Daudar Gora Book 1 Page 121
Kai hadimin ya jinjina yana mai sake ƙan-ƙan da kai, ya fara zayyano komai tiryan-tiryan tun daga randa aka ɗauke Iffah sashen har zuwa yau ɗin nan da yake gabansa. Ya kare da faɗin, “Idan na faɗi abinda ba shi shugabana ke buƙatar ji ba ina mai neman afuwa”.
Idan gunki ya motsa bayan ƙare abinda ya buƙaci ji to ya motsa. Hadimin dama dai baya tsammanin samun sharhi ko tambaya ko fashin baƙi daga abinda ya faɗa, dan haka yaja bakinsa yay shiru yana ɗan satar kallonsa ta gefen ido. Ba yau ya fara ganin Tajwar Eshaan ɗin ya danna wani abu a gefen kujerar da yake zama computer ta bayyana ba kamar yanda yayi a yanzu, sai dai a iya hasashensa da dube-dube idan yana gyaran saman ya kasa gano komai……
Hukuncin da kaka ya yanke, sakamakon tashin hankalin da suka kwana a ciki shi da Ummu da Iyyani tun da sassafe suka fito da nufin komawa gidan Babiy na daular ruman gaba ɗayansu. Kaka ya gama shirya tunkarar kowa gaba-da-gaba a yanzu, dan haka babu ko ɗar tattare da shi. Saurayin nan na kwanaki dake ƙoƙarin shigowa layin gidansu yay saurin taka birki idanunsa a kansu. Tabbatar da su ɗinne dai ke tafe a ƙafa ya sashi ɗaukar wayarsa da sauri-sauri ya latso wata lamba. Sai da tana gab da tsinkewa aka ɗaga, da ƙyar ya iya haɗa haruffan sallama bai jira an amsa masa ba ya ɗora da faɗin, “Oga abin mamaki gasu nan suna fitowa da alama ma garin zasu bari”.
“Woow interesting”.
Aka faɗa daga can cikin nuna ci da birgewa. Sai kuma aka ɗora da faɗin, “Maza ka juya ka koma kan ainahin hanya kafin su isa. Ka tabbatar nan da mintunan da basu wuce hamsin ba na gansu a gabana”.
“An gama boss”.
Saurayin ya faɗa da tsantsar girmamawa. Sam su Kaka dake tafiya hankalinsu bai kai kan motarba saboda Ummu dake tafiya a wahale, idan ma ta taka ɗaya biyu sai sun tsaya ta huta kafin su cigaba. Yayi jira na kusan mintuna goma sha ɗaya kafin su iso inda tuni ya iso shi yay fakin. Da sauri ya fito daga lungun daya laɓe hanunsa riƙe da leda yana ɗan cillawa yana ƴar wakarsa. Kamar wani shiri sai ko idon Kaka dake ma Ummu nasiha ta daure su ƙarasa akan wannan saurayi. Yay ɗan jimm alamar shan jinin jiki, sai kuma ganin yanda saurayin ya gittasu babu alamar ya gansa ya sashi zabura.
“Ƴan samari na ce ba…?”
Kamar saurayin bazai kula ba sai kuma ya juyo a ɗan yatsine yana faɗin, “Kace mi….?” sai kuma ya ƙi ƙarasawa da nuna alamar shock kamar gaske. “Ya ALLAHU wa nake gaji haka kamar Baba?”. Kaka ya sauke ajiyar zuciya da jin shakkunsa gaba ɗaya ya gudu yay ɗan murmushi. “Kaga ja’iri ni ne ɗin dai, yaushe haka a gari babu labari?”. Kai a sunkuye saurayin ya shafa ƙeya yana murmushi. “Afuwa kaka uziri ne ya ciyoni har nai ƙudirin shallakeku a karo na biyu batare dana leƙa ba. Yanzu haka ma nan jirana ake saƙo na amsa anan ɗin fatana na kai Dahab (Daular ruman) kafin cikar awa ɗaya da rabi”.
Cikin jin daɗi Kaka yace, “Kai Alhamdullah da wannan zance. Ka ganmu muma can ɗin muka nufa a she da rabon ba sai mun sha wahala ba na jiran mota ma”.
Saurayin ya ɗago irin da mamakin nan, irin sai yanzu ya lura da su iyyanin nan. Gaishesu ya fara da ban haƙurin bai lura da su ba ne wai. Iyyani ta amsa masa da kulawa tana faɗin babu komai.
“Idan hakane Baba ai ku shiga kawai mu wuce, gaisuwar ma a karasata a hanya”.