Daudar Gora Book 1 Page 1
Kwanakin mako uku kenan da shuɗewar komai amma komai ya kasa mantuwa a zukatansu. Kuzari ya samu rauni kamar yanda dukkan karsashi ya gujema gangar jiki. Duniya ta masu ƙunci, ƙunci irin wanda har ƙarshen numfashi da wahala su manta. Farin cikinsu ya zama fansar damuwar wasu, wasun da kansu kawai suka sani basa kallon na ƙasa da su. Da ace ƙarfin iko a hanun kowanne ruhi yake a zahirin rayuwa, da ita ce zata zama mace ta farko a duniya mai ƙarfin ikon da zai girgiza zukatan kowaɗanne irin azzalumai. Kafin shuɗewar makwanni uku masu ɗauke da kundun baƙin ciki rayuwar ahalin Mal. Zayyan tamkar dutsen lu’u-lu’u suke a cikin tsakkiyar zinare. Ba magana ake akan dukiya ba, dan tana a cikin jerin abu mafi rauni da suke ɗauka ko amsa sunan ko kallo farin ciki. ana magana ne akan kammaluwar ahali masu matuƙar ƙaunar juna zunzurutu mara gauraye. Masu kuka a yayin zubar hawayen ɗayansu, masu dariya a yayin farin cikin ɗayansu, masu jiyya a yayin ciwon ɗayansu, masu zama komai a lokacin da komai yake abu ɗaya a hanunsu.
𝕽𝖚𝖒𝖆𝖓 babbar ƙasace a tsakkiyar wani babban tsibiri a wani ƙarni daya shuɗe kafin yau, ƙasace mai yawan arziƙin zinare yankin nahiyar Africa. Ƙasar Ruman nada babbar Daular mulki data ƙunshi manyan sarakuna masu ɗunbin tarihi kala-kala da labaransu bazai taɓa kasancewa shuɗaɗɗe ba a duniya. Ba arziƙin zinare ne kawai suke da shi ba, sunada nau’i-nau’in kayan itatuwa da wajajen noma harma da kiwon dabbobi da akan fita da su ƙasashe daban-daban ko’a shigo cikin ƙasar a saya. Al’ummar wannan ƙasa sun kasance wasu irin ƙyawawan mutane masu kwarjini da cikar haiba, sai dai duk da ƙyawun da mafi rinjayensu ke da shi hakan bazai hana a samu masu ƙarancin ƙyawun ba. Sunada yawan addinai da ƙabilu tamkar kowacce ƙasa, sai dai mafi rinjayen ƙabila sune masu yara yaren rumanci, sannan addinin musulinci yafi kowanne addini ƙarfi da rinjaye. Abu mafi mamaki a ƙasar ta Ruman shine, duk da ƙarfi da rinjayen da addinin musulinci ya samu suna girmama al’adunsu na kaka da kakani musamman ƙarfin iko. Ƙarfin iko nada matuƙar tasiri a ƙasar Ruman ainun, hakama al’adu da girman masautunsu na taka rawar ganin hana dukkan abinda turawa suka zo musu da shi taka rawar gaban hantsi a garesu bayan ilimin boko, duk da suma sun shiga cikin ƙangi na mulkin mallakar turawan a ƙarnin daya shuɗe. Babu wani mulki dake da tasiri sama dana sarautunsu tun a farkon ƙarnikan baya har zuwa yau ɗin nan da suke rayuwa bisa mulkin mallakar sarakunan dake mulkin mallakar su.
𝕯𝖆𝖚𝖑𝖆𝖗 𝕽𝖚𝖒𝖆𝖓 itace babbar masarauta da dukkan masarautu ke ƙarƙashin ikonta bama su talakawa kaɗai ba. Itace tamkar fadar shugaban ƙasa a wasu ƙasashe. A maimakon mulkin siyasa, su 𝐃𝐀𝐔𝐋𝐀𝐑 𝐑𝐔𝐌𝐀𝐍 itace babbar masarauta mai faɗa aji akan komai da kowa na ƙasar Ruman, komai yana tabbatuwa ko akasinsa da ƙarfin ikon sarki mai mulki a kujerar wannan daula. Bama gasu talakawa ba, babu wata masarauta a cikin kasar Ruman data isa koda ɗaga murya a bayan idon Daular Ruman saboda karfin ikon mulkin 𝐒𝐡𝐚𝐡𝐚𝐧-𝐬𝐡𝐚𝐧 (King of kings). Ƙarfin mulkin wannan Daula yakai a duk faɗi da ƙasar Ruman ke dashi babu wani mahaluki da zai iya faɗar siffa kai tsaye ko kamanni na sarkin da duk zai mulki daular ruman tun zamanin ƙarnikan baya, saboda tsantsar girmamawa da akema sarakunan wannan Daula ko iya ɗaga kai a musu kallon ƙurulla na kusa babu maiyi, daga nesa kuwa fuskokinsu ababen kwarjinine irin na masu mulki da a ranar wasan al’ada na kowanne shekara ake iya ganinsu a zahiri daga nesa bisa keken doki. A tsari da ƙa’idar daular ruman dukan yarima mai jiran gado daya shiga shekaru bakwai na girma za’a ɗaukesa kowa ya daina ganinsa, a sirrance zaiyi ilimin zamani dana addini dama duk wata rayuwarsa irin ta kowa. Bayan cikar shekarun girma a garesa za’a fara bayyanasa ga sarakunan sauran masarautu cikin shigar da ƙwayar idonsa kawai zasu iya gani. Nuna yarima mai jiran gado ga sauran masarautu na nufin alamar mahaifinsa zaiyi murabus kenan ya ɗaurasa a karagar mulki basai bayan ransa ba. Sarkin kuma da baya buƙatar hakan bazai taɓa bayyana yarima ba ga kowa har sai bayan mutuwarsa.
𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐢𝐛𝐧 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐌𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝 shine sarkin daular ruman daya shuɗe aka ɗora ɗansa ɗaya tilo bisa karaga. Shi kaɗai ya haifa a duniya, shine kawai magajinsa sai mata huɗu da saɗaka daya bari. A yanda tarihi yazo ba’a taɓa 𝐒𝐡𝐚𝐡𝐚𝐧-𝐬𝐡𝐚𝐧 mai ƙarfin iko da daularsa ta gagari duk wani jar fata nunawa yatsa ba kamarsa, ya shimfiɗa mulki a Ruman dama yankin Africa gaba ɗaya, izzarsa da ƙarfin mulkinsa yasa ba masarautun Ruman kawai ba, dukkan masarautun Africa na biye da shi da girmamawa da tsoro mai ƙarfi. Ya tara arziƙi mai ban tsoro da ban mamaki, ya kuma shimfiɗa ayyuka da ba Ruman kawai ba, Africa gaba ɗaya bazasu iya mantawa ba. Kaf ƙasashen jajayen fata masu faɗa aji na tsoro da shakkar 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐢𝐛𝐧 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐌𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝.
Sarki Haysam ya raini ɗansa ɗaya tilo tamkar sauran shuɗaɗɗun sarakuna koma fiye da su, dan saɓanin sauran yarima da tarihinsu ya shuɗe shi wannan yariman tun a shekara uku na haihuwarsa babu wanda ya sake ganinsa kojin labarin inda yake rayuwa. Sai dai a kullum akanji sunansa a bakin Tajwar Haysam fiye da sau goma, ambaton sunansa shine mafi yawan magana dake fita a bakin Tajwar. Hakan kan saka razani da tabbatuwar shi wannan yarima zai kasance na daban a dukkan sarakunan da suka shuɗe kenan. Tabbas hasashen mutanen ƙasar ruman ya rabbata, dan kuwa dai kam da gaske 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 𝐢𝐛𝐧 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐦𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝ya zama sarki na daban a cikin dubban sarakuna, tare da labari mai ban tsoro da razani fiye dana mahaifinsa. Kamar yanda ƙa’idar daular ruman take bayan cikar shekara talatin da biyar yarima Eshaan ya bayyana a ƙasar haihuwarsa ta Ruman, sai dai kamar kowane yarima na baya babu mai iya ganin fuska ko suffarsa ta ainahi, hatta da idanunsa ma shi babu wanda zai iya ganin koda ƙwayar cikinsu sakamakon glass dake sakaye da su. Bayan gama bayyanashi ga masarautu da wata ɗaya kacal Tajwar Haysam bin Abdul-Majeed yay murabus aka ɗaura yarima mai jiran gado bisa kujerar mulkin daular ruman tare da auren mata huɗu galla-galla daga mabanbanta masarautu masu ƙarfin faɗa aji a kasar ruman. Kwanan 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 bakwai akan karagar mulki Tajwar mai murabus Haysam bin Abdul-Majeed ya kwanta jiyya, jiyya ce data girgiza kowa ta kuma bada mamaki, dan kuwa kwanansa ɗaya tak yace ga garinku nan. Kwatanta tashin hankalin da ƙasar Ruman ta shigama a lokacin bazai lissafu ba. Ƙura bata lafa ba mutuwar ɗaya daga matan 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 ta sake bayyana, kwana ɗaya da mutuwarta watama ta sake mutuwa a washe gari amare suka rage saura biyu. Al’amari ya fara saka zukatan jama’a hasashen da babu damar cewa komai. Wata biyu tsakani ɗayar matar ta uku ta sake mutuwa saura ɗaya. Tofa babbar magana.