Daudar Gora Book 1 Page 87
A take fuskokinsu suka nuna jin daɗin wannan girma daya basu. Sanin halinsa yasa daga haka sukai masa sallama. Har sun miƙe Miran Arshaan yace “Af niko kaga na shafa’a da wannan batun. Abni baka ganin yayi kusa kuwa ace fitar Zawjata-almilk har cikin books room? Yakamata ace tayi haƙurin cigaba da killace kanta kodan maƙiyan da bamu san ta inda suke shirya sabon shiri ba, dan yayi wuri ace mun shagala da tsallakewar ta ta a nawa ɗan hangen. Ai ƙoƙari a tsawata mata ALLAH ya cigaba da kare mana ku ku duka dai”.
Miran Jasim ya amsa da Amin yana jinjina kai alamar tabbatar da maganar, sai dai ganin Tajwar Eshaan bashi da alamar cewa wani abu suka fice abinsu. Koda suka fitan ya jima bai motsa a yanda yake ba, da alama dai maganar tasu ta ƙarshe ce ke masa kaikawo. Hasashen kam sai ya zama gaskiya dan akan lips ɗinsa daya motsa kaɗan ya ambaci, “Yarinyar nan ko”. Daga haka ya shanye sauran a cikinsa….
Kamar yanda ta faɗa bayan sallar isha’i ta fito cikin abaya fara tas. Duk da dare ne ƙamshinta da kwarjininta mai ɓoye ƙarancin shekarunta na tare da ita. Fuskarta ɗauke da murmushi mai bayyana haƙora take amsa gaisuwar hadiman da tuni sun kammala taruwa bisa umarninta. Ɗaya bayan ɗaya ta basu damar gabatar mata da kansu da matsayin ayyukansu. Har suka gama batace komai ba tana dai nazarinsu ne. Haka kawai take jin bai kamata ta yarda da kowa ba a wannan gaɓar, dan duk da tausayinsu dake nuƙurƙusar zuciyarta tayi imanin akwai masu gurɓatacciyar zuciya a cikinsu kamar yanda Daneen Ammarah ta karanta mata komai.
“Okay duk naji bayanan ku, sai dai kuma Ni zan canja tsarin aikin da bama kowa abinda nake ganin zai fi dacewa da kasancewar tare da ni. Bazan roƙi kowa ba a cikinku cewar ya kasance mai gaskiya da riƙe amana, sai dai zan tabbatar muku zan iya hukunci ga kowa idan na kamashi da waɗan nan abubuwan biyu. Dan na matuƙar tsanar mai wannan halayar koda a sama dani yake. Zan kuma iya aikata harma abinda mutum baiyi zatoba akan hakan…..” ɗaya bayan ɗaya ta rarrabasu ga ayyukan saɓanin yanda aka turosu suyi, salon nata ya matuƙar girgizasu a take kuma tasirin gizagonta ya shigesu, har suke ambaton tsarin da gaba kura baya sayaƙi kenan, dan kuwa dai kamar yanda Iffah tai hasashe mafiya yawan cikinsu zasu kasance da itane bisa umarnin iyayen gidansu na ɓoye bisa ɗabi’ar tura ƴan leƙen asiri da manyan masarautar suka tasirantu a kansa. Bayan ta sallamesu akan aikinsu zai fara daga gobe ne ta tattare littafanta da kanta tai ciki da su. Sai da ta tabbatar ta ƙarema ɗakin kallo yanda ya kamata fiye da ɗazu bisa zargin za’a iya saka mata camara kamar yanda Ajmaal ya tabbar mata. Babu alamar akwai abinda take zargin dan haka ta ɗauka wayarta. A maimakon WhatsApp yau a text message ta tura masa saƙo, daga ƙarshe ta ƙara roƙonsa bincika mata lafiyar iyayenta dan zuwa yanzu zuciyarta na tabbatar mata akwai abinda Sir Fawzan ya faɗa mata ba dai-dai ba ko yake ɓoye mata. Dan kullum takan gwada number Hanash da Babiy sama da sau babu adadi amma babu alamar zata samesu. Ga mafarkinta a kansu duk kusan bayan kwana biyu cikin maimaita kansa yake gareta. Bawai tayi imani da hakan bane, kawai dai zuciyarta takan rinjayu da tsoro akan mafarki musamman idan ta auna da abubuwan da suka tabbata akan wasu mafarkai da sukai wa riƙon wasarere ita da iyayenta a baya…….
Kamar yanda labarin fitar Iffah yaje kunnen kowa a masarautar itama yaje nata kunnen, sai dai saɓanin malikat Bushirat ita murmushi tayi batare data furta komai ba akan zancen. Rashin cewar tata ya Bama Hadimar damar ƙarasa mata zancen akan Iffah kuma ta koma sashenta bayan barowarta books room. Anan kam idanu Malikat Haseenat ta tsurama hadimar Tata tamkar zataga fuskar Iffah a jikinta ne. Sai kuma ta janye da wani ɗan murmushi a fuskarta ta maida ga hadima Banou.
“A haɗa abincin karin kumallo da Zawjata-almilk ta uku”.
Cikin tashin hankalin wannan umarni na Malikat Haseenat kamar Banou zata fasa kuka ta jinjina kai, har hakan ya bama malikat Haseenat mamaki, sai dai batayi magana ba kasancewar tasan shirmen Banou fiye da haka. Itama dai tana zaune da itane batare da tasan dalili ba, amma wasu lokuta takanji yanayi mai wahalar fassara koda a kallon hadimar tata ne amintacciya a bangaren girka mata abinci…