Daudar Gora Book 1 Page 25
Sosai mamaki ya bayyana a fuskokinsu dajin kalaman Babiy da kuma fitowar Iffah da Iyyani ta riƙo suka fito. Baki ɗaya daga cikinsu ta buɗe zatai magana wata ta girgiza mata kai alamar kartace komai. Badan taso ba tai shiru, sai dai ta juya ta fita tana mai danna wayar hanunta da alama wani take ƙoƙarin kira.
Babiy da kansa ya kama hanun Iffah tare da akwatin kayanta ƙarami har ƙofar gida gaban motar da aka tabbatar masa itace ta ɗaukar amarya.. Da gayya Iffah tai gaba zata kifa suna gab da fita a soron kamar tayi tuntuɓe da rigar jikinta dake jan ƙasa. Da sauri hadimai mazan dake tare da su sukai mata runfa da bayansu dan kar wanda yaganta, dan kofar gidan dama cike yake da jama’a, cikin sauri ta gefenta mai sanye da baƙar abaya harda niƙaf tai ƙoƙarin yin kamar zata tarota suka duƙe tare, a hankali ta ɗan ɗago suka haɗa ido, matar dake ƙoƙarin taimaka mata ɗin tai saurin kautar da nata da sukai jajur tare da ɗaukar littafin da Iffah ta saki ƙasa yayin da take kaiwa sunkuye. Miƙewa matar tai, itama Iffah ta ɗauka envelope ɗin da matar ta saki ƙasa dai-dai Babiy na ɗagota. Da baya-baya Sir Fawzan da yay ɓaddabamin shigar mata cikin baƙar abaya da niƙab kamar hadiman masarauta ya dinga jan jikinsa cikin mutane ƴan kallo har ya sulale gaba ɗaya a wajen….
Wannan ne karo na farko da Iffah ta shigo cikin masarautar daular Ruman. Duk da a cikin mota suke kuma har yanzu hawaye basu daina zirara daga idaniyarta zuwa fiskarta ba hakan bai hanata tsarkake sunan UBANGIJI ba, yayin da motocin da suke a ciki suka gama keta katafaren gate ɗin farko zuwa cikin masarautar mai matuƙar girma da hasashe ko kintace bazai iya bayyanawa ba kai tsaye sai al’amarin ya sake girmama zuciyata……..✍
Tabɗi jan🙆🏻 Ga aure dai ya ɗauru tsakanin Tajwar Eshaan Bin Haysam Abdull-Majeed. Da Fareedah Bint Zayyan. Shin itama zata mutunne kamar sauran matansa ko zata tsira? Wacece Uwa? Wacece Ta-ƙurya? Wanene shi kansa Tajwar Eshaan da ƴan ƙasar Ruman baki ɗaya kema kallon Fir’aunan wannan ƙarnin?. Miye dalilin mutuwar matan Tajwar? Shike kashesu? Ko akwai lauje cikin naɗi a kashesun?. amsoshinku duk suna a cikakken littafin nan na DAUƊAR GORA CIKI KA SHATA, dan cakwakiyarfa yanzune ma zata fara😉🤗.
…….Ta ko’ina bayine masu hidima ga wannan basarakiyar daula. Yo basarakiya mana, dan itace masarauta dake mulkin ƴan ƙasa dama sarakunan ƙasar baki ɗaya. Sun sake wuce gate na biyu inda anan ɗin ma dai katafaren wajene da misaltasa babban aikine ga mai hasashe. Ta ko’ina hadimai ne ke kaiwa da komowa maza da mata. Ga wasu irin gine-gine na alfarma da ɗaukar hankalin mai kallo tamkar ba’a cikin ƙasar Ruman ba. dogayen gine-gine ne da abaya sai dai su hangosu daga nesa tamkar yanda suke iya kallon jirgi yayinda yake keta giza-gizai. Ga wasu irin korayen shukoki tako ina tare da shimfiɗaɗen lafiyayyen titi da za’a iya rantsewa yafi kowanne titi dake a cikin ƙasar Ruman. Kasancewarta farin shiga a ganin wannan shimfiɗaɗɗiyar daula saita fara tunanin anyama kuwa a duniyar mutane take? Kokuwa dai mafarki takeyi ne? Dan sam inda take yafi kama da anguwanin ƙasashen turawan da a tv ne kawai suke iya ganinsu cikin film ko labarai da makamantansu…
Har motocin suka samu wajen tsayawa aka fito da ita sam ba’a hayyacinta take ba, bawai ƙawatuwa da tarin ƙyale-ƙyalen da aka zubane kawai ke ɗibar hankalinta ba, akwai wani ɓoyayyen tunani acan ƙasan ruhinta da ƙahon zuciyarta mai alaƙa da tabbatar da abinda mutane ke faɗa akan Daular Ruman ɗin…… Saukar sautin busar sarewa mai zaƙi da daɗin saurare da ya fara tashi a cikin daular Ruman ya sauka cikin kunnenta tare da katse tunaninta ya maidota hayyacinta. Wannan saƙone dake isa zuwa kunnen duk wanda ke a cikin masarautar cewar an iso da _Zawjata almilki_.
Tsawon lokaci sautin na tashi har sai da saƙon ya isa ga kunen kowan da ake buƙata. Daga Iffah dai bata san ma’anarsa ba, dan haka bata ɗaukesa komai ba. Sai ma share hawayen fuskarta data cigaba dayi, dan har yanzu fuskar tata na lulluɓe ne da hular ƙawatacciyar rigar jikinta da zamu iya kira alƙyaba. Sai dai zuciyarta cike take da alwashi mai ban tsoro ga duk wanda zai iya jinsa a kunne. Ta sadaukar zata mutu, amma ba ita kaɗai ba harda Shahan-shan na Daular Ruman, idan an hanata damar bayyanama duniya a ƙwato musu ƴancinsu, sai ya mutu aga wanda zai cigaba da kashesu. A karan farko ta saki murmushi mai ƙayatarwa, irin murmushin data jima batayiba kuwa……..
Babu wanda ta ɗaga kai ta ko kalla a cikinsu har suka gama bushe-bushen algaitunsu dana sarewa. Cikin girmamawa ɗaya daga cikin matan da suka ɗakkota ta matso gab da ita.
“Ran Zawjata-almilki ya daɗe, nan shine sashen Malikat Bushirat. Mahaifiya ga Zakin wannan daula Shahan-shan, Uwa ga duk wani ɗan ƙasar ruman”.
A karo na farko Iffah ta ɗan ɗago idanu ta dubeta kaɗan daga cikin alƙyabar, kanta a ƙasa yake ita a dole bazata iya ko haɗa ido da ita ba domin girmamawa. komai batace da ita ba, sai dai ta dubi katafaren ginin da ya tabbatar mata da maganar matar. Idanunta ta maida ta risinar kawai batare data nuna alamar tama jita ba. Abin mamaki bai nema tsaida bugawar zuciyar Iffah ba sai da suka shiga wannan katafaren gini, bayi sai zubewa suke akan gwiyawunsu tamkar wasu masu neman gafara ko kuma Tajwar Eshaan ɗinne da kansa. Zaman faɗa muku daula da dukiyar dake a wannan sashe ma ai ɓata lokacine, dan haka na baku damar ƙiyastama zukatanku kawai…. (Lol😉😋😆)