Daudar Gora Book 1 Page 93
A yanda hadiman suka sani daga haka hanyar da zata maidashi bedroom ɗin daya kwana yake bi, acan zai samu shayinsa na ƙa’ida mai dafawa ta kai, bayan yasha zai shiga wanka kafin ya fito inda aka shirya masa karin kummalo. Sai dai saɓanin yau yana ɗaga ƙafa domin barin wajen bayan ya dubi Aamin nasa ya rissinar da kai kaɗan na alamar sallama da girmamawa a garesa Iffah dake faman baza ƙamshin da ga Shahan-shan ɗin kawai suka sansa ta isowa wajen ɗauke da ƙaramin kofin shayi dake tururi fari tar na glass.
Da sauri duk hadiman suka juya bayansu, dan kallon abinda zai iya biyo bayan wanda suka gani ɗin haramunne a garesu. Iffah dake taku a nutse kamar wata hawainiya takalmanta da ba wani tsinin kirkine da su ba na bada sautin isar da saƙon tahowar tata ta iso gabansa.. Ƙin yarda tai koda wasa su haɗa idanu. Idanunsa da kallonsu ke canjawa ya sauke akan kofin shayin da take miƙo masan. Shiru babu alamar zai amsa, har hanunta na ƙoƙarin fara yin dayi. Sai da ta fara ambatar sunan ALLAH kafin ta ɗago fuskarta a dake,
“Ƙin sha na nufin rauni da muhimmancin Zawjata-almilk a gareka. Ko kuwa cigaba da tabbatarma duniya abinda suka sani shine gaskiya ranka ya daɗe”.
Yanda lips ɗinta da suka sha pink lipstick ke motsawa ya zubama ido, sai dai maimakon mata sharhi akan zancenta kamar yanda taso yau gefe ya ɗan maida kansa da amsar shayin kamar wanda ya shiga halin tarkon kasala. Karan farko ta sakar masa wani lallausan murmushi da faɗin, “Thanks”.
Basarwa yay ta hanyar ɗan duban gefensa a takaice ya furta,
“Aami”.
Da sauri Iffah ta duba wajen tamkar sai yanzu ne taga Miran Arshaan ɗin, “Ya salam”. Ta faɗa a zahiri da nufarsa ta zube ƙasa domin miƙa gaisuwa a garesa. Ya ɗan murmusa zuciyarsa taf da al’ajabin wannan figigiyar yarinya da da auren wuri yayi ya haifa wanda suka fita nesa ba kusa ba. Cike da salonsa na fuska biyu ya amsa yana mai ƙare mata kallo ta ƙasan ido. Iffah daba kula da hakan tai ba cike da girmamawa ta miƙe da faɗin, “Uncle bara a baka shayin kaima”.
“Zan so kasanwa na farko da zai ci abu daga hanunki Ibnati”.
Jin daɗin kalamansa yasa Iffah sakin murmushi da ɗan rissinawa ta furta, “Na gode Aam”. Shima dai shayin ta kawo masa, nan ma yay mata godiya da sanya albarka yana ɗan duban sashen da Tajwar yake tsaye dafe da ƙarfen da aka zagaye wajen ta bakin ginin yake ya tsurama cikin masarautar idanu yana ɗan kai shayin bakinsa tamkar bai san abinda ke gudana a wajen ba. A hankali ya taka inda yake shima yana shan nasa.
“Yanzu ne daular ruman ta tabbatar da samuwar Zawjata-almilk”.
Sarai Tajwar Eshaan ya jisa. Amma halinsa na ƙasaita da mafi yawan iyayen nasa suke ambato da girman kai yasa yay tamkar baiji ɗin ba. Sai ma juyawa da yay bayan wasu sakkani ya dubi Aamin nasa cikin tausasashiyar muryarsa mara hayaniya da kamewa ya furta. “A huta gajiya”. Ya bar wajen.
Ga mamakin duk wanda ke’a wajen gaban Iffah dake ɗan nisa da su ya isa. A bazata taji tattausan tafin hanunsa da yay sanyi ƙalau sakamakon iskar wajen a cikin nata. Da sauri ta rumtse idanu tana mai ambaton sunan ALLAH a zuciyarta da ɗan dubamsa. Ba ita yake kallo ba, sai ma fara takawar da yay wanda ya tilastata binsa tamkar raƙumi da akala. Batare da sun luraba takun sawayensu na sauka da ɗagawa a tare sakamakon shima tafiyar izza da ƙasaita irin na masu mulki yasa baida garaje a tafiya tamkar wani mace. Anan ɗin ma dai tana sanya ƙafarta na’ura ta sanar da ita wacece, haka shima. Da sauri hadimin dake a ƙofar ya zube yana kwasar gaisuwa. Hannu kawai ya ɗaga masa yay gaba abinsa har lokacin hannunsa na cikin nata ya riƙe gam kamar wanda aka bama amanar riƙon nata dan karta suɓuce……