Hausa Novels and Stories

Auren Shehu Hausa Novel Page 2

Sponsored links

Baka ce, irin wannan bakin mai shek’i kamar jikin tarwaɗa. Tsayuwar hancin ta da ya zo dab da ƙaramin bakin ta ba ƙaramin ƙarawa doguwar fuskar ta kyau yayi ba……

Jin shiru ba ta ji saukar gora kan ta ba ya sanya ya ta buɗe manyan idanun ta, hakan ba ƙaramin sake rikita shi ta yi ba ganin fararen idanun ta bisa kan shi har sai da ya ɗan ja da baya ya na mai tasbihi ga ubangijin sa, domin ya tabbatar wannan halittar da ke gaban shi ba mutum ba ce.

Ta na mai duban shi cike da tsoro musammam ganin mutum mai faɗi da tsayin da tun da ta zo duniya ba ta taɓa ganin irin shi ba, daɗin daɗawa gashi yanayin shigar shiri irin na waɗannan mutanen da suka saka Nijeriya a gaba ko kuma Fulani masu garkuwa da mutane, wannan tunanin tare da jin taku da haushin karnukan da ya ƙaru, wanda hakan ya tabbatar ma ta masu gadin sun kusa shigowa lambun ya sa ta sakin niƙab din ta na mai ɗage hijabin ta yanda za ta sami damar sauri, ta yi amfani da damar gushewar tunanin mutumin da yayi kasake ya na duban ta, ta bi hanyar da zai sada ta da kitchen da sauri, hannu na rawa ta ke ƙoƙarin fidda ɗan mukulli da ta ɓoye cikin dan wando da ke sanye jikin ta

Har tuntuɓe ta ke garin waige domin tabbatarwa ba ya biye da ita.

Allah ya taimake ta ƙofar ya buɗu, kasancewar ta sababbiya a harkar, cikin sanɗa da lalube ta ke tafiya domin wutan lantarkin kitchen din a kashe ya ke, sai dai hasken farin wata da yake ratsowa ta taga. Ba ta tsorata ba sai da ta jiyo muryar masu gadi daga cikin garden, ta na mai roƙon Allah ya sa ba asirin ta ba ne ke shirin tonuwa ba, ta bi ta falo ta shige ɗakin ta cikin rawar jiki. Dan tun da take fitar dare ba ta taɓa shiga tsaka mai wuya kamar na yau ba.

Hijabin jikin ta ta cire, ta na mai ajiyar zuciya ta zube bisa gadon ta.

Hasken da ya gauraye ɗakin sanadiyyar wutan lantarkin da aka kunna ya sanya ta yi zumbur ta tashi zaune a tsoro ce. Ganin wacce ke jingine jikin bango ya sanya ta fiddo ido tare da faɗin

“Wai ke Halitta ba za ki fita harka ta ba? Wannan masifar har ina haka?”

A hankali Halitta ke ƙare ma ta kallo, tun daga dan ƙaramin matsattsan wandan da ke jikin ta (bumshort) zuwa matsatsiyar jar riga wacce ta tsaya ma ta iya cibiya, ga kan nan ya sha kitson attachment da aka yi da gashin doki mai tsada da ake kira (Brazilian hair). Ta na mai girgiza kai ta furta

“please Halitta, ba yanzu ba, na gaji da yawa!!”

Ta katse ta tana ɗaga mata hannu. Ganin an murɗa ƙofar ɗakin ya sanya ta saurin janyo bargo domin ɓoye shigar da ke jikin ta. Mahaifiyar su wacce su ke kira Ammy ce ta shigo, ta na hamma tsabagen baccin da ke idanun ta, ta ke duban su cike da damuwa ta ce

” dama na san dole kuma kun tashi, hayaniyar su Audu da haushin karnuku ne ya tada ku ko?”

“eh wallahi Ammy…..”

Su ka faɗa a tare wanda hakan ya sanya Halitta sakin baki cike da mamaki ta ke kallan yayar ta ta, ita kuwa ko aji kin ta ta ce

“na kasa gane menene matsalar su da za su na sakar mana karnuka su na mana hayaniya, ya kamata a hana su shiga garden ma kawai….”

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button