Daudar Gora Book 1 Page 11
…..Baki ta murguɗa da juya idanunta farare tas tamkar madara cikin nasa da ya kafeta da su. “Inma kai mayene to wlhy bazan ciyu ba, Babiy kullum addu’a yake min shi da Ummu”. Tana gama faɗa tabar wajen.
Yaransa na waccan ranar ne dai yau ma a tare da shi. Kuma suma sarai kalaman Iffah da bazasu manta muryarta da wuri ba ta shiga cikin kunnuwansu. Dama sune suke dubama yaran dake tare da su books ɗin, shi ko yana biye da su ne kawai da binsu da idanu. Ɗaya daga cikin yaranne ya nuna littafin da Iffah ta ɗauka, su kuma kasancewar suna ɗakkoma sauranne sai shi da kansa yay yunƙurin ɗakkowa kafin su suyi hakan. Yunƙurin zagayowa wajen Iffah ɗaya daga cikin yaransa yayi, dan yay alƙawarin yau sai ya daddala mata mari, amma sai ya dakatar da shi ta hanyar yima ɗayan alamar ya tsayar da shi da ido. Da sauri wancan da shima yake jin kamar suje su haɗu su faffasa mata baki ya kira sunan wancan.
“Azaan!”.
Cak ya tsaya tare da rumtse ido da cije baki dan yasan dai ogane zaisa Fakhir ɗin ya dakatar da shi. Gashi harya hango Iffah dake gaban mai biyan kuɗi. Dole ya haƙura badan yaso ba, amma yaci alwashin duk randa suka sake haɗuwa da yarinyar can babu oga sai ya mata karyawar gasashshiyar masara danta tabbatar itace zata gujema haɗuwarsu ba su ba kamar yanda ta faɗa.
ak ya tsaya tare da rumtse ido da cije baki dan yasan dai ogane zaisa Fakhir ɗin ya dakatar da shi. Gashi harya hango Iffah dake gaban mai biyan kuɗi. Dole ya haƙura badan yaso ba, amma yaci alwashin duk randa suka sake haɗuwa da yarinyar can babu oga sai ya mata karyawar gasashshiyar masara danta tabbatar itace zata gujema haɗuwarsu ba su ba kamar yanda ta faɗa.
Iffah dai tuni ta biya kuɗin littafi daya cinye mata duka kuɗinta babu ko na bawa mai Mototaxi (napep). Sai mita take a ranta Littafin yayi tsada, koda ta fito ta iske mai Mototaxi ya cika yayi taf. Tana isowa inda yake hannu kawai ya miƙa mata alamar ta bashi kuɗinsa ya wuce. Fuska ta ƙyaɓe ta cikin niƙab ɗinta tana wani kif-kif da idanunta da kawai yake gani. “Oh oh kaiko duk daɗin asara ai ta jira samu ko? Idan mukaje inda zani nace maka bazan biyaka bane?”.
A fusace yana mai dalla mata harara yace, “Na fasa kaiki, dalla malama bani kuɗina kije ki hau wata. Kuma har na zaman danai anan sai kin haɗamun”.
“Lallai sannu shugaban ɓarayin Ruman. Saboda Babiy yamun baki ko? Idan kaga zaka ɗaukeni muje na baka kuɗinka ka daukeni, in kuma zaka zauna wage baki kana ihu ne na tare wata na hau ka biyoni a baya dan bani da shi anan sai naje gida”.
“Baki da hankali”. Mai Mototaxi ya faɗa a matuƙar fusace yana fitowa. Harga ALLAH Iffah ta tsorata, dan tasan wannan mai zubin samudawan ƙarnin farkon fyaɗa daya zai bazar da itane a titin nan sai dai a kaima su Ummu gawarta. Amma tsabar ƙarfin hali sai faman fiki-fiki take da idanu da faɗin, “To sai kayi duk abinda ma zakayi mana”.
“Hakama kika ce?”. Ya faɗa yana matsota. Jikinta taja baya tana wani zazzaro masa manyan idanunta masu matuƙar sheƙi tamkar ta tara ruwan hawaye a ciki, “Idan hanunka ya taɓa koda abayar jikina sai na ɓallashi! Idan kuma ka isa ka gwada”.
“Kan uban can kayyasa, ke yarinyar nan kin san wanene ni kuwa? To dan ALLAH gwada ɓallamin hanun nagani”. Ya faɗa yana yo kanta da gaske. Securitys ɗin dake a bakin bookshop ɗinne sukai saurin taresa, dama dai ganinsu yasa Iffah wannan hura hancin, ganin ta samu yanda takeso baki ya ƙara buɗewa ta buɗe baki zata cigaba da tsiwa idanunta suka sauka a kan mutumin nan. Yanayin takunsa na isa da ƙasaita kawai saka rawa a zuciyar Iffah yake, sai dai kasancewarta yarinya mai ƙarfin halin tsiya da rashin son a ga gazawarta yasa baka isa ganin wannan tsoron ba a kan fuskarta. Janye idanunta tayi tamkar bata gansa ba, shima sai ya cigaba da takowa tamkar bai ganta ɗin ba yaransa da tawagar yara kusan goma sha biyar biye da su. Kamar waccan ranar yau ma sanye yake cikin suit da sukai matuƙar fidda ƙyawun halittarsa ta tsayayyen mutum, saɓanin ranar na yau baƙaƙe ne, sai dai sunyi matuƙar dacewa da lallausar farar fatarsa mai matuƙar sheƙi da ɗaukar idon mai kallo. Ga mayataccen ƙamshinsa irin na ranar mai saka zuciyar mai shaƙa raunana da nutsuwa. Harya gotasu zai wuce a binsa sai kuma ya tsaya cak, hannayensa duk biyu ya zuba a aljihun wandonsa tare da juyowa. Ita ya fara kallo, sai kuma ya janye lulu idanunsa masu tabbatar da kwarjininsa da kamewarsa ga duk wanda ya kallesu ya maida kan securitys ɗin nan dake riƙe da mai Mototaxi ɗin har yanzu. Azaan daya fahimci mi ogan nasu ke nufi yay saurin faɗin “ku sakesa” duk da har cikin rai baiso hakan ba. Babu musu suka sakesa, shiko sai huci yake idonsa akan Iffah data juyar da kai gefe irin bata sanma mi’ake ɗin nan ba. Hanunsa ɗaya ya zare daga cikin aljihunsa ya ɗan ɗaga rigar suit ɗin tasa. Kuɗine masu yawa ya zaro ya miƙama mai Mototaxi ɗin. Cikin rawar jiki ya kai rissine kamar gwiwarsa zata taɓa ƙasa ya amsa yana godiya kamar zai haɗiye harshensa. Kansa kawai ya ɗauke zai juya suka sake haɗa ido da Iffah. Baki ta tura gaba tana fiki-fiki da idanu da sake ɗauke kanta…
Takaici kamar ya kashe su Azaan. Babu wanda a cikinsu bai harari Iffah ba kafin subi bayan ogansu da tuni yabar wajen. Mai Mototaxi da bakinsa ke washe uwa gonar audiga ya kalla Iffah. “A to hajjaju taho na kaiki koda karshen Daular Ruman ne ma”. Wata banzar harara ta balla masa da jan tsaki tabar wajen. Cike da takunta na nutsuwa ta gitta motarsu dake ƙoƙarin barin wajen. Azzan yay ƙaramar ƙwafa, a ransa yana raya shine zai zama sanadin nakasa yarinyar nan kuwa wataran. Mai gayya mai aiki kam da gaba ɗaya zuciyarsa ta gama tabbatar masa yarinyar nan aljanar ce idanunsa ya lumshe a hankali yana mai ƙara gyara zamansa na ƙasaita tamkar ba’a mota yake ba….