Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 9

Sponsored links

Sumayyah tsananin tsoro da tashin hankalin yanda mutumin yake tinkararta kai tsaye lokuta da dama idan suka hadu a hanya yasa ciwon damuwa da tsoro mai tsanani suka

shigeta,

Ta fadawa Benazir ma ta kasa, tsoro da fargaba takeji dan haka daga karshe saita dena fitowa kwata kwata daga hall din lecture dinta idan tashiga,

Wannan matakin data dauka yasa ta dauki lokaci mai tsayi bata sake haduwa dashi ba har tafara mantawa da lamarinsa gabaki daya ta koma tana fitowa kaman yanda ta saba.

Ta nasa bangaren Bilal kaante kasa mantawa yayi da ita musamman yanzu sbd ita din yake dan shigowa gurin prof duk da prof dinne ya kamata ya ringa zuwa yana samunsa sbd matsayi da karfin power tareda tarin Asalin dukiyar dasuke dashi Kaante Family harma da suna.

Rashin ganinta kwana biyu ya fahimci da kanta take boye kanta din sbd shi dan haka shima sai bai takurata ba a boye yafara bibiyarta yayi bincike akanta ya fahimci Mahaifinsu mai tsanani da zafin gaske ne hakama yanada tsaurin hukunci amma sam bai samu sanin irin halin da rayuwarsu take ciki ba a karkashin mahaifin nasu sbd wata rayuwa ce da babu wanda yasan asalin balai da ukubar dasuke ciki iya tsananinsa kawai aka sani sai Aikin wahalar dasuke yi musamman na wankin qattin mazan dasuke masa na shagon shagon wankin daya bude babba.

A qanqanin lokaci da gajeran bincikensa ya dan fahimci rayuwar tsanani suke ciki sbd ko a yanayin rayuwarsu zaka iya fahimtar basa rayuwar ‘yanci da sakewa sai yanda akai da rayuwarsu.

 

Ajiyar zuciya ya sauke bayan kwanaki yana yawo da tinanin rayuwarsu yana bibiyarta daga dai ya tabbatarda tausayinta ne tareda soyayyarta suke shigesa abinda bai taba faruwa dashiba soyayyar wata mace bayan ta mahaifiyarsu da qanwarsu qwalli daya dasuke uwa daya wadda itama DD ne ya saka masa kaunarta mai tsanani sbd yanda duk tsananin zafinsa daga Mammah sai Zeenah din yake ragawa a duniyarsa da babu kowa acikinta bayan kebe kansa daga yan uwa da familyn nasa.

Bilal Sumayyah ta shiga zuciyarsa cikin sanyi da nutsuwa,

Yanajin sonta na qarfafa zuciyarsa saidai kuma damuwarsa ta yanda bazata samu karbuwa a familynsa Ba dan fitowarta daga ahalin da ba kowa ba kuma basuda abinda shi a nasa familyn ake kira Girma maana kalman nan ta kwarya tabi kwarya,

KAANTE family wani babba,sananne,attajiran family ne da ake kiransu da billionaires wasu kuma su ce musu the family of power.

KAANTE’s Sun kasance wasu irin sananni dasu hada,fame,wealth,power harma da lokaci da Allah ya basu sam an kasa samun wanda ya wucesu ko ya fisu,

Idan akwai wanda zai iya tsayawa gaban KAANTEs din ya nuna musu isarsa da zafin kai a duniyarsu to DD KAANTE wato DAWOOD DAUDA KAANTE,wanda yake ‘da kuma guguwar da ita kadai take girgiza familyn batareda sun iya yin komai ba akai haka shine kadai yake tsayawa gaban duk wanda zai kawowa familyn Hayaqi

Tayaya zai iya gabatar da Sumayyah ga familynsa a matsayin wadda yake so da kaunar mallaka.

Kusan shine babba a familyn dan haka sunada high hopes akansa na auro macen data dace da matsayinsu,

‘Yar babban gida,wayayya ‘yar boko mai zurfi ilimi da class kaman yanda duka sauran mazan familyn suke auro matayensu.

Tayaya zai fara dan shi dai zuciyarsa tayi naam da sumayyah bayajin zai ja da baya saidai kuma fargabarsa bata gushe ba saima qaruwa datake yi.

*******Sumayyah data manta dashi sukaci gaba da rayuwarsu kaman mujiya acikin mutane suna sake maida hankali ga karatunsu ahankali ciwonta yafara dawowa sosai kaman qwaqwalwanta zai juye gabaki daya sbd yawon makarantarsu yanda yake cin kudin Ababa yasa Ababan ya tsananta musu azabarsu da wahalarsu sun koma yanzu so daya ake basu abinci hakama aikin wankin shagonsa harma da guga yanzu

Basa samun lokacin karatu ko kadan sai ya zama makarantar ma idan sunje yanzu kusan daqyar Benazir ke ganewa Sumayyah kuwa sam ta dena ganewa wasu lokutan ma magana takeyi ita daya ana lectures sai hakan yasa mutane suka fara ankara da kaman tana matsalar juyewar kai,

Tin maganar na yawo iya tsakanin course mate dinta sai maganar ta fara yaduwa har gurin da baa zato

Sai abin yafara zama kaman ana tsokanarta ana nunata akan tanada juyewar kai.

Tin tana daurewa tana nesanta kanta da mutane sosai har abin yafara yawa ko inda mutane suke bata iya zuwa sbd yanda ake mata kaman mai ciwon hauka sosai.

Tayi kuka,tayi kuka,tayi kuka amma babu wani sauki ko sassauci,

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button