Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 115

Sponsored links

“Wlhy zaka kara, ranar ba sai da kace bazaka sake ba amma yau ka kara, ni bazan sake zama a sashen na a kasheni kwana na bai kare ba”. Ta kara barke ma sa da kukan tabara.

Yanzu kam kasa rike dariyar yayi, dole ya Murmusa har jerarrun fararen hakwaransa masu da siririyar wushirya na bayyana a zahiri Bashi da zabin da ya wuce sake rungumeta a jkinsa tsam-tsam yay murmushinsa iya san ransa. (Shi kam wannan Fitinanniyar yarinya ALLAH ya bashi, kuma yana so da kaunar abinsa fiye da zaton mai hasashe). A zuciyarsa

 

yake maganar yana bata sumbata masu kyau a wuya. Kafin ya mike ya dagata cak zuwa bathroom. Idanunta ta rumtse sosai da kankamesa ita a dole karya gammata jiki kar kuma ta gansa itama.

Gashi yay mata mai kyau bayan ya duba yau baiyi barna ba dan ciwukan wancan ranar ma sun warke sai abinda ba’a rasa ba, taimaka mata yay tai wanka, hawaye kuwa da ya ga ba dainawa zatai ba bai sake ce mata komai ba kansu. Da zasu fito cewa tai ita why bazata iya ba sai dai ya dauke ta. Baice komai ba, illa murmushi da yay a zuciyarsa ya dauke ta cak suka fito tana faman tura masa karamin bakinta.Ga idanu sunyi luhu-luhu na kukan da tasha.

 

“Idan baki bar turamin bakin nan ba zan maimaita ni babu ruwana”. Ya fada yana tsane mata laimar ruwan kanta da towel. Narai-narai tai da fuska zata sake masa kuka ya daura yatsansa saman bakinta ya ce, “Shilli!! Harda kuka ma”. Babu shiri ta hadiye abunta da maida bakin da sauri. Murmushi ya saki da cigaba da tsane mata gashin…. kiran da ya shigo ta sashi dakatawa su duka suka dubi wayar, kamar bazai daga ba dan har tana gab da tsinkewa sai kuma ya kai hannu ya dauka batare daya matsa da ga gabanta ba ko dauke towel din da ga kanta.

Cikin girmamawa shugaban jami’ai ya shiga gaishesa da ga can, a takaice ya amsa masa murya a dake kamar bashine ke hidimtawa yar yarinya ba. Da ga can shugaban jami’ai ya kara nutsuwa sannan yay masa bayanin abinda ke faruwa. Shiru kamar bazaice komai ba kafin ya nisa a dan fisge da maganar nan tasa kasa-kasa ya ce, “Doctor Afif ya je ya dubasa a cikin kurkukun”. Daga haka ya yanke kiran.

Kallonsa Iffah tai da jajayen idanunta, gaba daya ya sauya kamar bashi ba ya koma mata Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed da ta fara gani a sashen Mammah. Muryarta a dashe saboda kukan da tasha ta ce, “Miya faru?”.Kamar bazai kulata ba yana cigaba da goge mata kan tsahon minti biyu kafin ya motsa lips da kyar ya furta “Jasim”…

Dakin Akhi na lallaba batare da sanin kowa ba, nai sa’a kuwa yana wajen karatu dan haka a shiga bincike dakinsa. Na samu nasarar gain hotunan Hubba da ya shirya tura masa cikin jin dadì na kwashesu na ajiye nawa da wasikar nan na sake sabon manne envelope din. Gudun a yanka ta tashi na kone hotunan Hubba a cikin toilet batare da sanin kowa ba…. Kamar yanda Akhi ya fada ya aika sakon Miran Haysam batare da sanin na canja hotuna ba. Kwana biyar tsakani sai ga masu neman aure sunzo. Hankalina ya tashi naita kaikawo da neman hanyar da zanji yaya akai amma ban samu ba. Dole na hakura har bakin suka tafi Abbie da Akhi suka shigo gidan. Cikin muryar damuwa najiyo Abbie na sanarma Ummu cewar maganar da sukayice ta taso, sai dai sabanin Hubba da su suka zaba shi yanzu ya aiko cewar Bushirat, harma sun rasa a ina ya sanni. Kokwanton da suka shiga yasa Akhi tashi da kansa zuwa masarauta dan tabbatar wa. Amma magana daya ce dai Bushirat ya zaba. Babu alamar damuwa akan fuskar Ummu tace ai duk kai da kaya mallakar wuyane ALLAH yasa haka shine mafi alkairi, dan itama dai batai magana bane kawai amma abin na damunta. Kar ace dan Hubba yarta ce aka tsallakeni aka bata alhalin nice babba. Oho ko dar banji da kalamanta ba, ni dai tunda burina ya cika damuwa ta kare. An shiga shirye-shiryen biki, yayinda niko keta nokewa kamar bana so dan harda kukana. Sai gashi su Abbie sun zubda makaman su sun koma lallashina. Da wanna salon nai amfani na cinye wasan akan bikina cikin kwanciyar hankali kowa na lallabani. An kawoni masarautar ruman masarauta mai abubuwan kawa da na birgewa. Duk da na tashi a gidanmu akwai kudi sai naga ashe muma yayan malam Shehu ne dukiya na’a inda take. Abu na farko da bai munba shine dole na zauna a kasan ikon Malikat Haseenat mai amsa sunan mahaifiya ga mijina, sai dai kuma babu yanda zanyi dan ta hakanne kawai zan samu yanda nake so. Na hakura na mika wuya anan dan koba komai tana nunamin kauna babu bambanci da yayanta. Abu na biyu shine Ashwaq a matsayin uwargidana wadda kowa ke jingina zamanta Malikat. Na shiga damuwa matuka a kanta tare da neman hanyoyin dakile al’amarin ta. Ban gama da itab ba aka auro Danish-Ara. Wannan shine mataki na farko da ya hada alakata da UWA. Dan tun sanda naji labarinta da dambarwar dake faruwa tsakaninta da Mammah a daura dammarar neman kusanci da ita. Nako sami nasara ta hanyar amintaccen hadimin Haysam, bayan na shaka masa makudan kudade amma ya nunamin har abada bazai ci amanar shugabansa ba, raina ya baci dan haka na koma barazana akan iyalansa, harma na aikata masa a aikace ta hanyar sakawa matarsa ta kawo min diyarsu daya da suka haifa sashena. Na tabbatar masa zan kasheta wanna shine dalilin amincemin badan yaso ba ya hadani da uwa. Na razana a ganin farko dana mata, dan mutumce mummunar gaske, da zaka iya rantsewa badaga yankin wanna kasa ta fito ba koma na dake zuciyata. A ranar batako kulani ba, hasalima korani tai wai ban shirya ba. Naji zafi amma na daure harda dukawa kasa ina bata hakuri akan laifin da ban san nayi ba. Bata dai kulanin ba haka na taso na taho.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button