Furar Danko Page 4 Hausa Novel
Babu alamar gargaɗin nata ya zafi MM Atik Kumo, dan wani murmushin ma ya saki da bin ƙugunta da kallo a ransa yana maimaita kalmar _(Furar danƙo a shekara ana damaki baki farau-farau)._ Wani shegen yawu ya haɗiye yana lumshe idanunsa da suka wani ƙanƙance tare da lashe lips ɗinsa.
A gaban motar da Uncle Smart ya ke tsaye taja birki, cikin hucin takaici tai masa kallon sama da ƙasa fuska a yatsine. “Kai kuma malam haka ake aiki a garinku? Kana kallon mutane da kaya bazakaje ka amsa ba!!?”.
Idan motar nan ta motsa to shima da ke jingine a jikinta ya motsa. Wani irin baƙin cikine ya sake turniƙe mata zuciya, “Kai sakarai kai waye da har ina maka magana zaka ɗauke mun kai? kan bala’i…..!”
Da sauri yaron ya katseta da faɗin, “Aunty Lu! Uncle Smart ne fa! Shi bai san ihu, muma idan zai kaimu school ca yake muyi shiru a mota, kuma Daddy ma baya masa ihu ki bari kem…..”
“Kai dalla yimun shiru. Shi ɗin waye da baza’a masa ihu ba. Shashasha da shi driver mai jiran wata tayi a bashi dubu goma”.
Ƙwal-ƙwal yaron yay da idanu kamar zai yi kuka. Ya kalleta ya kalli Uncle Smart ɗin da ya ɗauke kansa kamar ma bada shi take ba. Itako idanu rufe ta cigaba da zazzaga masa masifa kamar mai jiransa dama. Da yawan mutane hankalinsu ya fara dawowa kansu. A hankali ya raba jikinsa da jikin motar, batare da ya sake mata kallo na biyu ba bayan wanda ya mata sanda take gaban MM Atik ya buɗe motar ya shige abinsa, da wani irin ƙarfi ya fisgeta yay reverse ɗin daya saka taron fashewa ganin zai takasu, fuuuu ya ɓace da ga wajen yay hanyar fita airport ɗin baki ɗaya..
Tuni wasu da abin ya birgesu suka shiga ƙyalƙyala dariya da faɗin hakan da yay ya musu dai-dai. Wasu ko mamakin ƙarfin halinsa sukeyi. Duk da dai tabbas guy ɗin ya haɗu iya haɗuwa, sai dai duk wanda ya kalli uniform ɗin dake jikinsa ya san kalmar driver data kirashi da shi kam gaskiya ne. Wasu ko dariya suka shiga kwasa da yaɓa mata baƙar magana musamman ganin wulaƙancin da taima MM Atik Kumo da har yanzu yana tsaye a wajen duk da body guard ɗinsa da sukazo suka zagayesa shima yana kallon komai.
Lulu da gaba ɗaya ta koma butum butumi da wulaƙancin driver ɗin nata tuni jikinta ya fara tsuma. Numfashinta har wani irin fisga yake dan ɓacin rai, da sauri MM Atik ya matso gareta, yayinda security ɗinsa suka fara yima mutane nunin su tafi dan ALLAH. So yake yace wani abu amma wlhy shi tsoronta ma yake ji, bai taɓa ganin masifaffiyar yarinya irinta ba, ga azabar kwarjinin tsiya kamar wata babbar mace mai shekarun dattijantaka. Da ƙyar ya iya furta, “Please calm down Babie…”
“Anƙi ai Calming down ɗin kai kuma!. Har ni sakarai irin wancan guy ɗin mai aikin tuƙi a gidanmu ƙarƙashin ikona zaima wannan walaƙancin? Mi yake taƙama da shi….?” Da sauri yaron nan yace, “To Aunty Lu bana faɗa miki Uncle Smart baya son ihu ba ki daina masa…” Hannu ta ɗaga zata fallama yaron mari MM Atik ya janyesa da faɗin, “Please Babie karki aikata haka”. Idanu ta rumtse da masifar ƙarfi dan kuka ma take jin yana taso mata tsabar baƙin ciki da tuƙuƙin da zuciyarta ke mata duk da kasancewarta mutum mai shegen taurin kai akan abu.. Duk yanda MM Atik Kumo yay ƙoƙarin ganin ta shiga motarsa hakan ya gagara. Dole ya haƙura cikin bodyguard ɗin sa yay mata kiran ɗaya daga cikin taxi ɗin dake wajen da dama su aikinsu ɗaukar manyan mutanen. Nanma ƙin shiga taso yi, sai da ya dinga magiya da roƙonta sannan. Kuɗin dake a aljihunsa ya ciro batare daya irga ba ya ajiye masa kusan dubu goma. Godiya sosai mai taxi ya dingayi tare da tambayar ina zai kaita. Cikin ɗar-ɗar ya dubeta, sai ma yaji ya kasa cewa komai ganin yanda take uban huci.. mai taxi da ya fahimci shima bai sani ba ya dubeta ta mirror. “Hajiya ina zamuje…?
“Gidan ubanka!! Dilla malam kaja mota ban san shiga sharo ba shanu”.
“ALLAH ya baki haƙuri”.
Mai taxi ya faɗa yana kunna mota