Hausa Novels and Stories

Hariji Hausa Novel Complete Book 1

Sponsored links

_The Agony of destiny🥲_

 

 

 

Tsugune take qarqashin murhun duwatsun dake tsakiyar gurgurarren gidan Jan lakan tana hura wutan da bakinta cikeda qosawa

 

Shikam wutar banda bulbulo da wani irin hayaqi me toshe qofofin shaqar iska ,dasa idanu tsiyayar qwalla na zallar iccen damuna ba abunda yikeyi

 

 

 

Rumtse idonta tayi ta bude saboda sarewa da tayi wutar baida alamun kamawa، tsabagen wahalallen sullutayen iccen dake jikin murhun da suka jiqe jagwab ba alamun zasu ruru

 

 

 

 

 

Miqewa tayi tana gyara daurin dankwalinta sannan ta kama ha6ar zaninta ta sharce hancinta

 

Idonta ya kada yayi jaxur

Dakko wayarta tayi rakani toilet tana duba lokaci

 

Takwas ya gota Na safiya

 

 

 

 

 

Cikin sharar qwalla ta d’auki buta ta wuce Bayan d’akunan gidan ta wanko jikinta ,dukda hururuwan sanyi da akeyi hakanan take kwara ruwan mai kama da qanqara

 

 

 

Cikin gaggawa ta shafa Vaseline er had’in gida

 

 

 

Ta dakko uniform masu ruwan ganye ta saka ta saka qaramin farin hijabi ta d’aura wani tsohuwar abaya baqa ta saka baqar takalmi mai rufi

 

 

 

Sannan ta dage tattararren labulen d’akin

 

 

 

“Na wuce ummah”

 

 

 

“Au tafiya xa kiyi ummy bazaki tsaya ki karyanba”

 

Muryarta rawa ya kama yi alamun za tayi kuka

“Ummah zan makara kuma wutan yaqi kamawa tun shida da rabi ga yanzu takwas da rabi’

 

 

 

 

 

To ai Cikin ki qaryan kafiya kikeyi ,acedai ga en uwanki sun dawo da banqararrun kaji yaji yajin cittah ke kice dole bazaki ci abunsu ba baki horu bane”

 

 

 

 

 

Shiru tayi mata haka tayi mata sallama ta gangara general hospital dinda take aikin voluntary a qasa in wata yayi maaikatan suna dan sammata wani Abu

 

 

 

Sashen d’akin haihuwa ta nufa da gaggawa ta shige ba tareda ta tsaya a wajen nurses station dinba bare metron din ta ganta tayi mata fad’an makara

 

 

 

 

 

D’akin da suke ajiye kayansu ta shiga ta cire jallabiyar da takalmin ta ta zura wani soson takalmi da ake masa laqabi da shaku shaku

 

 

 

Sannan ta shige d’akin kar6an haihuwa

 

 

 

“Yawwa TBA(traditional birth attendance) zo ki gwada mana VE (vaginal examination) din matar nan”

 

 

 

Wata nurse tabawa ummy umurni,tana nuna mata wata hajiya da zatakai shekaru talatin da biyar

 

 

 

 

 

Da sauri ta zari safan hannu ta je ta wanke hannunta ta saka safan ta Debi antiseptic ta kwara a gaban matar sannan ta nitsa hannunta tana laluben saman kofar cervix din

Jimawa kadan ta zare hannunta ta fito tana rubuta findings dinta a folder din client din

 

 

 

Sannan ta chanjawa matar kayanta zuwa na haihuwa ta kaita delivery bed ta kwantar da ita

 

Ta dakko wani Leda me belt ta d’aura mata belt din asaman cikinta ledar a kasan duwawukanta

 

 

 

A nutse ta fara harhada kayan haihuwar ,wannnan ya tabbatar ma da matar haihuwarta yazo kenan

 

 

 

 

 

****

 

Bayan awa daya TBA ummy ta yaye screen din da ya kare matar da ta haihu ,ta tafi ta ajiye fine baby girl din akan scali ta gwada nauyin jaririyar sannan ta wuce tana gogewa yarinyar jikinta da olive oil

Saida ta kimtsa yarinyar da uwar tsaf sannan ta nado baby cikin showel ta fitoma da mijin matar gurin zaman relatives d’in

 

 

 

 

 

Wani qasurgumin Alhaji ta gani kuma da gani naira da boko ta gama tsumasa yina safa da marwa yina tsatsafe zufan goshinsa

 

 

 

A hankula ta taka gabansa tana rungume da babyn

 

 

 

 

 

_congratulations Mr. Your wife gave birth to baby girl_

 

 

 

(Ina tayaka murna ,matarka ta haifi d’iya mace)

 

 

 

“Mace ko maza”ya fad’a a qagauce

 

 

 

Mamaki abun ya baiwa ummy ace matarka ta haihu amma kana tambayar mace ko maza da yawa

“Sir macen dai guda d’aya” ta fad’a tana dan sakar masa da murmushin tabbatarwa

 

 

 

 

 

Kallonta yayi ,irin kallo mai ma’anoni iri iri

 

Sannan ya doka mata tsawa

 

“Ke !

 

Sa idonki cikin nawa ,dama Ku unguwar zoma kun yi qaurin suna wajen Satan jarirai…me kike nufi zaki fitomun da yarana maza biyu ,ko ko kuwa sai nakai zancen sama…?”.

 

 

 

 

 

Mamakine ya kama ta sosai,a take ya fara bata tsoro ,ganin yanda a take fuskarsa ya hade zuwa ruwan rikici da tashin hankali

 

 

 

A hankali ta fara ja da baya da baya ,yina biye da ita har suka kai gaban nurses station d’in

 

 

 

Murya ya soma bud’ewa yina zuba ruwan bala”i yina qoqarin qwace yarinyar a hannunta ,a yanda ta lura dashi tasan tabbas zai iya buga yarinyar da bango ,hakan yasata qanqame yarinyar ta soma kuka

 

Cikin fushi metron Abimaje ta miqe tana kallonsu duka

 

 

 

Wai lafiya kuwa…nan fa asibitine ba wajen tashin hankali ba in fitina ya kawoku cikin sauki Ku futa waje kuyi”

 

 

 

 

 

“Karki raina mun wayo kinji…ko a fitomun da twin gentle babies dina ko kuwa inyi qarar asibitin gabad’aya

 

 

 

 

 

***

 

A hankali qaramin case ya zama babba police har sun shiga maganar ,allah sarki ummy en sandan na zuwa suka saka ta a motansu da sauran midwives din da suke on duty

Nigeria gajaniya ,shigarsu be wuci da awa biyu ba duk aka fiddasu itakuma aka wuce da ita cell ،zata zauna a ciki har sai an gano inda jariran suke ko kuma ranar shiga kotu yayi,don har ya shigar da qara kotu

 

 

 

 

 

***

 

 

 

Qarfe Tara Na Daren ranar tana takure a cikin cell da baqin duhu ga kayanta masu duhu hakan ya qara jawo hankalin saurayen wajen dawowa kanta ,banda kudin cizo da suke watsowa daga saman silin din kamar zasu tsotseta danya

 

 

 

Ihu take kurmawa tana bibbige fatar jikinta

 

Hakan yasa wata er sanda leqowa da er iccenta a hannu

 

 

 

” yi mana shiru makira ,kina er talaka ana hada baki dake kuna sace jariran mutane to yau dubunku ya cika …gwara kiyimun shiru kafiin in amso makulli inzo in lallasaki”

A wajen reception din kuwa Hajara yayan ummy ne da akafi yiwa laqabi da *keken maza* ta shigo tana rangaji cikin wani matsatsen siket da Riga na atamfa ,dankwalin kayan ta riqesu a hannu da jaka mayafin rabin kanne kadai ya rufe da mayafin kayan

 

 

 

 

 

Tana tafe tana rangaji nonuwan ta na boosting suna bajewa a cikin breast cup duwawukanta suna wani irin girgiza amma dukda haka ta tattaro duwawun ta hanyar Jan siket din sama zuwa qasan duwawun nata

 

 

 

 

 

Zuwa tayi gaban wani dan sanda dake da alhakin sakaye mutane a Bayan kanta

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button