Fulani Page 11 Hausa Novel
Haka ta zauna a gurin tana kula da shanun har rana ta raba sannan ta nufi sandarta ta dauka ta kora shanun suka nufi hanyar gida tana tafi tana rare wakarsu ta fulani kamar ba ita ce ta gama kuka dazun ba.
Ita ta kanta ta saka shanun a gurin zamansu sannan ta daure ko wanne ta dauki abun shan ruwansu ta debo musu ruwa ta kawo musu sannan ta fita daga wajen.
Bukkarsu ta nufa ta shiga ciki tana cigaba da rera wakar da take tun da ta turo shanun har ta kawo gida, tufafin Fulanin dake jikinta ta cire ta daura zane ta fito tsakar gidan ta dauki wata karamar roba ta nufi tukuyar ruwansu ta debo ruwa a ciki ta nufi bandaki, sai da ta tube tufafinta sannan ta lura da kadangaran dake leke da windin da aka zagaye akai bandaki da shi suna a kai suna kallonta, bayan mutane abu na biyu data tsana yana kallonta kadangaru ne, dan ta lura har wani kada kai suke idan suna kallonta, abun haushi ma kallonta suke ba kakkautawa ko dauke ido basa yi.
Haka ta debi ruwan ta rika watsa musu suka fara gudu banda daya wanda ya tsaya yana kallonta sai wani rausayarda kai yake.
Hakan yasa ta tsorata ta fara ja da baya tana cigaba da watsa masa ruwa, aiko kamar jira yake sai ya sauko da sauri yai cikinta, tsakanin ihunta da fallawa da gudu da kuma sakin robar ruwan ba a san wanda ya riga wani ba, kamar bera haka ta shige bukkarsu har wani tsale take sama tsabar gudu da tsoro.
“Inna Kadangare ne ya bijoni”
“Ba dai zaki daina watsa musu ruwa ba ko? Wata rana sai kin watsawa aljani”
“Inna wannan ma da gudu yake, ba zan iya wanka a ciki ba”
Duk maganar da take da Inna ba ta dago ta kalleta ba sai aikin auna giɗa take a kwarya, sai da ta mike tsaye sannan tai arba da yarta.
“Innalillahi Fulani a tsirara kike fa, zindir Subhanallahi”
“To Inna kadangaren ne ya biyo ni ai ba zan iya tsayawa daura zane ba”
Ta fada tana turo baki tare da sa hannu ta kare kirjinta wanda da shi da babu duk daya kamin ta nufi inda zane yake ta dauka ta daura. Sai da ta ga mahaifiyarta ta fito sannan ita ma ta fito waje tana labe bayanta kamar wacce zata sake arba da shi.
“Ni ban ga komai a bandakin ba”
“To Inna ki tsaya na gama wanka tukuna sai ki tafi”
A bakin kofar bandakin Inna ta tsaya Fadime ta dauki robar taje ta debo wani ruwan ta tsaya daga baki-baki tai wankan ta fito da sauri…
FALMATA POV.
Bayan gama sallah isha’i Baba ya shigo gidan rike da yar ledarsa, da sauri ta karasa ta karba tana masa sannu da zuwa, ya amsa mata can ciki yana dauke fuska kamar wanda baya kaunar ganinta.
Dakin Tumba ya nufa tana biye da shi a baya rike da ledar sai da ya shiga sannan ita ma tai sallama ta shiga ta aje ledar ta juyo ta fito kamshin tsire na dukan hancinta, guri ta samu a saman tabarmar dake shimfide tsakar gidan ta zauna tana ta bitar karatunta na iziya. Hango mahaifinta ya fito daga dakin Tumba zai kama ruwa yasa tai sauri tashi ta karasa ta dauki butarsa ta zuba masa ruwa ta mika masa tana sirinawa kamar yadda ta saba.
Sai da ya shige bandakin sannan Tumba ta fito ta rike kofar dakinta tai tsaye tana watsa mata harara.
“Fulani dauki bokiti kije ke samo mana ruwa”
Juyowa Falmata tai ta kalleta da fuskar tausayi tana jin kamar tace ta dauki bokiti taje ta debo wuta, har ga Allah bayan surfe deban ruwa ne abu na biyu data tsana, sai dai babu yadda za tai kullum sai ta yi surfen sai kuma ta yi deban ruwan abu ne da ya zame mata dole ko a ciwo ko da lafiya dole ne tai.
“Umma na debo ruwa dazun da safe fa sai da na cika komai”
Ta fada da muryar dake nuna rokon take a tausaya mata.
“Ba gabanki Naja tai wanki ba? Ruwan ya kare ko so kike mu tashi da safe babu ko na alwala?”
Umma na kai aya Abba ya dauka yana daka mata tsawa.
“Dauki kije debo ruwa aka ce sha-sha -sha kawai”
Ya karasa yana daure zariyar wandonsa karen sigari a bakinsa. Kamar wacce tai arba da mutuwarta haka ta nufi inda bokin ruwan yake ta dauka da sauri jikinta har rawa yake ta shiga dakin da suke kwana ita da naja ta dauko hijabinta ta saka ta dauki bokintin ta fice daga gidan tana ala ala kar ma tai numfashi da karfi mahaifinta ya ji.