Bakon Lamari 23
Ya Ɗauki plate da Spoon ya aje a gaban shi sannan ya ɗauki Sarving Spoon ya Buɗe Flask ɗin Dambun shinkafar daya ji gyaɗa da Zogale da Albasa da wadataccen Man gyaɗa da ƙananun Hantar da aka yanka aciki ya matsar da Plate ɗin gaban flask ɗin ya saka sarving spoon yana ɗiba wani haɗaɗɗan ƙamshin Dambun na dukan Hancin sa.
Ɗan kaɗan ya zuba sabida bai da yawan cin abinci sannan ya rufe flask ɗin, ya janyo na farfesun Ƙoda da hanta da Tumbin da akai wanda Aka yanka manyan albasa acikin sa shima sai ƙamshi yake ya zuba wadatacce a saman Dambun sabida Yana da son Naman kayan ciki A rayuwar sa.
Bisimillah yayi ya ɗauki spoon ya soma Juyawa yana ɗiba Haɗe da farfesun yana kaiwa Cikin Bakin sa Daɗi Mai ma’ana yana kaiwa ƙwaƙwalwar sa Ziyara A ranshi yana addu’ar Allah yasa Zainab Ta iya Girki Domin mace wadda tasan kan ludayi itace Mace Duk macen da bata iya Girki ba sunanta Sorry Bini Bini daya ci loma ɗaya zai ɗauki Cup ya tsiyayi ruwa a Roba ya kai bakin sa har ya kammala Cin Abincin yayi Hamdala Ga Allah tare da Ɗaukar tissue ya goge bakin sa Lokacin daya tashi daga saman dinnig Ɗin wayar zainab kusan ta Biyar na shigowa bai ɗauka bane sabida ƙa’idarshi idan yana cin Abinci Baya magana har sai ya gama Kuma Bashi kaɗai ba wannan tarbiyar Duk wani Ɗan gidan Mama ne.
Bin kiran nata yayi Lokacin daya ƙarasa Saman one seater dake Falon Mama ya zauna ya ɗaura Ƙafa ɗaya kan ɗaya yana girgizawa.
“Baby ina ta kiran ka baka ɗauka ba wai baka tawo bane ba?”
Ya shafo gemun shi tare da cewa.
“Zainab sau nawa ina gaya Miki Ni musulmi ne ki soma yi min sallama kafin ki fara Min magana”
Ya faɗa Muryar shi a dake.
“Kai haƙuri Ina ɗaukin Ganin kane Tun ɗazu nasa masu aiki suka maka girki Ni kuma naje Gidan Kwalliya yanzu Haka kai nake Jira kai Min waya nazo airport Ɗin”
Tausayin tane ya tsirga masa har Ranshi Zainab na son shi Haka Shima yana son mace mai Son shi wadda zata Nuna masa tattali da kulawa.
“Ina gida yan zu haka nagama cin Girkin Mama na”
Ya faɗa a dake.
“What!! Girkin wa? banji me kace ba haba Ahmad kana Nufin duk wahalar dana sha Na kwalliya da sakawa ai maka Girki ya tashi a banza kenan?”
Ta ƙarasa maganar tana Kuka!
“To ya za’ai kinsan Ni ba korarre Bane Ina da gidan mahaifa Kano ai gida ce Ki min uziri yau na gaji Amman Gobe zan Zo”
Ya faɗa Cikin kwantar da Murya.
Kuka kawai zainab take masa na takaici da Baƙin cikin abin da yayi mata.
Gajiya yayi da Jin kukan nata dan shi bai iya rarrashin mace ba sabida haka sai ya kashe wayar tashi Baki ɗaya.
Ya kwantar da kanshi Jikin seater Yana mai rufe Idanunshi.
“Har ka gama cin abincin?”
Yaji Muryar mama wadda take zama a kujerar dake kallon shi.
Da sauri ya zame daga saman Kujerar ya zauna a ƙasa.
“Na gama mama Amman ina son Baƙin shayi asa Kamal ya miƙa Min ɗaki”
Ta Jinjina kai tana cewa.
“Daman na dafa maka mai kayan ƙamshi sai ya miƙa maka idan ya shigo”
“Nagode Mama”
Ta kuma fuskantar sa taga yadda ya nutsu a gabanta yay ƙasa da kanshi sosai.
“Amatu tana gida fa Auren ta ya Mutu, wannan abu da shi na kwana na tashi dashi da Alhaji ya gayan Jiya duka yaushe akai auren nata amman yaron nan ya sake ta ga jaririya ina ga basu yi arba’in ba! sannan Ina son kaje kaga Jikin Babanka sha’aibu yakamata ai wani abu akan wannan Jiki nasa sannan Kuma ka ƙaro Kayan abinci Wa matan kawun ka da sauran matan gidan sai Kuma Kuɗin makarantar Yaran kawunka suma naji ance an koro su Jiya”
Dama a ƙa’ida idan sukai waya da mama tana gaya masa dukkan buƙatun Gidan da kuma abin da ya faru sabida shine Babba a kaf ƴaƴan gidan, Gudun kada a ce bata gaya masa Komai. To yau kuma ganin Allah ya kawo shi yasa take gaya masa waɗancan maganganu waɗan da dama tace zata bari In yazo ta gaya masa tun sanda yace mata zaizo.
“Sannan ina son Hafsa ta dawo gida ta haihu kaga haihuwar fari ce”
Ta kuma faɗin hakan duk da yayi shuru ya ƙi cewa komai.
“A,a mama ki barta a gidan ta kawai In yaso a ɗauki mai aiki ta kula da ita”
Ya faɗa batare daya ɗago ya kalleta ba.
“To shike nan hakan za’ayi”