Mu Rayu Tare Hausa Novel Complete
Zaune take gaban mahaifiyar tata wacce ta kasance mahaukaciya, Iffat yarinyar ƴar shekara huɗu, tunda ta fara wayo ta gano basu da gidan daya wuce bola, inda taga mahaifiyarta take zama koda yaushe.
Iffat yarinya ce mai wayon gaske, gata da surutu, tana gyarawa mahaifiyarta zani wanda ya buɗe ana ganin ilahirin cinyoyinta, taji ance “kee yarinyar mahaukaciya ungo”
Kafin ta juya taji saukar abu a gabanta, a hankali takai dubanta tare da kunce baƙar ledar dake ɗauke da abinda mutumin ya jefo mata, tana washe baki tace “Umma tuwo ne miyar kuka zakici?”
Umman ta karɓe ledar tare da ajiyewa a gabanta, ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya, tunda Iffat taga Umma ta kusa cinye tuwon, ta janye ledar tare da rugawa da gudu, tana gudun tana cin tuwon.
Umma ta miƙe tana wasu irin yaruka wanda Iffat ɗin ta gane me take faɗa amma sam taƙi kula Umman,
UNGUWAR DALA, DAKE CIKIN GARIN KANO.
“Haba Wasila tun ɗazu na kawo cefane amma naga ko tukunya baki ɗora ba?”
Cikin yanayin rashin jin daɗin gane halin da take ciki na hura wutar tace “malam tun ɗazu nasa yara su kwasomin makamashi, wlhi har yanzu basu dawo ba gashi gawayin sam yaƙi kamawa, ko uffan bece ba ya juya yana tsaki, Juwairiyya ta fito riƙe da ƙugu tace “baba..”
Har ya kusa kaiwa bakin ƙofa ya juyo, cike da nuna kulawa yace “ƴar baba ya akayi?”
Tana cikin tafiya tayi karo da ƙaton dutse wanda yai sanadiyar kai ta ƙasa, cikin kuka Iffat ta taɓi bakinta wanda yakeyi mata zugi, hannun nata ta kalla, ganin jini ya sanyata fashewa da kuka tana yarfe hannaye, daga can gefe shayin da bredin ya zube, bredin ne dai beyi komai ba, dan haka ta miƙe tana karkaɗe jikinta ta, kasancewar garin yayi duhu, yasa bata hango kofin ba, ta riƙe bradin taci gaba da tafiya tana kuka.
A hankali mutumin ya raba mahaukaciya da zanin jikinta, idan mai karatu yaga mahaukaciyar nan, wlhi bazai fara tunkararta ba, duba da inda jikinta yake fitar da tiririn wari, marar daɗi,
A haka ya faɗa mata ya dinga sukuwa a kanta, daga ƙarshe ya wani shigeta da ƙarfin bala’i har ƙafafuwansa na rawa, kafin ya ɗaura mata zaninta kamar inda ya ganta, shima ya mayar da kayansa, yasa tissue paper ya goge gurin ya fesa turare, kana ya bar gurin da motarsa
Suna tafe yana waya, sai cewa yake “ai nasamu na kwashi gara duk da mahaukaciyar ba wata babba bace amma wlhi tayi daɗi”.
Kafin mutumin yayi parking a inda ya ɗaukota, ya waiga ko ina baiga kowa ba, kana ya ajiyeta tana dukansa, harda cafke masa riga, yai saurin ƙwacewa ya ƙara da gudu, tare da shigewa mota.
Iffat kuwa tayi nisa da anguwar sosai, saboda tsakaninta da inda aka dawo da mahaukaciya yakai nera ɗari, babu wanda ya ganta ya taimaka mata, haka ta dinga tafiya har, takai bakin titin anguwar da suke, wato ɗorayi, tana kuka ta nufi bakin titi ko waigawa batayi ba, sai ji kake ƙuuuuu…ƙiiii…, kafin kace me, wanda basu ga tsayuwar yarinyar ba duk suka hallara a gurin, sakamakon ƙugin motar da suka ji,
Kowa sai ambatar “innalilahi wa inna ilaihir raji’un” yakeyi, a gigice mamallakin motar ya fito, hankalinsa a tashe yana cewa “ku taimaka ku samin ita a mota wani ya biyoni mu kaita asibiti”
Wanda ya taya mai motar sa Iffat a mota, shine yabi mai motar suka wuce asibitin Murtala.
Suna isa aka karɓesu cikin kulawa, sakamakon jinin da yake kokawar kwaranyowa jikinta, aka wuce da ita ɗakin gaggawa,
Sosai suka fara bata kulawa ta musamman, kafin suka sanar musu da cewar “dole zata iya kaiwa gobe, bazai yiwu a sallameta a yau ba”
Hakeem ya danna number Hajiya babba, cikin wani irin yanayi na damuwa yace “Hajiya babba nayi hatsari a hanyar ɗorayi, nidai banji ciwo ba, amma yarinyar taci ciwo, bazan dawo gida yau ba sai zuwa gobe, dan Allah ki sanarwa da Hajiya ƙarama da Dady”
Bayan an gama gyara Iffat, barci mai nauyi ya ɗauke ta, doctor ya kira Hakeem zuwa office, cikin azama Hakeem ɗin ya bishi, anan ne doctor yake tambayarsa “ina iyayen Iffat?”
Hakeem ya sunkuyar da kansa ƙasa, kana yace, “sir a bakin titi na ganta, banma lura tana gurin ba, kawai ƙarar motata ne ya fargar dani, na tambayi wani mutumi wanda suka taimaka min gurin kawota da sanyata a mota, sunce basu santa ba”
Likitan ya girgiza kai kana yace “gaskiya bazan ɓoye maka ba, yarinyar ta samu ciwon taɓuwar ƙwa-ƙwalwa, ba komai zata iya fahimta a yanzu ba, sai dai nan gaba insha Allah idan kuka kiyaye maganin da zamu ɗoraku akai, abubuwan zasu dinga warwarewa a hankali, sannan a kiyaye ɓata mata rai