Wace Ce Ita Book 2 Chapter 28
Ko kafin khaleel ya karaso sun bar gurin, shiga motarsa yayi ya bisu a baya a shima……
Wani irin mugun tuki Deen yake kamar ze tashi sama, kauce masa kawai ake a hanya, tuni ta dade da galabaita tin a jaye jayen da suka dingayi da ita har numfashinta dakyar yake fita, sosai tsanar Deen ta ninku a ranta dan ya zame mata tamkar karfen kafa tinda ya shigo rayuwarta, ada ita ake bi kuma sai abinda tace amma yanzu dole yake mata saita bishi ko tana so ko bata so, yazo yayi kane kane akan lamarin rayuwarta kamar wani ubanta…….
Ikon Allah ne kawai ya kawosu gidan mami dan duk inda sukabi sai andinga Allah yasa karsuyi hatsari da mugun tukinnan da me motar yake…….
Horn yake babu kakkautawa a bakin gate din gidan mami, sai akayi rashin saa gateman din daya gama jinya ya dawo ya tafi ya dan zagaya, da sauri yazo ya bude kofar bayan ya fito, yana ganin Deen ne ya manna a guje dan be manta illar dayamasa ba last time, a halin yanzu ma hakorinshi guda daya ya tafi…..
Ko daidaita parking Deen beyiba ya fito daga motar, janyota yayi ya fito da ita sannan ya fara janta da karfi har ya kaita parlour mami, wurgata a kasa yayi ya cire belt din jikinsa dan yasan inbe fasa mata jiki yau hankalinsa baze kwanta ba, zuga mata guda daya yayi ta saki wani karar da saida gidan ya amsa, ze kara zubamata kenan Umm ta rike hannunsa tana fizge belt din tace;
“Ashe baka da hankali saif? Meh tamaka zaka duketa? How can you even think of beating a lady, ashe bakada imani baka da tausayi? Tarbiyyar aka baka kenan?”……..
Tinda Mami da Umm sukaji wannan mugun horn din sukasan Deen ne, da sauri suka sauko saidai anyi rashin saa dan har ya fara zuga mata belt din……
“Umm dan Allah ki barni in babballa yarinyar nan ko zuciyata zata samu salama, kinsan metayi ne?”……..
“Koma me tayi be kamata ka tabata ba kodan lafiyarta sannan a responsible man won’t beat a lady kome tayi kuwa”………..
“Count this stupid girl out, dan Allah ki bani in fasa mata jiki!”……
Ya fada yana fizge belt din a hannun Umm ya daga da nufin cigaba da dukanta mami ta sauke masa wani lafiyayyen mari tana sake kwace belt din…….
“Wai me yake damun brain dinka ne? Akanka aka fara zafin zuciya ne, kai a wa zakazo kana dukan yarinyar mutane? Meyasa bakada tinani ne? Tana fama da kanta zaka duketa, inka kasheta ai sai kafi kowa shiga damuwa, bismillah cigaba da dukanta”……
Ta fada tana mikashi belt din…..
Durkushewa yayi a kasa yanajin kamar yasa kuka, tabbas da ze iya kuka da yau yayishi saidai duk girman abu taurin zuciyarsa bata bari yayi kuka, ko mami da dad da suka haifeshi basu taba ganin kukansa ba, haka Umm ma data renesa…….
“Kunsan me suke shirin aikatawa ne? Guduwa fa zasuyi itada yaron mugunchan da bamusan dame yake nemanta ba, amma saboda karamar kwakwalwarta take cemishi zata bishi su gudu suyi aure gasu tantabaru, har fa I love you tace mishi mami, wai har wannan yarinyar tasan soyayya Umm?”……
“Au yanzu kuma tayi yarinya ta fara soyayya? Ina cewa kayi zaka mata aure dama? Tinda ga wanda takeso sai ka aura matashi”…