Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 18

Sponsored links

Malikat Bushirat duk da labarin farkawar Iffah ya zo har kunenta ta hanyar doctor Afif batace komai ba hakama bata leƙa dubata ba, sai ma yazam a safiyar ranar har zuwa yamma bata leƙa sashen Tajwar Eshaan ɗin ba gaba ɗaya, ta dai kira waya domin jin cigaban lafiyar jikinsa. Shi ɗin ma dai bai shiga duba Iffahn ba sai yamma duk da kuwa jiyan ma a gaban idonsa ta farfaɗo, Sannan har yanzu jikinsa babu ƙarfi shima, dan da gaske gubar da suka haɗa da dafin macizan ta so masa illa ƙwarai da gaske tunda gashi ma har sai da akai masa aiki dalilin taɓa wani sashe na jikinsa data so tayi saboda ƙarfinta.

 

Duk da ɗakunan jiyyar tasu na maƙwaftaka da juna a yau bamai iya ganin wani sakamako labulolin da aka zuge suka toshe gilashin da ya raba sun, koda babu labulen gilashin mai ƙarfine da babu mai jin maganar wani koda za’ayi da ƙarfi ne, sai dai zaka iya hango mutum fes. Har zuwa yanzu dai kayan jiyya ne a jikinsa sai dai a kullum yakan canja da wasu sabbi sau fiye da biyu, ya ɗan rame saboda yanda ciwon ya bugesa. Sai hakan ya sake fiddo hasken fatarsa mai launin tar-tar a cikin idanun mai kallo. Cikin jarumtarsa da ƙarfin hali yake tafe doctor Afif biye da shi a baya tare da Sayeed Fayzul-haq dake tsaye da ga bakin ƙofa dan zuwansa kenan. Cikin sauri Sayeed ya danna maɓallin ƙofar gilashin ta zuge kanta a hankali. Baya ya ɗan ja yana mai rissinar da kansa ga shugaban nasa mai matsayin gaske a garesa da bazaya iya musaltuwa ba. Izzarsa da ƙasaita na tattare da shi, dan tamkar itace jinin dake zagayawa a maimakon jininsa, ya ɗan ja iska ya fesar na wasu sakkani kafin ya cigaba da takawa a sannu ya shiga bakinsa ɗauke da sallama can ƙasan maƙoshi. ..

Daneen Ammarah da ke zaune a gefenta tana ƙoƙarin bata shayi mai zafin gaske da Doctor ya bada umarnin bata ce ta ɗan waigo najin motsi, numfashi ta ɗan ja ƙaɗan tana mai sauke idanunta a kansa. Sai kuma ta miƙe dai-dai Iffah tana damƙe kofin shayin cikin hannunta duk da zafinsa da takeji sakamakon jin Daneen Ammarah ta ambaci “Abni”. Sosai zuciyarta ke harbawa da ƙarfin gaske, kusan tare da ɗaga sawunsa da saukewa cike da izzar da raunin ciwo bai rageta a gareshi ba sam. A tsumen da fuskarsa take ya tabbatar ma Daneen Ammarah a Shahan-shan ɗin sa ya shigo ba ɗanta ba, dan haka ta ɗan ja gefe a yanayin girmama darajar da ALLAH ya basa. Cikin sauri Sayeed Fayzul-haq ya gyara masa kujera yana mai ja baya kusa da Doctor ya rissinar da kansa. Duk abin nan dake faruwa yana tsaye kaifafan idanunsa masu matuƙar tasiri da tabbatar da girman da ALLAH ya bashi na mulki badan yafi saura ba na a kanta, kallo yake mata irin na ƙasan ido mai hana wanda akema sukuni koda bai san wanda ke masa ba. Sai da ya gaji dan kansa sannan ya kai zaune sannu a hankali ga kujerar da aka gyara masan…

Iffah ta kasa sake iya motsi duk da azabar zafin shayin da raɗaɗin da ke ratsa mata hannu, sauƙinta ma ta ɗora shi ne bisa lallausan duvet ɗin da ƙafafunta ke ciki har zuwa cinyarta. So take kawai taji ta ɓata, ɓata irin wanda ta daɗe tana jin labarin masu layar zana nayi, ta kasa tantance ainahin abinda ke razanar da kasancewar sa gareta, shin tsoro ne ko matsananciyar kunyar kai ne?. Inama inama, inama daga halin data tsinci kanta bata sake farkawa ba balle su haɗu, inama an cigaba da barinta ta dawwama a kurkukun da bazata sake ganinsa ya ganta ba har abada. Tabbas har yanzu tana jin zafi, zafi mai haɗe da raɗaɗin rasa ƴan uwanta guda biyu, sai dai saɓanin yanda ta ɗauka abun a da akwai banbanci da yanda take kallonsa a yanzu…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button