Daudar Gora Book 1 Page 63
“Lafiyarki da tsahon zamani su da ɗa tabbatuwa uwa mai share kukan masu kuka”.
Ta-kurya dake kai gwuyawunta ƙasa ta faɗa sakamakon zuwan Uwa gareta a bazata. Kamar ko yaushe, cikin shigarta ta jajayen kaya, ta gyara zaman ƙasaitar ta. Ƙoƙon dake hanunta ta miƙama ta ƙurya. Hannu biyu ta karɓa, ta kafa kai ta shanye abinda ke ciki.
“Tukuycin cika umarninmu na yanka babbar baƙar dabba da kikai ne. Azamarki da himmarki zaisa bazaki taɓa nema daga garemu ba ki rasa Ta-kurya (Wa’iyazubillah 😭).
“Nagode uwa mai share kukan masu kuka”.
Murmushin daya sake munana fuskarta ta saki tana ƙara kalmashe ƙafafu a kujerarta.
“Karki damu ke mai nasara ce. Minene makomar ayyukan da muka barki da su?”.
“Ina kan yunƙurin ƙarasawa. Na kuma samu ƙyaƙyƙyawan labari a majiya mai ƙarfi yarinyar zata koma sashenta. Sai dai akwai zaman sirri dasu Uwar masu gida sukai wanda babu wanda yasan misuka tattauna. Ina dai ƙyautata zaton duk akan komawar yarinyar ne”.
“Kar tattaunawarsu ta dameki. Tabbatar da ƴan leƙen asirinki cikin hadimanta shine aikinki na gaba. Dan kunada yawa masu wannan burin kema kin sani basai na sanar miki ba. Ina kuma tunatar dake rigar can dake a sashen Uwar masu gida. Da zaran ta tare ki kasance ɗaya daga cikin masu janta a jiki. Yardarta gareki ne zai bamu damar amfani da ita wajen cikar burinmu”.
“Na gode da kasancewar ki haske mai haskamin duk wani surƙuƙin da zai iya zamemin duhuwa uwa”.
“Biyayyarki garemu ita ce tushen share kukanki Ta-kurya. Dan haka bazamu taɓa barin kiyi kuka ba maƙiyanki suyi dariya ba. Sai dai su suyi kuka ke ki kasance cikin dariya a kullum bisa nasararsu. Karki shagala ƴar shilar suda nada taurin kai, Karki zama cikin jerin mutane masu raina allura ta zame musu garma. Muna son tasha madarar nan a ƙalla sau uku daga gareki da zaran ta tare a sashenta”. Ta ƙare maganar da miƙama ta ƙurya ƙoƙon da bata san daga ina ya fito ba. Dan ganinsa kawai tai a hannunta tamkar ƙyaftawar idanu. Hannu biyu tasa a wajen amsa tana jera mata kirari da godiya. A hankali ta fara disashewa a idanunta tamkar baƙin hadarin da masha ruwa (Bakan gizo) ya shanye cikin sakanni.
Ta-ƙurya ta sauke nannauyan ajiyar zuciya. Sai kuma ta miƙe da ƙoƙon da Uwa ta bata. A guri na musamman da na’urar sanyi ke aiki ta ajiye madaran, murmushin jin cigaba da tabbatuwar nasararta na cigaba da ƙawata ƙyaƙykywar fuskarta. Ji take a ranta yanzu ne fa za’a fara wasan na gaskiya. Dan dama idan aski yazo gaban goshi masu iya magana kwance yafi raɗaɗi da zafi. Ta jima bata samu irin wannan damar ga uwa ba a ɗan tsakanin nan da mafi yawan lokuta sukafi ganawa cikin ɓacin rai da rabuwa da ɓacin ran. Amma a yau yanda uwa ta ziyarceta ya sakata jin karsashi da ƙarin kwarin gwiwar cigaba da ruguza duk wanda ya cigaba da yunƙurin shiga gaban nasararta
“Humm masu karatu, da gaske fa yanzu ne za’a fara wasan na gaskiya. Ga dai Iffah zata koma ɗakinta. Komawar dake cike da burikan wasu dake zagaye da ita. Buri kuma irin wanda ke kamanceceniya da juna ta fuskar wanzuwa. Manufa kuma kowa da irin tasa. Ita kanta Iffah da nata ƙudirin karku manta. Shin wanene zaiyi nasara ne? Yaya batun su Babiy kuma? Dan maimakon haske komai ƙara cuɗewa yake. Kaka zaiyi wani yunkuri a alamarin kokuwa Barrister zai janye bisa gargaɗin da akai masa shima?. Kumuje zuwa dai dan ba’a fara komai ba sai yanzu