur in Khairul-Bashar tana bada umarnin ware kayan masarufi nau’i-nau’i domin dorasa a jagorancin rabawa talakawan kasa. Sai matasan masarautar da ta saka shi Abdul- Shakhur din ya samo har su hamsin da zasu jagoranci sauran jihohi da wanda za’a kai wasu kasashen da yaki ya samarwa yan gudun hijira da ma iftila’ in rayuwa na talauci.
Wannan al’amari ya matukar jjiga kunnen duk wanda ya samu labari a cikin masarautar, dan abinda bai taba faruwa bane, duk da duk azumi akan fitar da kayan masarufi a dan kai jihohi suma kuma ana da kasune ga Tajwar na jihohi bawai a wakilta wasu suyi aikin ba a cikin masarautar. Sannan a duk shekara tun ba hawan Tajwar Eshaan din Malikat Bushirat ce ke da wanna karfin ikon matsayinta na mahaifiya ga Shahan-shan. Sai kuma a yau labarin ya canja akaga Zawjata-almilk kan komai cikin kuma sauyi.