Zafin Kai 11
Na yau basu ci ba sbd yanada qamshi zaa iya jinsu dan haka suka boye cikin kayansu sai tsakar dare suka tashi yunwa na neman kashesu suka hau ci kaman wainda sukai shekaru ba abinci.
Suna gama ci ko ruwa kasa fitowa su sha sikai sbd fargaba dan haka a hakan suka kwana yauma ledojin a cikin jikinsu suka kwana dasu.
Anne da sukaiwa bayanin Abinda yake faruwa tsorone yafara shigarta sbd ranar ra zaa ganesu take tsoro dan kuwa ranar ruwan masifar fa zaayi a gidan hakama shi kansa mutumin dake taimaka musun Ababan ba barinsa zaiyiba da balainsa dan haka ta ringa musu nasiha da gargadin su kiyaye su nesanta kansu da abinda zai qarasa kashe musu dan kwanciyar hankalin dasuke samu wasu lokutan idan masifar Ababa da hande ta kwanta.
Tamkar wanda aka wajabtawa haka Alh bilal kaman yanda su suke fada yafara sauya rayuwarsu daga wahalalliyar azababbiyar yunwa,
Kullum sai ankawo musu abinci a boye suke karba suna isa dashi gidan sunaci su da mahaifiyarsu wadda a yanxu ciwon yunwar daya gama cinye hanjinta yafara dan sakewa sbd a baya haka take kullum a mokade kaman ledar da aka jefa cikin tafasasshen ruwa.
Aduk sanda suke shigowa da cin abincin cikin masifaffen tashin hankali da firgici mai tsanani sike cinsa su gama dan kuwa sun sani na lahira sai yafisu jin dadi duk randa mummunan tsautsayi yasa kaddarar tonan asiri ya kamasu.
Shi kansa Alh bilal din daya sake fahimtar yanayin da suke ciki na ba qaramin taimakawa abincin ke musu ba daya fara fahimtar yunwar dake tareda sumayyah tafara sakinta kaman yanda likitan dake dubata yafada sai ya dage da ciyar dasu din a boye ta yanda shima nasa familyn basu san rayuwar daya jefa kansa ba.
A yanzu da ya zama kaman biyayyarsa shima kusan tilas ce garesu sbd kyautatawarsa garesu sai ya zama wani irin girma da darajarsa suke gani gashi shima din sai ya dena tinkararsu kai tsaye cikin mutane sbd fahimtar suka tsananin shiga firgici da tashin hankali idan yayi hakan dan haka haduwarsu sai ya zama a sirrance sukeyi.
Hawa Mashin din zuwansu makaranta daya tsana fiyeda komai sai ya siya musu napep kai tsaye sbd kaisu kawai da daukosu tinda basa son shiga motarsa koyaushe suka shiga cikin yanayi na mummuna suke dan haka wanda ya bawa napep din aikinsa kawai kaisu da dauko su.
Da farko tsoron hakan sukeji sosai sbd basu san yanda zasiyi da kudin mashin din da ake basu ba,
Basu iya boye kudi ba sbd ko sun boye basu san me zasiyi dashi ba tinda basu taba sakawa ransu tinanin guduwa subar gida ba bare su ringa boye kudin gashi idanma sun gwada boyewan tinda suka fara zuwa makaranta akai akai Ababa ke sawa hande tana bincikesu da kayansu dan haka basu taba tinanin boye wani abin ba ko ba kudi ba
Abincinmq dasuke shigowa dashi dan suna cinyewa ne a take dasun shigo dashi, dan haka kaman yanda Allah ya kawo musu mai taimakonsu a boye sai suma sike bawa wani tsoho makaho kudin a hanyarsu ta tafiya kullum sbd baida kowa shima yana cikin mawuyacin hali.
Tsohon daya gama wanyewa dasu kullum shima a duk lokacinda ya bude bakinsa Benazir yakewa addua sbd itace mai fitowa ta basa,
Adduarsa kullum Allah yakaita matsayinda bata taba tinanin zuwaba tareda rayuwa mai Albarka da kwanciyar hankali tareda zuria dayyaba.