Daudar Gora Book 1 Page 75
(Mi wannan mutumin ke ƙullawa?). Ta faɗa a zuciya batare data motsa ba. (Keda ke neman kusanci da shi dama miye matsalarki da koma mi yake nufi) wata zuciyarta ta sake ayyana mata. tamkar wadda aka zaburar sunan Arfa da Fariha ya fara amsa kuwwa a zuciyarta har tana jinsa yana tashi bisa sararin samaniya.
Kaifafan idanunsa masu nuna tsaurinsa ya zuba mata ganin ta basar da shi itama. Kusan mintuna uku babu alamar zata tankama zancen nasa har ya fara jin haushi. Ta taɓe baki da kauda kanta gefe, cike da dakewa ta furta, “Da gizago na tsorata ƙwarin gwiwata da bazan amincewa shigowa ramin zakin da ɗanyen nama shine abincinsa ba. Karka damu a kaina ranka ya daɗe, dan a wannan gaɓar *_cuta ce ta ɗakko cuta, ɓarawo ya ɗakko akwatin maciji”._*
Fuska ya ɗan motsa kamar zaiyi murmushi, sai kuma ya basar. “Bana haɗa ƙwanji da mage duk da kamaninta na yanayi da nawa matsayina na ZAKI har a hallaya. Ki kama kanki dan kina buƙatar rayuwa mai tsaho wajen moran ƙuruciyarki”.
Ya faɗa da muryarsa mai zurfi da ƙasaita yana miƙewa ya zagayeta ya wuce abinsa. Shiru bata motsa ba har ta gama jin ɓacewar sautin takunsa a wajen, ta ɗan cije bakinta “Zaki zako ka magantu fiye da haka”. Ta faɗa a fili cike da kwaikwayo salon maganarsa tana sakin wani lallausan murmushi da kai kofin shayi a bakinta, duk da zafinsa ta rumtse ido ta kwankwaɗe abinta sannan ta juya taima hadiman dake tsaye har yanzu kallo ɗaya ta ɗauke kanta batare da damuwar komai ba, dan tasan basuji komai ɗin ba da suka tattauna. A yanda suke maganar ma wani sai ya ɗauka wani zancen soyayya ne ya haɗasu. Komai batacema kowa ba itama ta miƙe tabar wajen, duk suka bita da kallon ƙasan ido kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa.
A tafiyar tata tana ɗan kalle-kalle taci karo da camara, komai bataji a ranta ba, dan tayi tsammanin hakan tun farko, saboda babu yanda za’ai sashen mutum mai ƙarfin iko kamar Tajwar ace babu wani tsaro makamancin hakan koma fiye da hakan. Da ƙyar ta iya gane ɗakin data kwana. Tana shiga ta zube a kujera da sauke nauyayan numfashi, ɗakin da akaima gyara ɗan gaske tabi da idanu, sai taga ma kamar ba’a cikinsa ta kwana ba, ganin akwatin kayanta kawai ya tabbatar mata da shi ɗin ne. Tunani mai ƙarfin gaske ta faɗa kusan kashi uku zuwa huɗu musamman akan kawota da Malikat Haseena tayi, mi tsohuwar ke nufi da haka bayan su suka sanar mata an rasa matan baya ne a dalilin kawosu turakar Shahan-shan ɗin. Sai kuma akan Tajwar Eshaan ɗin, na farko waccan fuskar data gani a waje kafin shigowarta masarautar matsayin matarsa. Na biyu wannan fuskar ta yanzu da bata da banbanci da waccan ɗin, na uku hanyar da ya kamata ta cigaba da bi domin sanin ainahin wanene Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed a baɗini da zahirin rayuwa. Domin da gasken gaske tana a cikin ruɗani akan fuskokin nan biyu data gani a mabanbanta muhallai. Su ƴan biyu ne? Kokuwa shi ɗinne ke ɓadda kama yana fita?. Abu na uku kuma abinda ya faru a daren jiya da sai a yanzu yake bata matuƙar mamaki, tun a jiyan bawai ta ajiyesa a gefe bane dan bashi da muhimmanci ga haɗarin da tasan ta kawo kanta ciki, kawai dai bata san dalilin da yasa bataji ko ɗar ba a zuciyarta na tsoro, kuma har yanzu batajin tsoron sam, dama kuma tun asali bata da tsoron. Dan Iffah irin mutanen nan ne masu ƙesashiyar zuciya mai iya tunkarar komai koda yanada haɗari a garesu, tanada naci da zama kaifi ɗaya akan zimma da cimma buri duk da ƙarancin shekarunta. Na ƙarshe tattaunawarsu ta yanzu da shi da girman kalaman da yay amfani wajen jifanta da su. Ta ɗan murmusa da cije lips ɗinta tana mai lumshe idanu a hankali…