Daudar Gora Book 1 Page 70
Ni’imtaccen ƙamshin dake tashi a katafaren ɗakin ta zuƙa ta fesar da cigaba da bin komai daki-daki. Ɗaki kam ya cika a kirasa ɗaki ga masu arziƙin dake ɗaukar duniya gidan zama. Sai dai ta gama ayyanawa a ranta babu wani ƙyale-ƙyale da zatai sakacin da zai ruɗeta har ya dakatar mata da ƙudirinta data fara taka tsanin nasararsa a yau insha ALLAH. Ta saki
kasaitaccen murmushi da ware hannayenta iskar na’urar ac ta busota tare da ƙamshi, idanunta ta lumshe ta buɗe tare da tsuke fuska. Cikin wani kakkausan sauti daya bambanta da nata na baya ta furta.
“Yanzu ne za’a fara wasan na gaskiya. Dodon matsafa MATAN ƘWARAI bisa kanka!!”…
Tun wucewar Malikat Haseenat ya bar falon shima. Tsaye yake jikin windown ƙaramin falonsa na hutawa da babu mai shigarsa sai shi ɗaya tak da amintacen hadiminsa mai gyarasa. Dan a doka ma hatta matarsa bata da hurumin shiga wannan falon a tsari da ƙa’idar masarautar. Hasken daya ƙawata cikin masarautar ya bashi damar iya ganin abubuwan dake kusa daga inda yake, sai dai kuma a zahiri idanun nasa ne kawai ke kallon zuciyarsa sam ba’a nan take ba. Ya kwashe tsahon lokaci a wajen kafin ya warware hannayensa dake goye a bayansa ya furzar da numfashi. Ƙofar ɗakin barci ƙwaya ɗaya dake a falon ya nufa. Shima tsaf yake tamkar anan yake zaman din-din-din. A maimakon kwanciya anan ɗin ma zaune yakai cikin kujerar dake ajiye a gefe domin hutawa kawai. Tun agogon ɗakin na juya sakanni da mintuna har ya koma awanni yana zaune idanunsa lumshe, ya kwantar da bayansa a makarin kujerar dake ɗan juyawa a hankali. A kallon fuska baka isa gane yanayinsa ba balle ka samu damar masa fassara. Bugawar agogon ɗakin mai nuni da cikar ƙarfe biyu dai-dai ta sakashi buɗe idanunsa da ƙarancin hasken ɗakin ya hana damar iya tantance launinsu a yanzu. Agogon ya tsurama ido tamkar mai lissafa daƙiƙun da suka cigaba da motsawa…..
A ɓangaren Iffah wannan lokaci na dai-dai da kai goshinta ƙasa domin yima UBANGIJI suduja a karo na babu adadi. Tun bayan kammala lissafe-lissafenta da ƙidaye-ƙidaye ta zanzare rigar jikinta, ƙaramin akwatinta ta buɗe babu alamar damuwa tattare da ita ta sauya kayanta zuwa abaya. Daga haka ta nufi bayi bakinta ƙunshe da tarin addu’oin da taketa yi tun shigowarta ɗakin. A karan farko data buɗe fanfo da nufin yin alwala saɓanin zubar ruwa sai taci karo da jan abu tamkar jini. Tabbas taji firgici, amma sai tai yaƙi da rauninta wajen cigaba da addu’a da son daidaita harbawar da zuciyarta keyi da sauri-sauri. Tamkar almara kalar jan ya ɓace a idanunta ainahin ruwa ya maye gurbinsa. Numfashi taja ta fesar zuciyarta na tabbatar mata ta ƙara dakewa. Tsaf ta ɗaura alwalarta kuwa ta miƙe, tana ƙoƙarin gyara ɗan kwalinta taji tamkar an gitta ta bayanta. Anan ɗinma dai zuciyarta ta tsinke, amma sai ta cigaba da ambaton sunan ALLAH ta basar. Bata damu da nan wanin abin salla ba, dan tsaftar dardumar da aka ƙawata ɗakin da ita ya gamsar da ita. Mayafinta ta naɗa tai nagartacciyar tsayuwar salla domin fuskantar UBANGIJIN talikai mai jin kukan wanda ma basu fara kukan ba, mai bada kariya ga wanda ya yarda babu abin dogaro sama da shi…
Taja tsahon lokaci a sujidar tana mai zubda hawaye da ƙaskantar da kai ga mai gani a duk inda ka ɓuya. Bayan ta sallame tai zaman karatun Alkur’ani a cikin wayarta dan batajin zata samu Alkur’ani a wannan ɗakin da ƙyaleƙyalen cikinsa ya tabbatar mata zamowa fadar aljanu ba komai bane. Sai da ta gama karance baƙara har zuwa inda suka tsaya a makaranta sannan tai addu’a mai tsawo itama. Sosai taji wata iriyar nutsuwa na ratsa dukkan jikinta, ta sauke ajiyar zuciya da miƙewa. Hankalinta kwance ta haye katafaren lafiyayyen gadon da Shahan-shan ne kawai ya taɓa hawansa a tarihi. Nanma zama tai tai addu’ar barci ya shafe jikinta ta gyara lausasan filos ɗin da aka ƙawata adon gadon da su ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Barci mai daɗi ya fara fisgar idanunta a sannu-sannu sai gata tana sauke numfashi…..
Bayan wucewar saurayin da Kaka ya shimfiɗama sha tara na arziƙi gidan yay shiru. Kamar yanda bai cema Iyyani komai ba itama batace ba, tsahon wasu mintuna sannan ya miƙe ya shiga ɗakinsa. Tashi Iyyani tai ta bisa, dan ta fahimci maganarce baya buƙatar ayi sam..
A ɗakin ma baice mata komai ba har tsahon wani lokaci, ganin haka ta katse shirun da faɗin, “A haɗa maka ruwan wanka?”.
Batare da ya bar abinda yake ba ya jinjina mata kai. Fita tai jiki a sanyaye, babu jimawa ta koma ta sanar masa an haɗa. “ALLAH yay miki albarka”. Ya faɗa kamar yanda ya saba. Ta ɗan ji sanyi a ranta, dan haka ta amsa da “Amin tare da kai” cikin sauke ajiyar zuciya…