Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 48

Sponsored links

Sai ajiyar zuciya da take faman saki a jajjere. Da alama ita ɗaya ta kwana a ɗakin batare da tasan sanda ya fice ba. Hanunta ta kai saman goshinta da zuwa yanzu Alhamdullah babu matsanancin ciwon kan nan data kwanta da shi. Sai ma ɗan sanyi-sanyi da damshin zufar data haɗa ya haddasa mata. Janyewa ta sake yi tana mai lumshe idanunta, haka kawai take jinta wata daban a yau kamar ba Iffahn Babiy da Ummu ba. Ko miye dalilin jin hakan bata sani ba. Kabbara salla da aka farayi ya sata miƙewa zumbur tana ture komai gefe. Gaba ɗaya jikinta babu ƙarfi, ga mafarkin da tai ya sake nunar mata da gaɓɓan jikin baki ɗaya. Haka dai ta ɗan watsa ruwa mai ɗumi ko zai saki sannan tayo alwala ta fito. Bayan ta gabatar da salla maimakon ta koma ta kwanta sai tai zaman karatun Alkur’ani ko zata samu nauyin da zuciyarta ta mata na kwana biyu ya ɗan rage…

Saɓanin ita shi ko rintsawar ma baiyi ba gaba ɗaya. Dan tun bayan barowarsa ɗakin da take yana zaune ne gaban laptop yana aikin da shi ya barma kansa sani. Har kusan uku yana zaune kafin ya tattara ya ajiye ya ɗauro alwala. Bai tashi a sallayar ba sai lokacin asubahi da zai wuce masallaci. A maimakon Gym da ya saba shiga ko yin wasan takobi a wasu ranakun sai ya nufi sashen Malikat Bushirat ta sirrintacciyar ƙofar dake kaisa sashen batare da kowa ya gansa ba idan yaso hakan. Jin nutsatstsiyar muryarsa nayin sallama a can ƙasan maƙoshi Jasrah da Malikat Bushirat suka dubi juna a yanayin mamaki. Cikin rashin aminta da abinda suka jin Malikat Bushirat ta bada umarnin shigowa. A maimakonsa shi ɗinne kuwa. Shi kam baiyi wani mamakin ganinsu taren ba duk da a yanzu aka idar da salla, dan yasan ɗunbin shaƙuwar dake tsakaninsu ta dabance. Maimakon zama a cikin kujera a hankali ya kai zaune kusa da Malikat Bushirat dake zaune kan sallaya har yanzun. Dan tana idar da salla Jasrah ta shigo mata. Gab-gab da ita yake zaune yana mai tanƙwashe ƙafafunsa tare da ɗaura kansa a kafaɗarta. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana lumshe idanunsa.

Malikat Bushirat da ke kallonsa cike da tausayawa sanin in har ta gansa a yanayin nan yana cikin damuwa ta kai hanunta kan tattausar sumarsa yalwatacciya ta shafa a hankali. Nan ma ajiyar zuciyar ya ɗan ƙara saukewa. Kafin ya motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta “Barka da asuba ya Ammie-na”.

“Ka tashi lafiya Saiful-malik”.

 

Ta amsashi da kulawa tana sake tura yatsunta cikin sumar kansa a hankali. Kai kawai ya ɗan gyaɗa mata, sai kuma batare da ya dubi Jasrah da ke kallonsa ba ya ce, “Aunt good morning”. Murmushi ta saki jin yau kuma ita ake gaidawa. Itama ta amsashi da kulawa tana tasowa da ga inda take ta dawo ta ɗayan gefen Malikat Bushirat suka sakata tsakkiya ita da shi. Idanunsa ya ɗan buɗe kaɗan ya mata hararar wasa, a zahiri kam babu alamar ko murmushi a fuskarsa. Cikin fisgo maganar tasa da kamar an masa tilas yace, “Ammie kice ta tafi ta barni, ita kullum tana nane da ke tai auren ma baki huta ba”. Wani sassanyan murmushi Malikat Bushirat ta saki, dan yanda yay ɗin sai ya tuna mata da ƙuruciyarsa lokacin idan sunje dubashi harda Jasrah. Yata mita kenan Jasrah ta tafi tunda ita tana ganinta kullum har sai mahaifinsa ya shiga lallashinsa yake haƙura. Ita kanta Jasrah sai komai yake dawo mata, fuska ɗauke da murmushi tace, “Nikam babu inda zanje, sai dai kai ka koma inda ka fito ka barni da mamata”. Fuska ya ɗan kauda gefe yana sake tsuketa, amma baice komai ba. Ita kuma Jasrah ta cigaba da ɗan tsokanarsa kamar yanda takeyi a baya Malikat Bushirat na karesa tana musu dariya. Shi dai da ya fara takalo wasan bai sake ce musu ko kanzil ba.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button