Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 19

Sponsored links

★Washe gari ta ɗan danne kaso sittin cikin dari na damuwarta dan kar Ummu ta hanata zuwa makaranta. Sai dai koda taje makarantar ma dai zaune kawai ta kasance badan ta nutsu a fahimtar komai ba har aka tashi. Kanta tsaye ta fito domin samun abin hawa a bakin gate kamar sauran ɗalibai. Da ƙyar ta samu tare da wasu da suke kusan a anguwarsu, sai dai zasu rigata fara sauka…

A hankali wata baƙar mota dake fake ɗan nesa da makarantar tasu ta fara bin bayan mai Mototaxi ɗin da sam shi hankalinsa baima kai ba. Haka suma su Iffah babu wanda ya kula da motar. Da mai motar ya fahimci zasu zargesa sai ya canja salon bin nasu. A haka har aka sauke abokan tafiyarta. Motar ta cigaba da binsu har titin anguwarsu, anan aka dakata har mai Mototaxi ɗin ya shiga ya kai Iffah ya juyo zai fita suka tsaidashi……….✍

Kamar wasa Iffah na shigowa gida ta zube kwance tana rawar sanyi, ga jikinta ya ɗauka matsanancin zafi. Ummu bata kawo komai a ranta ba game da ciwon Iffah sai tunanin ranar da ake ƙwallawa ce ta washeta. Da ƙyar ta tilastata tai wanka, taci abinci kaɗan ta ajiye. Maganin zazzaɓi Ummu ta bata tasha, daga haka ta koma ta kwanta ranar ko Islamiyya bataje ba.

Da dare firgita data dingayi saboda munanan mafarkai ya sa kusan kowa bai rintsa ba a gidan sai gab da asuba. Da barci yaɗan figeta saita tashi a firgice har sai sun rufeta da addu’oi take samun nutsuwa ta sake komawa barci. Al’amarin ya tsayama kowa a rai, sai dai ganin ta tashi ragal da asuba tai salla sai sukaita mamaki. Dan bazaka taɓa tsammanin itace a daren jiya ba.

Da safe koda tace zataje makaranta hanata Babiy yayi, acewarsa ma asibiti zasuje da Hanash. Kasancewar Iffah da rashin son asibiti sai ta turje akan itafa ta warke, dama jiyan rana ce (ta fake da abinda Ummu tace). Ganin harda ƴan kwallanta Babiy yace to inhar zazzaɓi ya sake dawowa a yinin yau dole suje asibitin nan. Da sauri tace ta yarda. Bayan wucewar Babiy tai ta ɗan ƙarfafa kanta harda taya Ummu aiki, duk da yanda takejin yanayinta babu daɗi haka tai ƙudirin shirin Islamiyya idan lokaci yayi, tana ɗaki kwance bayan idar da sallar azhar sai ga kiran malaminta Fawzan, wayar kawai ta tsurama ido tamkar bazata ɗauka ba harta katse, wani kiran ya sake shigowa shima harya katse bata ɗaga ba. Duk da zumuɗin son ganin kiran nashi da take ciki a kusan kwanaki uku sai taji hanunta ya mata nauyin ɗagawa a yanzu daya kira… Shigowar saƙo ya katse mata tunani, ta kai hannu kan wayar ta ɗauka kamar mai tsoro…

_“Fareedah ga dama ta biyu ta sake samuwa, Idan kinga saƙona kiyi ƙoƙarin fitowa kafin Four”._

A zabure ta miƙe jikinta na tsuma ta hau shirin Islamiyya, tare da tattare dukkan takardun bayanan da take ta faman adanawa harma da waɗanda ta ƙara haɗawa a kwanaki ukun nan.

“Ummu zan wuce Islamiyya”. Ta faɗa lokacin da take ƙoƙarin saka takalmi a ƙafarta Ummu na tsakar gida tana alwalar sallar la’asar.

 

“Ke da baki da lafiya auta”.

 

“Ummu naji sauƙi wlhy, kinga saukarmu ya kusa babu buƙatar na fara wasa ai. Malam nata mana gargaɗin hak……”

 

Sauran maganar ya maƙale a harshenta sakamakon tashin sautin busa mai nuni da isowar jama’ar masarautar Daular Ruman. Tamkar an daki kan Iffah da guduma haka taji wani dummm! A cikin kunnenta har suka ƙarasa shigowa cikin gidansu jinta bai dawo ba. (Shin tsoro ne? Ko firgici?) bata san wanene ya risketa ba…… Taɓata da Ummu tayine ya sata jan kakkauran numfashi tare da kallonta. Jikin Ummu ne ke rawa, idanunta kam tuni sun tara ƙwalla. Iffah ta shiga girgiza mata kai alamar kar tai kuka, ta sake damƙe hanunta cikin nata tare da maida kallonta garesu rai ɓace, dan ta ɗauka alwashin a wannan karon komi sukazo da shi sun tara sun samu, sai dai a kasheta…

“Mi kukazo yimana a gida kuma? Ko kun dawo muma ku idasa kashemu tamkar yanda kuka halaka min ƴan uwana da tsafink……”

Da sauri Ummu ta danne mata baki da tafin hannunta tun kan ta ƙarasa faɗa. Kai take girgizamata cikin rawar jiki. Da ace ba Ummu bace babu abinda zai hanata ta ture hanunta ta ƙarasa abinda ta fara faɗa ko zata samu salama a ranta. Sai dai kuma bazata iya ba, dan haka ta shiga yima Ummu alamar roƙo da magiyar ta barta amma taƙi yin hakan…

Basamuden nan ne na kullum mai riƙe da bulala ya daka mata tsawa. Da sauri Ummu ta sakemata baki, sai dai ta jawota jikinta ta ƙanƙame. Iffah jitai zuciyata ta ƙara hautsunowa, a matuƙar zabure ta sake buɗe baki zatayi magana ya dakatar da ita…

“Ke ƴar talakawa lura da inda kike. Bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane. Idan taƙamarki tsageranci tamkar ƙiftawar ido za’a sauke miki shi, a kuma shafe babinku daga ke har iyayen naki a doron ƙasa”.

Hasala iya hasala Iffah tayi, Kukan da Ummu ta fashe da shi ya hanata cewa komai ta juya gareta jikinta na rawar shiga tsananin ɓacin rai, kanta take juyamata alamar karntace komai…..

“Umm….”

“A’a Iffah! Ina umartarki karki ce komai”.

“Kibarta tace ɗinma yanzu harshenta ya zama datsatstse a gabanki.”

Kafin Ummu dake girgiza kai tace komai Babiy ya shigo tamkar an jehoshi, da alama dai wanine ya sanar masa da zuwan jama’ar masarauta gidan nasa. Ko sau ɗaya basu bashi damar cewa komaiba suka isar masa da saƙon kira daga daular ruman.

 

“Innalillahi…..” Iffah ta shiga ambata ita da Ummu, dan sunaji a ransu tarihine dai yake ƙoƙarin maimaita kansa, hawaye masu tsananin ƙuna da ɗaci na gangarowa bisa ƙyaƙyƙyawar fuskata Babiy da shima dai yasan labarin gizo bazai wuce ƙoƙi ba. A gaban idonsu aka wuce da Babiy Daular Ruman a karo na uku, tare da barin wasu dakaru a ƙofar gida ta hanyar hana duk wani mai yunƙurin fita daga gidan. Haɗe kai kawai Iffah da Ummu sukai suna kuka, dan shi kaɗai suke da damar yi ɗin..

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button