Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 123

Sponsored links

Cak ya tsaya daga abinda ya keyi, duk da bai juyo gaba ɗayansa yana kallonta ba, hankalinsa kaf ya koma gareta. Kusan a tare zuciyarsa da jininsa ke tsitstsinkewa. Bashi da bukatar shan madara a wannan gaɓar dan a nasa tsarin da rana ko dare kawai yake shan madara. Sauran lokuta shayi ne mafi rinjaye da ruwa. Amma a yanzu duk da bahagon yanayin da yake jin jikinsa, da wanda yaga yarinyar a ciki sai ya kasa nuna bazai sha ba, tamkar shima ana ingizashi da remote ɗinne ya kai tattausan hannunsa saman nata a karo na biyu. Zabura tayi kamar wadda ke son dawowa hayyacinta sai kuma ta koma laƙwas tare da buɗe idanunta da sukai jazur ta sauke a kansa. Kallon cikin ido sukai ma juna na kusan tsahon minti ɗaya cirr batare da ɗaya su ya motsa ba abinda bai taɓa faruwa da su ba. Shi ya fara janye nasa a kasalance tare da hanunsa da ya zaro kofin daga cikin nata…

A yanzun ma firgigit tayi tamkar wadda ta farka a barci harda ɗan zabura ta kai hannu kamar zata riƙo kofin sai dai abin mamaki shi har ya kaisa kan baki

Dire kofin da ke empty a hanun Tajwar Eshaan dai-dai da komawar Iffah daɓas zaune ƙasan lallausan kafet ɗin kamar wadda aka zarema dukkan numfashi. Ta

 

matse jikinta tana mai ƙoƙarin riƙe tsumar da takeyi tare da miƙewa zumut. Ya kafeta da ido lips ɗinsa na ɗan motsawa alamar son cewa wani abu amma jin kai da ƙasaita ya hanashi yin hakan. Sai kawai yay ƙoƙarin janyewa cike da basarwa amma hakan ya gagara. Shi kansa bai san yaya akai ba, bai san tayaya ba kawai ya samu kansa ne da riƙo hannunta. A tare suka rumtse ido bisa mabanbanta dalilai. Karan farko na fara tasirin dafin macizan da suka gama gauraye jininsa ya matsota a hankali garesa. Babu zato Iffah tajita saman jikinsa da ke fitar da wani irin sirrintaccen ƙamshi mai karya zuciya. Numfashinta ne ya fisga da ƙarfi kamar mai cutar Asthma, ta buɗe ido da sauri dan gaba ɗaya hankalinta ya dawo jikinta. Zumbur ta mike jikinta na wani irin kaɗawa ta fara jan ƙafafunta da baya-baya siraran hawaye da batasan na minene ba na rige-rigen sakkowa. Cikin son danne tashin hankalin dake cigaba da gauraye jijiyoyi da tsokar jikinsa ya ɗago idanunsa da launinsu har ya fara canjawa ya zuba mata, gab taci tuntuɓe da centre table, kaifin idanunsa da tasirin su gareta a wannan gaɓar ya sata zubewa gaba ɗayanta akan tebirin…

 

Wata irin zufa ce ta fara keto masa a dukkan ƙofifin gashinsa, yayinda tun yana iya ganin Iffah a kusa da shi har ta fara masa nisa. (Tabbas a kwai matsala) ya ayyana a zuciyarsa yana mikewa da ƙyar. Da kallo ta bishi zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu tamkar zata buntsiro ta bakinta. Ganin ya shige ta miƙe itama cikin sassarfa, harta nufi ƙofa ta dakata, tamkar an janyo idanunta suka sauka kan computer ɗinsa, janyewa tai dan burinta tabar sashen kawai amma sai zuciyarta ta dinga ingizata ga computer ɗin. Bayanta ta ɗan waw-wai-gawa irin dai na rashin gaskiya kafin ta koma da baya ta zauna a kujerar tasa ta dasama rubutun fuskar computer ɗin ido. A karan farko ƙirjinta yay wani irin masifar motsawa. Tsabar kaɗuwa batama san takai hannu ga computer ɗin ba har rawar jikinta na bayyana. Babu tantama saƙon data turama Ajmaal ne na karshe, kaɗan ya rage zuciyar Iffah ta ɓaro waje a wannan gaɓar, babu shiri ta fara sama dukkan saƙonin data tura masa ne babu ko ɗaya daya goge, kowanne kuma babu canji a date ɗin data tura ne. Ai babu shiri ta fito ta shiga settings ɗinsa na WhatsApp. A Profile ɗinsa, dp pic.. ɗinsa, da komai na dai Ajmaal ɗin data sani ne… “Allahumma ajirni fi musibati wa’akhlifni khairin minha”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button