Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 39

Sponsored links

Jikinsa rawa ya neman farayi saboda yanda ta ƙanƙamesa, tunda yake a rayuwarsa bayajin ya taɓa rungumar mace kamar haka. Gaba ɗaya abinda ya ɗauka tsahon shekaru yana dakon dannewa ya nema yunƙurowa. Ƙoƙarin janyeta yake tana sake ƙadandanesa a tunaninta so yake ya cire matan koda tsiya. (Ya arrahaman zata halakani) ya faɗa a zuciya yana mai rumtse idanunsa da masifar ƙarfi a zahiri. Cikin zafin nama ya finciketa da sauri yana ƙoƙarin riƙe rawar da jikin nasa ya fara. Cikin wata ƴar sassarfar da bata hana takunsa na ƙasaita fita a yanda yake ba ya bar wajen, a kujerar da ya tashi ya koma ya zube. Faɗi yake (shike nan ta buɗe aiki, Fitinanniyar yarinya zata halakani).

 

Oho Fareedatu batama san yanai ba, dan tana samu ya jayetan daga jikinsa ta kwasa da gudu sai saman katafaren gadon da aka gyara tsaf kamar ba yanzu ta sauka akansa ba. Bata da nutsuwar tunanin yanda akai aka gyara ɗin ko wanda ya gyara taja lafiyayyen duvet ɗin ta naɗe jikinta dake faman kakkarwa. Dan jinta take kamar wadda ta jonu da lantarki. Shiru ɗakin kowa yay ɗif a cikinsu. Babu ko motsin ac dan bai kunna ba saboda ita, duk da yana buƙatarsa, sai dai ya kashe na’urar ɗúmama ɗakin dake aiki tun ɗazun saboda itan. Sai da ya ɗan saita kansa kaɗan kafin ya miƙe, batare da ya dubeta ba ya nufi hanyar fita. Ƙasa-ƙasa ta bishi da kallo, ganin ya tsaya tai saurin kauda kanta. Bai juyo ba sai dai yaji a jikinsa ana kallonsa, murya a shaƙe can ƙasan maƙoshi ya motsa lips ɗinsa kaɗan. “Ki canja wannan rigan”.

 

Jitai kamar ana narkama jikinta ƙanƙara, ta wani lumshe idanunta dake faman yin mar-mar, sai kuma ta sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya dai-dai da rufe ƙofar da yay bayan ya fice. Jitai gaba ɗaya kanta yama tushe, ta gagara tunanin komai kamar yanda take buƙata, kamar wadda aka zabura ta miƙe, idanunta ne suka sauka kan wata ƙyaƙyƙyawar abaya mai ɗaukar idanu. Karasawa tai ta daga rigar, sai kuma ta ɗan waro idanu ganin b&p a ƙasa, “Kam babbar buta, duk shi ya ajiye wannan ma? OMG! Wannan Shahan-shan ɗin daular ruman ɗin ko”. Ta ƙare faɗa kamar zata fashe da kuka. Dan ji take duk ta daburce tsabar wata kunya da take ji na ratsata tamkar tana a gabansa……..

(Itace muke buƙata ta zama uwar Miran mai jiran gado, ki gaggauta, ki gaggauta tabbatar da ita cikin masarautar nan matsayin Zawjata-almilk daga nan zuwa mako huɗu. Inba haka ba kiyi kuka da kanki ta-ƙurya hahaha!!! hahaha! hhhhh!!!!)_

Zumbur ta miƙe daga ɗan barcin daya figeta, firgitattun kalaman uwa da tayi mata su a zahiri ne waccan ranar ke maimaita kansu yanzu a barcinta matsayin mafarki. Hannu takai ta yarce uban gumin da ya jiƙe mata goshi har yana zirarowa akan fuskarta. Tana a tsaka mai wuya, irin tsakan da bata taɓa shigaba a duk umarnin da uwa ta bata a baya. Maganar ƙulla auren nan bazai kasance ƙarami ba gareta a wannan karon, sakamakon zaman babu wanda ya yarda da ɗan uwansa da akeyi yanzu a masarautar ta ruman. Gaba ɗaya ta rasa ta inda zata ɓullowa al’amarin nan. Ji take komai ya sukurkurce mata, sai dai kuma bazata iya yarda da barin cikar burinta ba na tsawon shekaru da take ganin tazo gab da cimmawa. Dolene ma tai wani abu, sai dai salon zai banbanta dana baya koda kaɗanne, zatai irin ɓadda kamar data saba wajen ganin wannan auren ya ɗauru, dan ko zatai yawo tsirara bazata taɓa yarda Iffah ta zama Malikat ba, mai haihuwar magajin Shahan-shan never for ever hakan ta faru tana numfashi a doron duniya….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button