Daudar Gora Book 1 Page 110
Abu Zainab kam a yau Kaka ya fara bashi tsoro. Sai dai ya danne bai yarda ya nuna ba. Kaka ma ya fahimci haka amma ya kanne, sai jakkar ya tura ma Abu Zainab yana faɗin, “Wannan sune kuɗin dake tare da takardar”.
Nan ma dai da mamaki Abu Zainab ke kallon kuɗin, kuɗine masu yawa sabbi ƙal sai ƙamshi suke na sabunta. “Baba waɗan nan mutanen kuwa anya….”
Kaka yay murmushi mai bayyana haƙora. Sai kuma ya ɗan kalli sashen da Ummu ke zaune. Tuni ta tashi batare da sun farga ba har Iyyani.
Lokacin da kaka yayi ma Abu Zainab rakkiya sukejin halin da ƙasar ke ciki, dan shima Abu Zainab kasancewar fitowar sassafe yayi sannan komai bai fasu ba. Hankalinsu yayi matuƙar tashi dan basu san wacece a cikin matan sarkin ta rasu ba.
“Zakariyya zama bai ganni ba, dole ne mu wuce tare kenan, kayi haƙuri kaɗan jirani anan ina zuwa”.
Kaka bai jira cewar Abu Zainab ba ya koma gida da sauri, koda su Iyyani sukaga a yanayin da ya shigo suma hankalinsu ya tashi, amma tambayar duniya yaƙi ce musu komai kan abinda ya farun, sai cemusu da yay shima zaije Daular ruman ne.”. jin wannan furucin nasa yasa jikin Ummu fara rawa, a hankali ta zube ƙasa dan zuciyarta ta gama bata kodai ta rasa Iffah ko su Babiy. Dama yau kusan gabbanin asuba tayi mafarkin Iffah na kuka da kiranta tazo ta ceceta, sai kawai ma zuciyarta tafi karkata akan Uffan
Su Kaka sun iso daular ruman a harmutse, dan ƴan zanga-zanga nata da ɗa karuwa harma abin na bama mutane mamaki. Yayinda jami’an tsaro tuni sun fito ta kowane titi na masarauta sun tare. Da ƙyar suka samu ƙarasawa gida, kasancewar ana aikowa gidan domin halartar jana’iza yasa Kaka yay tunanin wannan ma indai Iffahr ce zasu aiko. Dan haka suka shiga tambayar ƴan anguwa amma kowa na tabbatar musu babu wanda yazo. Hankalin Kaka ya tashi fiye da farko, dan kuwa dai bayan wannan hanyar babu wata mai sauƙi da zai iya ji sai abokinsa dogon yaro da ke cikin masarauta. A yanda kuma garin yake hakan abune mai wahala a garesa kenan……
Yanayin da aka wayi gari a ƙasar bai hana su Barrister fitowa ba, sai ma lokacin shi yasan abinda ke faruwar, al’amarin ya taɓa masa zuciya, dan ta wani fannin case ɗinsa tamkar kacokal yanada alaƙa mai ƙarfi ne da abinda ke faruwar. Har yaji yana tsoron ace yarinyar ce ma ta rasa ran nata. Dan dole dai ya daure ya isa inda ya nufa. A yau dai bai samu Sayyid Faizul-Anwar a falon ba, sai dai kasancewar an san da zuwansa ya samu tarbar data dace. Bayan zaman kusan mintuna arba’in Sayeed ya fito cikin shigar jallabiya, cikin girmamawa Barrister ya gaidashi, ya amsa masa da kulawa shima yana masa barka da zuwa. Suna tsaka da gaisuwar cikin yaran Sayeed ya shigo ya isar da saƙon zuwan wasu baƙin. Damar shigo da su ya bada dan yasan da zuwansu, daga haka ya maida hankalinsa kan Barrister.
Barrister yayi matuƙar mamakin ganin baƙin, sai dai ya danne hakan dalilin kallon da suke masa matsayin Barrister Akeem. Gaisuwa sukai ta mutunta juna, har suna tsokanarsa da cewa shine idonsu na gari. Murmushi yayi yana rissinar da kai alamar girmamawa. “Kar kuji komai ranka ya daɗe, a komai muna tare da ku kuma zamu kare mutuncin ku”.
Sosai suka nuna jin daɗi da zancensa. Nan suka shiga kwarzantashi. Shi dai nasa murmushi ne a zahiri, a kasan rai kuma yana matuƙar mamakin abokinsa da ɓoyayyun ayyukansa. Dan bai taɓa tunanin Barrister Akeem zai iya irin waɗan nan ayyuka ba…..
“Barriter ina alkawarin mu?”.
Sayeed Faizul-Anwar ya katse masa tunani. Ajiyar zuciya yaja a ɓoye, sai kuma ya muskuta yana murmushi da taɓa bag ɗin daya shigo da ita. “Ranka ya daɗe komai yazo hannu fiye ma da yanda kuke buƙata. Sai dai kafin mukai ga nan ina son nace wani abu saboda wasu dalilai”.
“Faɗi kanka tsaye Barrister baka da damuwa akan hakan”.
“Nagode ranka ya daɗe. Bawani abu bane mai girma akan dai shi wannan case ɗinne. Komai dai gashi na gani anan kuma na tattaro, sai dai yanda aka bani aikin a dunƙule ina ganin ya kamata nace wani abu duk da dai naga komai a kansa, amma saboda nasan inda duk ya kamata na toshe a ramukan da zasu iya yunƙurin buɗewa koma su buɗe ɗin yasa nake son bada shawara bisa wani hangena”.
Shiru kamar bazasu ce komaiba. Sai dai sun maida dubansu ga Sayeed Faizul-Anwar, kai ya gyaɗa musu alamar tabbatar da babu matsala, dan haka kusan a tare suka sauke numfashi, kafin ɗaya a ciki ya shiga faɗin. “Barrister mun yarda da kai, sai dai ka sani koda baka san komai akan case ɗin nan ba bazamu taɓa bari wani rami a buɗe mana ba koya buɗe maka, zamu kasance a bayanka a kowanne lungu da saƙo na ƙasar nan.”