Mijin Malama Page 4
Mummunan hatsarin ya ja hankalin mutane da yawa, hatsari ne wanda za a iya cewa tsautsayi ne da kuma gangan cin driver da yake driving yana waya. Da gudu babbar mota tayi gaba bayan tayi wurgi da Tajju zuwa gefe guda, nan take kan Tajju ya fashe jini ya fara zuba hannunsa guda ɗaya ya fita fit daga jikinsa ko shurawa bai ba rai ya yi halinsa. Motar dake bin bayan babbar motar data buge Tajju ce ta tsaya, cikin sauri driver da wanda yake gefen mai zaman banza suka fito bakinsu ɗauke da sallati “General kira mana Ambulance” cikin sauri General ya ɗakko wayarsa tare searching asibiti mafi kusa da kuma motar asibitin. Hammad ya ce “Allah sarki, haka rayuwa take Allah ya jiƙansa ya yi masa rahama” General ya amsa da “Amin” da sauran jama’ar wajan suka amsa.
Har Hammad zai juya idanunsa ya sauka akan Envelope dake can gefe guda iska na kaɗata a hankali ya ƙarasa tare da ɗauka, a ransa yana tunanin maybe a samu wani bayanai akan mamaci
Ya ware Envelope ɗin first abin da ya gani shi ne ring irin na al’ƙawarin nan, ya juya ring ɗin sosai sai kuma ya zura acikin aljihu, gently idanunsa ya sauka akan headline na wasiƙar kamar haka.
*_BAD MAN, THE STUBBORN BOY, CRIMINAL, GANG BOY, THE LEADER_*
Daga wannan rubutun idanun Hammad ya sauka ƙasan headline ɗin inda aka rubuta “The memories, was going on my mind, har abad, nasan ni mahaukaci ne da gaske kamar yadda ki ke faɗa Jee” jikin Hammad ya shiga rawa ganin General na ƙara suwa ya tura wasiƙar Aljihu “Lafiya?”
“Actually, good”
Kafin suyi magana Ambulance ta ƙara su aka ɗauki gawar Tajju tare da sanyata ciki, Hammad ya buɗe ya ɗauki wata number da yaga ana ta kira anyi saving da “Bad boy”
“His phone” cewar Hammad bayan kammala komai Ambulance suka tafi asibiti da shi. Suma su Hammad mota suka shiga driving kawai yake amma tuni ya yi losing mind ɗinsa, fatan sa kawai ya isa Gov. Abu-turab Alƙasim, ya san cewa yanzu ya koma gida kasa jurewa ya yi ya ɗauki Wayarsa tare da kiran keɓantacciyar number Abu-turab kusan kira uku kafin ya ɗauka cikin nutsuwa ya ce.
“Uhm” Hammad ya ce
“Your Excellency, akwai damuwa” a taƙaice ya ce
“Kace komai, banda rasa Majee” cikin ladabi ya ce “Am very sorry for that, amma bamu sameta ba, amma mun sami maganin matsalarta, ɗan waye, cikin waye, yadda aka samu cikin duk yana ciki” Abu-turab ya miƙe daga zaunan da yake ya shiga zagaye haɗaɗɗan parlourn nashi fuskarsa tayi jajir. “Ok, meet me at my house” yana faɗin haka ya kashe kiran. Tafiya kaɗan ce ta ƙara su da su cikin gidan Abu-turab wanda yake zaune tare da iyayensa, sojoji birjik ta ko’ina daka nuna rashin gaskiya zaka ji maza akan ka. Girman gidan ya zarce tunani, motoci kala-kala na kamfani daban-daban.
Ko a jerin masu kuɗi ba kowa zaka samu da wannan haɗaɗɗan gidan ba, gida ne 50 by 50 iya compound na gidan zai ja hankalinka balle ciki. Kasancewar ba wanda bai san Hammad ya sa ba wani wahala ya nufi cikin gidan, a Main parlour ya samu Mama na sakkowa daga bene ya yi murmushi ya ce
“Sannu da gida Mama” kallonsa kawai take fuskarta kwance da annuri amma kana ganin sanyin jikinta kasan akwai damuwa, kyakkyawar dattijowa mai nutsuwa da sanin ya kamata,ga ilimi na iya zama da ko wanne mutum ga kyakkyawar mu’amala. “Na ɗauka mun yi laifi yau ne” cewar Mama bayan ta zauna.
“Laifi kuma Mama?” Ta dubesa kafin ta ɗauke kai ta ce “Naga babu ko mai kama da kai, hala wani aikin ka ke” ya shafa kai yana rusunawa ya ce.
“Haka ne kam, ina Yake?”
Ta ɗaga kai zuwa part ɗin dama da yake upstairs ta ce. “Ina son tambayarka dama, meke damun shi? Tunda ya shiga part ɗin sa bayan ya dawo bai fito ba, hatta wajan art ɗin da yake shiga yau shiru, lunch ma bai ci ba na kira phohe number sa na gida a kashe” ta tsare shi da idanu ya ce “Akwai wata tattaunawar sirri da yake da ita, maybe shi ne yake duba muhimman abu kasancewar tattaunawar sai 12 na dare”
Ta jinjina kai tare da faɗin “Allah ya taimaka, kasan ƴar rigimarsa ta hanani sakat ita dai Abbi” Hammad ya yi dariya sosai ya ce “Jiddatul-khairi ai ya saba mata ne” kafin Mama tayi magana sai gata ta fito da gudu ta faɗa jikin Hammad ta ce “Uncle, Abbina” ya ɗauketa ya shiga hawa upstairs yana faɗin
“Daughter me, bari muje muga Abbi sai muje siyan chocolate ko?” Tayi murmushi dimples ɗinta soka loma tana ta masa surutu har suka isa haɗaɗɗan part ɗin da kana ganinsa kasan Gov. Abu-turab Alƙasim ne a ciki. Hannu Hammad ya saka cikin wani screen dake ƙofar nan take ta fito da bayanan Hammad a hankali kuma ƙofar ta buɗe.
Jidda ta ƙwace daga hannun Hammad tayi cikin parlourn da gudu tana kiran sunan Abbi, yana zaune saman kujera daman alrdy ya san da zuwan Hammad ɗin, kayan shan iska ne a jikinsa fara Armless da black ɗin 3 gauter.
Hannunsa ɗaya riƙe da Black tea wanda aka sanya masa zuma a ciki, news yake kallo har Jidda ta faɗa jikinsa hankalinsa baya tare da shi. “Abbina”
Your Excellency barka da yammaci” jinjina kai kawai Abu-turab ya yi.
“Ga wannan wasiƙar, idan ka karanta sai ka ɗauki matakin daya kamata akai, ita kuma zamu nemota In sha Allah” hannu ya sa ya amshi wasiƙar tare da warewa zuciyarsa na harbawa, bai san mene ya sanya duk abinda ya shafi Malama Majeederh ya ke jinsa har ƙasan zuciyarsa ba, barci ya ƙauracewa idanunsa, ga ciwon kan dake ƙoƙarin kwantar da shi.
Duk Yadda ya so ya daure da riƙe kansa ya kasa ya miƙe tsaye da sauri yana ware idanunsa akan paper ɗin, tsoro,fargaba damuwa da kuma firgicin rashin sanin makomarsa wajan Majeederh ya taro ya haɗe masa waje guda.
Ya sanya hannu ya share zufar daya yanko masa, lokaci ɗaya ya hargitse wani zazzaɓi na neman kawo masa farmaki.
“Your Excellency, lafiya dai?” Ba tare daya kalli Hammad ba ya ce
“Ham…mad” “Yes, Your Excellency”
Ya juya gabaɗaya fuska a haɗe ya ce “Tun yaushe nake baka labarinta?”
Kai tsaye ya ce “Shekaru wajan biyar, tun ranar daka halarci musabaƙar da aka yi ta ƙasa”
Abu-turab ya jinjina kai, Elxty 5yrs kenan, a wannan musaɓar ya ji muryar Majeederh, muryar data sanya masa dafin so a zuciya ta zautar da duk wani tunaninsa, ya wanzu cikin muradinta a zuciyarsa, shi kansa ba zai iya sanin abinda ya sanya bai tun kare ta da wannan maganar ba, samun Majeederh Abdul’aziz Khan a garin nan ba wahala zai masa ba. “Har abada Majeederh kada ta san da wannan wasiƙar” da mamaki fal fuskar Hammad ya ce “Your Excellency amma kamar ba a kyauta mata ba, wannan wasiƙar ita zata fitar da ita daga zargi, kuma ita ce zata gane waye ya aikata mata haka” Abu-turab ya koma ya zauna kawo yanzu yasan Bp nasa tuni ya hau cikin kamilalliyyar muryarsa mai tsafta ya ce “Me ka ke nufi?”