Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 53

Sponsored links

Shaƙaƙƙiyar muryarta da ke fita a dakushe saboda sarƙewar da tai ta sake ratsa dodon kunensa. Cak ya sake tsayawa tamkar wanda ake juyawa da remote, sai kuma ya ɗan waiwayo ya dubeta ganin abun nata serious ne. Tana a kwancen da take dai ta juyama ƙofar baya. Kallon kusan sakkani a shirin ya mata sai kuma ya juya ya cigaba da tafiyarsa batare da ya tanka ba. Idanu ta rumtse da ƙarfi jin ya fice a binsa.

Ranta a dagule cikin kamar bori-bori ta shiga kaima gadon ƙananun duka da tittirza ƙafafunta tana fadin, “Ni dai na faɗa ma gaskiya ai, duk abinda ya sameka kai ka sani mi ma ya shafe ni”.

(🥱Ato idan ya mutu bashi ya huta ba Iffah’r mu🤭🏃😜).

 

★Tsahon wasu mintuna bata iya ta tashi a kwancen da ya barta ba. Kokawa take da zuciyarta dake ingizata taje ta duba karfa ya fita ɗin. “In ma ya fita shi ya sani”. Ta faɗa a fili tana tura baki irin ko’a jikintan nam. Sai kuma can ƙasan zuciyarta ta ayyana mata (Idan ya mutu shikenan bazaki san gaskiyar rasa iyayenki da sanin waye Ajmaal ba fa kenan) zumbur ta miƙe kamar wadda aka tsikara, sauri-sauri ta fisgi mayafin abayarta ta yana a kai tana zira slippers. Ko sanda ta zauna a sashen bata san wannan ɗakin ba, amma ko gezau ta fito tana kalle-kalle. Da canki canka ta fito katafaren falon kamar wadda aka jeho.

 

Da sauri Sayeed Fayzul-haq da ke zaune a ƙasa gefen ƙafafunsa da wasu tarkace marasa ƙyan gani ya ɗago, shiko hamshaƙin ko motsi bai yi ba idanunsa na kan waya da ke hanunsa. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke da ɗan galla masa hararar ƙasan ido, sai dai kuma can ƙasan zuciyarta wani irin bugawa yake da sauri-sauri. Dan tabbas tarkacen gaban nasu irin abubuwan da ta gani ne a mafarkinta kamar yanda kayan da ya sanya sukai dai-dai da wanda ta gani sanye jikinsa a mafarkin.

 

 

A ɗan daburce Sayeed Fayzul-haq ya sake maida kansa ya rissinar. Tunaninta ya katse cike da girmamawa ya ce, “ALLAH ya ƙarawa Zawjata-almilk lafiya da tsohon rai mai albarka. Barka da fitowa”.

 

Jin al’amarin tai wani gin-girin-gin ganin dattijon da shi kansa Tajwar Eshaan ɗin zai girmesa nesa ma ba kusa ba amma yana gaisheta da wani sinne kai na tsantsar girmamawa. Kai ita kam wannan mulkin mallaka na masu mulki baya burgeta. Tajwar Eshaan ɗin da har yanzu bai nuna yasan da zuwanta wajen ba ta ɗan saci kallo, sai kuma ta ɗauke a kasalance ta buɗe baki tana gaishe da Sayeed Fayzul-haq. Bawon ALLAH duk sai ya rikice, duk da kasancewarsa shaƙiƙin a zuri’ar gidan ina shi ina Zawjata-almilk ta gaidashi. Komai bata sake cewa ba ta juya ta koma hanyar da ta fito.

 

Da kallo ya bita ta ƙasan idon da tun ɗazun yake kallon nata dama. Harga ALLAH ta fara bashi tsoro. Dole yace tsoro, da farko ƙin ɗaukar abinda ta faɗa ɗin da muhimmanci yayi, amma sai zuciyarsa taƙi yarje masa hakan. Shine ya kira Sayeed Fayzul-haq akan a sallami shari’ar mutanen da ke jiransa sai nan da kwana biyu bisa wani uzirinsa. Cikin girmamawa Sayeed Fayzul-haq ɗin ke sanar masa ma ai ɗaya a ciki bai ƙara so ba har yanzu, dan sunama shirin tura dakaru nemosa ne kasancewar dama shine wanda ake ƙarar.

A dakatar kawai ya bada umarni ya yanke wayar. Bayan tabbatar da fitar kowa Sayeed ya sake kira ya sanar masa. Shine ya bada umarnin a duba masa kujerar zaman nasa da tace an saka abu. Sai gashi kuwa a cikin abinda baifi mintuna ashirin ba Sayeed Fayzul-haq ɗin ya iso da tarkacen da aka samu ɗin, daka gani kuma kasan kayan surkulle ne..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button