Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 38

Sponsored links

“Hafsah zoki bude kofarnan kafin na ballata”… Dan ganin kofar a rufe ya kara tabbatar masa da batada gaskiya….

 

Jin muryar daddy yasa mama ta fito tana dingishi ta nufi kofa dan su husna har lokacin basu budeba…

 

Bude kofarta yayi daidai dajin saukar wani kykkyawan mari a kuncinta da yariga yayi jahur dalilin marin da tasha a gurin fatima zainab….

 

Dagowa tayi da sauri murya na rawa tace

“Alhaji lfy? Ni ka mara?”

“An mareki din munafuka,azzaluma,Allah ya isa tsakanina dake,kuma ki saurari sammaci daga court dan yanda kika kasheta toh kema sai an kashe ki wallahi!”….. Ya fada a hassale

“Wai wa kake magana a kai ne?,ni wa nakashe?”

 

Wani marin ya kara mata sannan yace

 

“Au baki san wacce kika kashe ba,ki bari in kika ganki a gaban kotu sai ki musu bayanin yadda kika konata”…..

 

Take idan mama ya rena fata,cikin rawar baki tace

 

“Wlh bata mutu ba,bata kone ba,kuma……”

 

“Karya kike azzaluma,an tabbatar min da ta mutu,kuma saina tabbatar da anbi mata hakkinta,wlh sai ankashe ki kamar yadda kika kasheta,ki saurari sammaci daga kotu”….. Yana fadin haka ya fita daga part din,ya nufi police station direct……..

 

Tinda Doctor yace tazo office hankalinta yake a tashe,cike da zullumi ta zauna tana jiran abinda zece… Dan rubuce rubuce Doctor din yayi sannan yace “Matarsa ce ne?”

 

Kallonshi tayi alamun bata fahimcesa ba,tace

 

“Bangane ba Doctor”

 

“I mean patients din da sukayi accident,mata da miji ne?……

 

Rasa me zatace tayi,dan ita kanta bata sani ba,kuma a tantirancin Deen tsap sai ya iyayin aure baa sani ba,so kartace ba matarsa bace a samu matsala daga baya….. Gyada ma Doctor kai kawai tayi alamun eh matarsace…..

“Well Alhamdulillah zamuce akan su duka dan komai yazo bayanda muke tinani ba,amma akwai dan investigation da mukeyi akan ita matartasa,idan mungama we’ll let you know,meanwhile are you his mom?”…….

Murmushi tayi jin ance komai yazo da sauki sannan tace

“Yes,zan iya ganinsu yanzu?”

“Sure,let me lead you”…..

Ya fada yana mikewa,bin Doctor din tayi har suka karasa dakin da aka kwantar dasu,nuni ya mata da tashiga ciki,shikuma ya koma office……

Tinda tashiga takejin gabanta na faduwa,su biyu kadai ne a well furnished room din,kasa karasawa tayi ganin bugun zuciyarta ya tsananta,wani irin abu takeji da takasa fassarawa,hakan kuma tasan yanada nasaba da anxiety din data shiga,ga pressure din da Deen ke sawa rayuwarta……..

 

Karasawa tsakiyarsu tayi,saita rasa gurin wa zata fara zuwa,ta dade tana sake sake a ranta kafin ta samu courage din zuwa bed din Deen,kallonshi tashigayi hawaye na zuba daga idanuwanta,wannan wani kalan rayuwa ne,ka haifi mutum baka haifi halinsa ba?inba dan hannunka baya rubewa kayar ba da tini ta fita sabgar rayuwarsa?,shi kwata kwata be san ciwon kansa ba,bai damu da damuwar kowa ba,be damu da wani hali zesa mutane a ciki ba,shidai duk abinda ya raya masa shi yakeyi,kamar wanda aka chanja mata dan Deen dinta ba haka yake ba sam,lokaci daya rayuwarsa ta koma gefen hagu batareda wani dalili ba,yanzu gashi accident yayi wai da mace? Macen da basusan wacece ita ba,tasan dai akwai dalili dan Deen baze tabayin zina ba,inma tare suke zaune saidai in aurenta yayi…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button