Daudar Gora Book 1 Page 73
A ɓangaren jama’ar masarauta dake a zaman jigum-jigum kam fitar hadimar nan ya isar da saƙon Zawjata-almilk na raye. Da farko duk wanda zancen yaje kunensa ɗaukewar numfashi na wucin gadi ne ke riskarsa, sai kuma rashin gaskatawa a zahiri ya biyo baya. Hatta da Malikat Bushirat da Daneen Ammarah yanayi da ruɗanin jin hakan bai tsallakesu ba suma. A kusan tare suka ɗauka wayoyinsu domin neman Iffah ko zasu samu jin gaskiyar zance. Cikin Sa’a kuwa ta Daneen Ammarah ta fara shiga….
Iffah na zaune har yanzu cikin ɗaurewar kai akan wanda ya maidata saman gado da wulƙawar fitar wadda bata sani ba wayarta ta katseta. Numfashi taja ta fesar da ɗan ƙarfi tana kai hannu akan wayar. *_Mamy_* ta gani rubuce ɓaro-ɓaro. Ganin zata katse tai ƙarfin halin ɗagawa ta kai kunne tana faɗin, “Assalamu alaikum. Amincin UBANGIJI da rahamar sa su yalwatu a gareki Mamy barka da safiya”.
A matuƙar razani da motsuwar zuciya Daneen Ammarah taja numfashin dake neman ƙwace mata. “Ibnati!”. Ta ambata cikin son tabbatarwa.
“Na’am Mamy”.
Iffah ta amsa kanta tsaye babu alamar irin fargabar dake harshen Daneen Ammarah ɗin a tattare da ita. Dan ita wanda ya ɗauketa daga ƙasa ya maida saman gado da fitar macen data ganine kawai damuwarta a yanzu. Daneen Ammarah da taji al’amarin tamkar a mafarki ta lumshe ido hawaye na silalo mata saman ƙyakykywar fuskarta a hankali. Ƙasa takai durƙushe tana mai godema UBANGIJI ta hayar kai goshinta ƙasa tai sujjadar shukur…
Iffah da mamaki ta cigaba da ambaton “Hallo Mamy! Mamy kina jina kuwa?”. Shiru babu alamar za’a amsa. Yanke wayar tai da yunƙurin sake kira a zatonta matsalar network ce sai ga kiran Malikat Bushirat ya shigo shima. Ɗan jimm tai tana kallon wayar, sai kuma ta ɗaga takai kunne da sallama nan ma. Malikat Bushirat da idanunta ke cikowa da ƙwalla sakamakon jin muryar Iffah tar-tar a kunenta ta kai zaune tana ambaton sunan ALLAH. Iffah na son tambaya tana jin nauyi, sai kawai tai shiru tana sauraren kalmomin godiya ga ALLAH da Malikat Bushirat ɗin ke ambata daga can.
(Ya rabbi! Wai mike faruwa ne haka?) Ta ayyana a zuciyarta da al’ajabi. Knocking ƙofa da akai ta hanyar danna alerm a dai-dai lokacin ya katse tunanin nata. Ta kai dubanta ga kofar babu alamar zata tanka har aka sake danna alerm ɗin sannan tai ƙarfin halin amsawa da bada umarnin shigowa tana gyara mayafin data yanama kanta.. Hadimar ɗazun ce dai ta shigo ɗauke da ƙaramin tray mai ɗauke da butar shayi. Kanta a ƙasa ta ajiye a inda ya dace tana mai zubewa ƙasa durkushe. “Amincin ALLAH da tsahon rai mai albarka su kasance tare da Zawjata-almilk Barka da safiya”.
Babu yanda hafimar ta iya dole ta miƙe domin bin umarni shine kawai huruminsu. Da kallo iffah ta bita abubuwa masu yawan gaske na son fara mata kutse a ƙwaƙwalwa da zuciya. Ƙwarin gwiwar da take bama kanta akan turesu ya sata miƙewa ta nufin toilet tana mai ambaton addu’ai a bakinta saboda tuna abinda taci karo da shi a daren jiya a toilet ɗin.
Ko’ina tsaf, kuma cikin ƙamshi irin na daren jiya. Sai da ta ƙarema komai kallo fiye da jiya kafin ta ɗage kafaɗa irin na koma miye ta shirya masa. Tsabagen rigima da wuce wuri ko tsageranci za’ace ta haɗa ruwanta mai ɗumi da zuba duk wani nau’in turaren wanka da aka jera domin Shahan-shan ta shige cikin kwamin wankan tai luf. Sai da taji ko’ina nata ya miƙe yanda take buƙata sannan ta fita a ruwan domin fara wanka…
Tsaf ta kammala shirinta cikin doguwar rigar material sky blue da akaima ɗinkin daya fidda ainahin halittarta tamkar ƴar tsanar roba. Rigar ta zauna mata ɗas, siririn mayafin da aka haɗa rigar da shi ta naɗa tamkar yanda larabawa keyi, ta ɗakko after dress shara-shara mai kamar alƙyabba ta ɗora a sama kalar blue sosai. Ta ɗanji babu daɗi na rashin turarurrukanta tare da ita, dan ko waɗan nan kayan ganinsu kawai tai, cikin ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa a zahiri ta dinga kwasar turarrukan da taci karo da su a ɗakin cikin wani ƙyaƙykyawan glass dake kusa da mirror ta dinga zazzagama jikinta har sai da ta gamsu ƙarfin kamshin zai kai duk inda mai rai ke numfashi a sashen sannan ta haƙura. Idanunta ƙyam a mirrorn ta saki ƙayataccen murmushi da kanne ido ɗaya a fili ta furta “Irin wannan haɗuwa haka autar Ummu”. Tai salute ɗin kanta….