Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 4

Sponsored links

ga ‘karfi ba’a magana duk da saninsa danayi yana yaro ‘karfin bala’i gare shi, ya ‘Karfinsa zai kasance yanzu kuma? Hakan yasa bashida Aboki ko d’aya, daga shi sai mahaifiyarsa ita ke kula dashi, duk da kudin da suke dashi nasan bata cikin kwanciyar hankali, malumai da dama sun kasa ceton Junaid a halinda yake ciki,

Junaid yana zama cikin hankalisa amma duk sanda Damusan ya motsa masa tofa ba zaman lafiya, kowa tsere mishi yake sai dai idan anyi gaggawar d’aureshi da igiya mai karfin gaske,”

Umma tana zubda hawaye tana fad’in “ni dai nasan Damusan bazai bar jikin Junaid ba, duk sanda Damusan nan ya mutu shikenam shima Junaid mutuwa zaiyi”

Ayush kam tayi sumar zaune idon ta ya ‘kame ‘kam ko ‘kifta su batayi,

Umma ce ta bubbuge kafad’arta sannan tayi firgitt ta dawo daga sumar zaunen,

Tsananin tsorone ya bayyana a fuskar Ayush jin yanayin da Junaid ke ciki duk da bata sanshi ba amma tana jin fargabar haduwa da shi “hatta idanunsa komawa yake irin na Damusa?”. Tayi tambayar a ranta tareda jinjina kai ,

Ayush ce ta maido hankalinta kan mahaifiyarta sannan tace “Umma kenam bashida magani shi ciwon Junaid din?”

Wani irin murmushi Umma tayi mai ‘kona rai sannan tace “akwai mana, warakar ciwon Junaid yana a jikin ki”

Wani irin had’iyar yawu Ayush tayi ido waje tace “Umma meyasa duk wani tsafinsu yake jikina, shin meye abun dake jikina?”

Tace “ba nace miki raunin mahaifinki yana jikinki ba, to haka shima Damusan tsafinsa yana jikin mahaifinki, da zarar kin cire wannan abun dake jikinki shikenam kin lalata komai, kin tarwatsa mahaifinki sannan kuma Damusan shima tsafinsa zai lalace da zaran tsafin Damusan ya lalace kuma shikenam Junaid zai samu lafiya, Damusan zai fita daga jikinsa,

Sai dai hakan zaiyi matukar wahala saboda dole saikin zubda jininki sosai kafin abun ya fita daga jikinki hakan kuma zai iya jawowa ki rasa rayuwarki”

Fashewa Ayush tayi da kukan gaske tana fad’in “Umma ki gaya mun abunda ke jikina, wallahi nayi Alkawari ko zan rasa rayuwata saina tarwatsa tsafin mahaifina sannan na ceto rayuwar Junaid” kuka takeyi sosai.

Cikin lallami Umma take fad’in “Zan gaya miki Ayush, badon zaki raunana ba dana dad’e da cire miki saidai mahaifinki bazai bari hakan ta faru ba, saboda hatsabibin boka ne,

Amma Zan gaya miki kodan saboda rayuwar Junaid”,

Tana zubda hawaye tace ” *AYUSHMAT* wannan abun tsafin ba komai bane face abunda ke jikin!!

Bata ‘karasa maganar ba taji an sha’ko mata ma’kogaro, numfashi Sama-sama Umma take ta zaro ido waje,

Ji tayi daga sama ana magana cikin tsawa ” KEE BARA’ATU NI ZAKI CIWA AMANA A GABAN ‘DIYATA ZAKI TONA MUN ASIRI, ZAKI MUTU! ZAKI MUTU!! ZAKI MUTU!!! HAHAHA, HAHAHAHA,

Dariya ne mai rikitarwa, nan take ta rasa hankalin ta,

Itama dariyar ta farayi, tana tafa hannayen ta biyu tare da fad’in ” *Junaid* *Damusa* *wayyo* *Damusa* *kamoshi* *naan*” haka ta rinka Maimaitawa tana kwashewa da dariya, alamu sun nuna cewa Uma ta haukace.

 

Salati Ayush ta shiga yi tana fad’in “Uma meye haka? Dan Allah ki daina” kuka ne yaci raanta sosai, tazo zata rungumi mahaifiyar tatan. A haukace Uma ta cillata gefe guda tana fad’in “Damusa ce ke! Kar ki ta6ani, Damusa ce ke!! Ta tashi da gudun gaske ta nufi bakin hanya.

Itama Ayush binta tayi tana kuka tana fad’in “Umma Ina zaki je ki dawo dan Allah!.. Kafin Ayush ta sake magana wata karamar motor ce ‘kirar Jeep brown colour ta taho da gudun gaske bata Ankara ba tayi sama da Umma,

kanta ne yayi mungun buguwa a saman kwalta , kafin kace mai jini kamar anbaliya,

Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un daman Umma mutuwa take jira Gashi kuwa rai yayi halinsa, sai ido a bud’e.

Wani irin ‘Kara Ayush tayi mai rikitarwa, da gudun gaske ta nufi Uman wacce take kwance …

Tsugunawa Ayush tayi gaban Uma tana girgiza ta ” Dan Allah Uma ki tashi karki mutu ki barni, Idan kika mutu ban San ina zansa kaina baaa” wani irin kuka take na fitar hankali “wayyo Umanaa, ki tashi mana”

 

Duk kukan da take mai motar yana kallonta ta cikin madubin motarsa ko fitowa bai samu damar yiba,

Motarsa ya fara ja a hankali zai bar wajen!

Cikin 6acin rai Ayush ta mi’ke ta d’auki wani qaton dutsi ta wurga bayan motor da shi, nan take glass d’in motor ta fashe, kansa ne ya bugu da sitiarin motar tsabar burkin daya Danna,

Ransa ne yayi matukar 6aci, DA karfin gaske ya cankar da marfin motar da kafarsa ya fito yana huci.

Itama Ayush gabansa tazo tana fad’in “Kai wani irin Dabban mutum ne Wanda baka San darajan Dan Adam ba, mungu, Azzalumi Mahaifiyata ka buge amma kamar Wanda ka kashe kiyashi,”

Ya kasa juran kalamanta haka yasa hannu ya shaqo wuyanta da karfin gaske, ya d’agata sama da hannu daya, idanuwansa ne suka fara chanzacolour,

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button