Latest Updates

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 43

Sponsored links

“Maganar gsky danku is in a critical condition because heart rate dinshi is very high,it’s more than 130 beats per minute which is very dangerous,normal rate should range from 60-100 beats,kunga ko akwai matsala sosai, kuyi kokari a masa abinda yakeso tin kafin heart dinsa yayi blowing!”…….

Kallon juna momma da daddy sukayi suna zaro ido,suka daure dai suka amsawa likitan sannan suka fita….

Suna fita daddy ya kalli momma yace……

“Kinji dai abinda Doctor yace, tin wuri in kinsan wacce yake magana akai gwara ki fada tin kafin ya mutu”……

Dagewa momma tayi akan gamo khaleel yayi ita batada masaniya akai, yes tasan ciwon khaleel na matukar damunta but that doesn’t mean ta barsa yayi settling for less, zata kuma dage da addu’a Allah ya yayemasa wannan abu daya dorawa kansa, amma kome za’ayi bazata nuna tasan wacce yake nufi ba……

 

Sai bayan azahar khaleel ya farka,yana farkawa ya birkice musu sai an kaishi gida,shiyasan tananan kuma ze ganta inyaje….

Ba yadda momma da daddy da Doctors basuyiba akan khaleel ya zauna ya kara samun lafiya,amma ya nuna sam baze zauna ba..  Sunaji suna gani suka rankaya suka tafi gida…..

Ko gama parking daddy beyiba khaleel ya fita daga motar,direct part din mama ya shiga,luckily ya kuma ganin Imaan da Husnah a zaune a parlour,baice musu komai ba ya kamo hannayensu ya fita daga part din,sudai binsa kawai sukayi da ido…..

Part din momma yayi dasu, ya tarar da momma da daddy suna tattaunawa…. Kallon su imaan yayi yace

“Kunce min a part dinnan take, toh ku fito min da ita!”…..

Zuba mishi ido sukayi duka banda daddy da ransa ya baci ganin kamar dagaske ba gamo khaleel yayi ba momma kuma bataso ta fadi gaskiya,su husnah ko rasa abinda zasu ce sukayi….

Daddy ne ya hada rai cikin tsawa yana nuni dasu husnah yace….

“Oh ashe kuma kunsan wacce yake magana akai?”sannan a tsawace yace…..

“who is that?”….

A tsorace husna da imaan sukace…

“Kamar fatima zainab yake nufi daddy”…..

A take gaban daddy da momma yayi wani mugun faduwa,ita momma saboda asirinta karya tonu na karyar da tayi, shi kuma daddy saboda wani dalili nasa daban…..

Da sanyin muryar daddy yace…..

“Ina fatima zainab din take?” Ya fada yana kallon momma…..

A firgice momma tace bansan inda take ba kuma ba ita yake nufi ba!”….

“Ita nake nufi daddy”… cewar khaleel batareda da tabbacin ko ita din bace…..

“Koma ba ita bace a nemota duk inda take a gidannan yanzu!, Imaan ku tashi ku nemo min ita!”…

Tashi sukayi da sauri suka shiga dube duben inda zasu ganta……

Babu inda basu duba ba amma shiru kamar baayi halittarta ba….

Dawowa sukayi suka fadawa daddy basu ganta ba….

Jin haka khaleel ya tashi da sauri ya shiga nemanta shima,haka yagama dube dubensa bai ganta ba, sosai ya daga hankalinsa ganin sun nemeta sun rasa….

Hakanan hankalin daddy ya kasa kwanciya da momma,yaki yarda batasan inda yarinyar take ba duk da bazaiso ita khaleel yake nema ba,saidai khaleel kamar rayuwarsa yake babu abinda baze iya masa ba…..

“Koki fito da yarinyarnan ko a bakin aurenki wallahi!!”….

Daddy Ya fada a hassaale..…..

Zaro ido momma tayi tace…..

“Alhaji wani irin magana ne haka a gaban yara?, nifa bansan inda yarinyarnan take ba”…..

“Kindai ji abinda na fada miki,na baki 10mins kuma!”…..

Ba karamin rudani momma tashiga ba,wannan wani kalan masifa ne?, itafa matsalarta daya da daddy abu kadan sai yace a bakin auranka, Itako da wannan aure ya mutu ai gwara ta fito da ita kawai inyaso daga baya sai tasan yanda zatayi……

Haka akayi kuwa cikin borin kunya ta dauko makullin dakin ta mikawa khaleel,sannan ta nuna masa dakin……

Khaleel baice komai ba ya nufi dakin,hannu na rawa ya bude ya shiga da sauri…..

And there he saw her lying helplessly, ko numfashi batayi alamun dai ta suma,he couldn’t help it but held her tight,from that moment, that very moment he knows every single breath of his depend on her…..

“This is all I know about Fatima zainab”….. Khaleel ya fada yana sauke numfashi kamar wanda yayi tsere……..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button