Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 92

Sponsored links

Bayan an idar da salla ya samu rakkiyar manyan masarautar duba mahaifiyarsa. Duk da amota suke duk inda motocin suka gitta hadimai ƙasa kawai suke zubewa kawuna a sunkuye har suka ƙarisa ƙofar sashen. Motar da yake ciki ma har cikin barandar gaban falonta ta tsaya. Amintaccensa da yay saurin fitowa da ga gaban motar ne ya buɗe masa. Shiru babu alamar zai motsa balle ya fito har sai da minti ɗaya da sakkani ya shuɗe. A hankali ya ziro ƙafarsa dake cikin takalman masu tsananin ƙyau da ɗaukar idon mai kallo farare tas heif cover, sai da ya sake jan wasu sakkanin kafin ya zuro ɗayar, nan ma ya sake jinkirtawa sannan ya fito gaba ɗayansa. Tuni mayataccen ƙamshinsa ya mamaye sashen tunkan ma ya shiga. Hadimai kam rige-rigen shigewa suke dan mai RUMAN ne fa da kansa ba aike ba. A waje kam jami’an tsaro sun zagaye sashen tamkar ba’a cikin gida ba. Ameera Danish-Ara da ke zaune a falon tare da Ameera Haifah da wasu a cikin matan masarautar masu faɗa aji da suka shigo duba Malikat Bushirat ɗin tuni sun miƙe kawunansu a ƙasa. Takun sawayensa kam tuni ya saka kowa nutsuwa kowa na satar kallon hanyar da zai shigo da kallo. Yayinda ƙafarsa ke taka cikin falon babu wanda bai ja numfashi ba, dan a wajen ado kam kowa shaidane Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed ɗawusu ne. Ƙamshi kam ba’a magana idan yana waje kowane turare disashewa yake duk ƙarfinsa. Ko sau ɗaya bai kalli kowa ba, takunsa yake a nutse cikin izza da ƙasaita da ka gansa kaga gwarzon gwaraza mai gwara kawunan gwarzo mai son nuna gwarzantaka. Gaisuwar da suke ta faman masa Sayeed Fayzul-haq ne dake take masa baya kawai ke amsawa. Dan sauran jama’ar da ke a tare da shi duk a farkon shigowa falon suka ja birki.

Sayeed ɗin ma a ƙofar ɗaki ya dakata bayan ya buɗe masa ƙofar ɗakin da akai musu iso Malikat Bushirat na ciki. Isar ƙamshinsa ciki kafin shi ya saka Jasrah da ke kusa da ita tana bata shayi miƙewa da sauri. Malikat Bushirat kam idanunta dake matuƙar jazur ta zubawa ƙofar zuciyarta na wani irin bugawa da sauri-sauri. Tunda ya shigo shima kaifafan idanunsa dake sakeye cikin gilashi na kanta. Nata dake cikowa da hawaye ta rintse da sauri tana kauda kanta, wani irin zafi takeji, zafi mai amsa suna zafi na gaske a ƙirjinta har tana jin turirinsa a maƙoshi. A maimakon zama a kujerar da Jasrah ta gyara masa bakin gadon ya kai zaune. Hannun Ammien tasa ya kamo a hankali cikin nasa ya sumbata. Maimakon murmushi da take sakar masa a da idan yay mata hakan yanzu hawaye ne masu zafin gaske da ta kasa riƙewa suka ziraro da gudun tsiya kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da duk ta dame kamar ba Malikat Bushirat ɗin nan ba ƴar gaye, hamshaƙiya ƴar ƙwalisa. Idanunsa ya rumtse a hankali hawayen na ratsa har tsakkiyar zuciyarsa. Ya jima a haka kafin ya buɗesu ya sauke a kanta. Handkherciff ɗin jikinsa ya zaro ya miƙa mata, tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, *“لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ .*

_La ba’asa tahoorun in sha’al-lah._

(Ba komai, tsarkaka ce in ALLAH ya yarda).

أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ *.(سبع مرات)*

_Asalul-lahal-‘azeem rabbal-‘arshil-‘azeem an yashfeek._

(Ina rokon ALLAH mai girma, UBANGIJIN Al’arshi mai girma, ya warkar da kai)”.

_(MANZON ALLAH, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; “Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya faɗi wannan (addu’a) sau bakwai face ya sami lafiya”.)_ (ALLAH ya azurta marasa lafiyar mu da lafiya, ya basu ikon cinye jarabawa, yasa ta zama kaffara garesu. Masu ita ALLAH ya ƙara musu, ya karemu daga cutukan zamani masu haɗari da hana nutsuwar zukata😭🙏).

Damƙe handkherciff ɗin kawai tai taƙi share hawayen da suka gagara tsayawa. Sai Jasrah ce ke faman amsa addu’oin sa da sannu. Cikin damuwa ya kalli Jasrahn batare da yace komai ba. Ta fahimcesa, dan haka ta fara bayani tana sharar hawaye itama. “Nima ban san ainahin abinda ke faruwa ba wlhy. Amma dama kwana biyun nan duk bata cikin walwala. Na kuma tambayeta amma tace min babu komai yanayine kawai, sai jiya dai da ƙyar ta ce min akan matarka ne, tace ka saketa amma ka share ko zancen baka sake tadawa ba, ta nema iso gareka ance ka shige ciki a jiya after isha’i. Ni dai na bata haƙuri da nuna mata abi komai dai a sannu kodan abubuwan da suka faru na rasa matanka da kai idan kuma akace ka saki wannan haka ɓakatatan ba’a kai ƙarshen case ɗin nan ba maimakon ita da bata da gaskiya sai a koma zarginka kai. Ta nuna kamar taji ma wuce, amma sai banyi barci cikin nutsuwa ba dan nasanta da saka abu a rai, shine ana idar da sallar asuba nazo dan gaisheta na sameta a ƙasa babu alamar rai tattare da ita. Na nemeka amma baka ɗaga ba, dole nai kiran amintacciyarta dan ta sanar da Mammah. Sai da ma sukazo ne muka iya ɗagata a ƙasan ni da Nina Ammarah da ƙyar, kafin a kira Doctors sukazo kanta har dai ALLAH yasa ta farfaɗo suka sake maidata barci dan tanata zabura kamar wadda ke a firgice. Sun tabbatar jininta ya hau ƙololuwa har yanama zuciyarta barazana ma. Amma dai yanzu data farka Alhamdullah Dr Aliyah tace jinin ya ɗan sauka bakamar ɗazun ba”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button