Daudar Gora Book 1 Page 124
Iffah ta ambata a karon farko numfashinta na barazanar barin gangar jikinta, computer ɗin tai ƙoƙarin singumowa gaba ɗaya dan maidata cinyarta akai rashin sa’a ta danna abinda bata sani ba kamar ƙiftawar ido suuu ta shige cikin table ɗin. Ƙwaƙwalwarta neman bugawa tayi tsabar rikicewa, ta shiga leƙe-leƙe a wajen sai dai babu abinda ta gane. Babu shiri ta zabura hanyar da Tajwar Eshaan ya bi tana haɗa hanya…..
A ɓangaren Tajwar Eshaan kam da kyar ya iya kai kansa ɗaki, dan jefa kafar kawai yake batare da yasan inda yake takawa ba. A ƙasan lallausan carpet ɗin ɗakin ya zube yana mai jingina jikinsa da yay sharkaf da zufa jikin gado, duk wata addu’ar da tazo bakinsa ambata yake, a haka Iffah data gano ɗakin da ƙyar ta shigo a ɗimauce. Idanunsa dake a lumshe ya buɗe a hankali suka sauka a kanta. Dukkan ƙarfin halinsa da jarumta ya tattaro ya adana tashin hankalin da ke tattare da shi. A ɓangaren ta itama ruɗanin da take ciki ya bada gudunmawa wajen makantar da ita yanayinsa, cikin rawar harshe idanunta dake tsiyayar hawaye a kansa ta durƙushe ɗan nesa da shi.
“Dan ALLAH na roƙeka ka faɗamin wanene kai? Miye alaƙar ka da Ajmaal?!”.
Babu alamar zai tanka mata, sai dai idanunsa dake sake rinewa jajur na tsaye a kanta ƙyam. Tsahon wasu mintuna ya lumshe su da sake buɗe su a kanta yana cije lips ɗinsa. Ya kauda fuskarsa cike da ƙarfin hali, da son saisaita muryarsa, a maimakon ta samu amsar tambayarta sai saɓaninta ya fito da ga garesa.
“Ki canja madarar da kika bani da wadda ke akan dining. Hatta kofin da na sha daga cikinsa karki bari”. Ya ƙare faɗa a wahale cikin cije baki da rumtse idanunsa.
(Iffah ki nutsu karki tonama kanki asiri) zuciyarta ta ayyana mata. Idanunta ta rumtse da karfi tana gyaɗa kai kamar wadda ake faɗamawa a cikin kunne. Sai kuma ta shiga goge hawayen nata da maida kallonta garesa a yanayin son kare kai.
“Ni ba batun madara na tambaye ka ba. Wanene Ajmaal?!!!”. Ta faɗa a matuƙar tsawace.
Birkitattun idanunsa ya rumtse da ƙarfi dan sam baya son hayaniya, balle ma a irin wannan halin da yake ciki a yanzu. Ya buɗesu kanta shima a fusace har sai da kallon cikinsu ya sakata zabura. Shima cikin tsawar da fisgar numfashi ya ce, “Babu abinda zai amfanar da ke a jin amsoshin da kike buƙata a yanzu. Kije kiyi abinda nace!! Kije!!!!”.
Ba ƙaramin firgici Iffah ta shiga da yanayin nasa ba. A zabure kuwa ta miƙe, batama san taya ta nufi ƙofa ba ganin kanta kawai tai a falo, harta nufi ƙofar lifter ta dawo da baya, tambulan ɗin madarar ta ɗauka, ta nufi dining wajen wanke hannu ta juyeta, kofin ta ɗauraye jikinta nata ƙyarma, gaba ɗaya ta nema jarumtarta ta rasa, sai da ta tabbatar ya fita ta dawo kan dining ɗin inda aka shirya break fast, madarar dake a jiye a wani tambulan ta ɗaga ta juye a wanda ta wanke ɗin, ta sake komawa ta wanke wannan, sai kuma ta rasa ina zata ɓoyesa kamar yanda zuciyarta ke bata shawara. Da kyar ta samu nutsuwar samun wajen makalasa, ta dawo harta sake nufar hanyar fita ta sake dawowa da baya, kofin da ya sha madarar ne, shima ɗauka tai ta wanke ta zuba sabuwar madarar ta kauraya ta maida inda ya sha. Sake nufar ƙofa tayi sai kuma ta sake dawowa ta nufi ɗakin dai da ka ganta kasan tana a cikin halin ɗimuwa….
A ɓangaren Tajwar Eshaan kam tana fita tari ya sarkesa, jin saukar abu a tafin hannunsa da yake tare bakin ya sashi saurin kallon hannun. “Jini..” ya ambata a hankali saman lips, sai kuma ya saki wani irin wahalallen murmushi da mai da kansa ya kwantar jikin gadon yana ambaton “Sunci nasara, sun sami nasara ta dalilinki *_My Sohaa_*….” tari ya kuma sarƙesa a hankali, sai dai murmushin na nan maƙale a fuskarsa har yanzu, sai faman lumshe idanunsa da suka birkice yake yana ƙoƙarin buɗesu da ƙyar fuskar Iffah da hawayenta ne tsaye ƙyam a cikinsu. Ba mutuwa yake tsoro ba a yanzu, baya da ƙurar da zai barta a ciki, ya tabbatar itace zata sha wahala, wahala irin wadda ba ita yay mata tanadi ba. Hakanne ya zaburar da shi, yaja jikinsa da ke saki gaba ɗaya da ƙyar zuwa telephone..