Daudar Gora Book 2 Page 10
Ƙwayoyin idanunsa ya juya ga Doctor da ke daga gefe, tazbihi kawai yake ma UBANGIJI da girmama jini irin na masu mulki da ƙasaitar Shahan-shan ɗin na su, har zuciyarsa na raya masa anya kuwa akwai wani sarki mai mulki da ƙasaitarsa zata iya kamo ƙafar ta Shahan-shan ɗin nasu Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed?. Rashin mai tayasa ya sashi haɗiye tarin gulmar dake ran nasa ya saci kallonsa ta ƙasan ido, sai akai sa’a dai-dai saukar idon Tajwar Eshaan ɗin a kansa. Da sauri ya maida nasa ya rissinar yana mai jin kaifi da tasirin na Shahan-shan ɗin a kansa.
“ALLAH ya ƙara lafiya da tsohon rai mai albarka ko ana buƙatar wani abu ne?”.
Ya faɗa cikin rawar harshe da kaifafan idanun Tajwar Eshaan suka haddasa masa. Kallon nasa ya cigaba da yi har na wasu tsahon sakanni da suka kusa ƙulla mintuna biyu kafin ya motsa lips ɗinsa kaɗan ya faɗi abinda ya ke ta juyawa a ransa tun ɗazun.
“Zata iya kasancewa tare da mu anan?”.
Cikin gyaɗa kai da sake risinar da shi Doctor Afif yay saurin faɗin, “Idan hakan shine buƙatar adalin sarki shugaban sarakunan ƙasar ruman da al’ummar cikinta ya tabbata abu mafi sauƙin zartarwa a bisa umarninsa”.
Kansa kawai ya ɗauke ba tare da ya sake magana ba har doctor ya fice. Daneen Ammarah da fuskarta ke faɗaɗa da murmushi ta buɗe baki zatai magana, sai hakan yay dai-dai da ɗagowarsa gareta, har cikin rai yaji daɗin ganin murmushin a fuskarta, amma bazaka taɓa gane hakan a tashi fuskarba. Ya dai ɗan sake ƙasa-ƙasa da idanunsa masu yalwar cikar gashi da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta…
“Kinyi farin ciki?”.
“Sosai sosai kuwa sweetheart. ALLAH ya albarkaci rayuwarka, ya cigaba da tsare min kai ga duk wani abin ƙi. Ya yalwata zuciyarka da imanin da baya yankewa da tsoron ALLAH. ALLAH ya ƙara maka lafiya adalin shugabanmu abin alfaharin ƙasar ruman da al’ummar cikinta….”
“Mammyy!”.
Ya faɗa da wani irin sanyi-sanyi da ke son bayyana shagwaɓarsa a fili duk da fuskarsa ta shanye komai ta ɓoye. Karan farko Daneen Ammarah ta saki ƴar siririyar dariya dan ganin Baby Eshaan ɗin ta na baya a zahiri. (Su baby Eshaan anji jiki😜🏃)…
★Cikin ƙankanin lokaci aka cika umarninsa ta hanyar saka gado a ɗakin dake jikin katafaren ɗakin jiyyar tasa da gilashi kawai ya rabasu da nashin da ya kasance na musamman a sashe na musamman tare da dukkanin kayan aikin kula da duk motsin mai jiyya da abinda irin tata jiyyar take buƙata. Yana zaune a irin zaman da yafi yi a gadon jiyyar tasa ƙafafu a miƙe an rufesu da farin lallausan duvet har zuwa ƙugunsa, bayansa jingine da filon daya zauna dai-dai yanda ake buƙatarsa da taimakon ɗaga gadon da akai irin na mai jiyya. Duk da yanayi na mai jiyya da fuskarsa ta nuna tana nan tar-tar da ita da hasken nan nasa mai ɗaukar ido kamar madara, hakama kwantaccen gashin daya zagaye fuskarsa baƙi siɗik na kwance a fuskar kai kace wani hamshaƙin gyara yake samu. Duk da kasancewarsa a asibiti mayataccen ƙamshinsa da nasa ne shi kaɗai babu wani mahaluki mai irinsa ya gama manne ɗakin da duk wani abu da ake sarrafawa. Alkur’ani ne a hannunsa yana karatu dan haka bai ko motsa ba har aka kammala gyara gadon da za’a ajiye Iffah itama aka gungurota a gado. Da taimakon likitoci biyu mata aka ɗagata daga gadon da suka turota suka maidata a gadon da aka kafa. Sharɓan take kwance idanu a rufe, ƙyaƙyƙyawar fuskarta ma’abociyar tsiwa da rashin barin sai ta kwana tayi wani fayau. Ta rame ga idon duk wanda ya santa duk da bata cikin hayyacinta, damma bargon da aka lulluɓeta da shi ya ɓoye ramar da tayi ta jiki. Har suka kammala komai suka fice bai motsa idanunsa da ga kan Alkur’anin ba, karatunsa yake a nutse cikin zuciya da tattara dukan hankalinsa kacokan.
Sai da ya kai inda yake buƙatar kaiwar sannan ya dakata yana mai lumshe idanunsa da sakin jerarrun ajiyar zuciya, dan a duk sanda ya kusanci Alkur’ani ta hanyar karantasa ya kanjisa cikin wata tarin nutsuwa da mulki ko dukiya ko wata ɗaukakar duniya bata bama ɗan adam. Yakan shagaltu da wani sirri da mai karanta Alkur’ani ne kawai ke iya samunsa a duniya. Sannan dukan damuwa da nauyin zuciyarsa kan kwaranye ya dinga jinsa tamkar wani sabon mutum sabuwar haihuwa. Bayan jan tsahon mintinan da suka sake tabbatar da gamsuwar nutsuwar da gangar jikinsa da zuciyarsa ke buƙata ya sake sauke ajiyar zuciya da buɗe lumsassun idanun nasa inda zuciyarsa ke fisgarsa da umarnin da bazai iya bijirewa ba.