Hausa Novels and Stories

Furar Danko Page 10 Hausa Novel

Sponsored links

Ɗakine ɗan babba mai ɗauke da kafet maroon color mai laushi, sai ƙatuwar katifa irin wadda ba’a sakawa a gadon nan. Wadrobe mai biyu sai kanta a gefenta cike da litattafan addini dama na bokon, an ɗan yi teburin karatu da kujerarsa. Ɗakin babu wani tarkace sannan fes yake ga ƙamshi kamar ba ɗakin namiji ba. Uniform ɗin da aka sharɗanta masa sakawa matsayin driver ya cire, a kujerar 2sitter dake ɗakin ƙwara ɗaya ya jefasu ya haye katifarsa da ga shi sai boxer da singlet yay kwanciyarsa yana furzar da tagwayen huci masu zafi da ɗaci, dan abinda yarinyar tai masa sam yaƙi barin ransa. Sai kuma shigar jikinta da tafi komai ƙona masa zuciya. Haka yake shi ya tsani mace haka. Kai koda atamfa ko lass yaga mace tama ɗinkin fidda surar jikinta baƙin ciki yake ji balle wannan da gaba ɗaya ta canja suffarta daga hausawan ta koma kamar wata jinin kafirai. Tsaki yaja mai ƙarfin gaske ya juya kwanciyarsa yana mai ingije tunanin a ransa. Sai dai duk yanda yaso hakan bai yiwu ba. Al’amurin ma yaƙi barinsa yin barcin da yake buƙatar yin ko zai samu sassaucin baƙin cikin dake sukar zuciyarsa.. Da ƙyar ya samu barcin ya ɗaukesa, baima yi na minti talatin ba akai kiran sallar la’asar. tashi yay da ƙyar yana faman yamutse fuska dan a barcin ma harda mafarkinta. siririn tsaki yaja ya miƙe ya shiga toilet ɗin ɗakin nasa, a gurguje yay wanka da alwala ya fito jin har za’a shiga salla. jallabiya kawai ya saka da turare ya fita kasancewar masallacin a kusan ƙofar gidansu yake, dan baifi gida huɗu ba ne tsakaninsu….

Ana idar da salla gidan ya dawo, sai dai maimakon ɗakinsa yanzu ciki ya shiga ɓangaren iyayensu. Gida ne da tun a farkon shigowarka zaka iya fahimtar na zaman mace huɗu ne. Yaran dake kai kawo a tsakar gidan a ƙalla zasu iya kaiwa goma koma fiye da haka, wasu sanye da uniform na islamiyya wasu nacin abinci wasu kuma na ɗan kai kawon aiki. Tsit kake ji duk wani ihu da hayaniyar da gidan ya ɗauka ya tsagaita, yaran suka shiga gaidashi. Sau ɗaya ya amsa musu ya nufi ɗakin mahaifiyarsa kai tsaye. Sun san ba wasa yake da su ba dan haka babu wanda ya damu da yanayin nashi, sai dai sauri-sauri da suka shiga yi na son kowa ya kammala abinda yake ya fice islamiyya kafin ya fito ya sake ganinsu..

Daga ɓangarensa kam da mamaki mahaifiyarsa ke kallonsa daga inda take zaune. A hankali ya kai zaune a ƙasan carpet ɗin da aka saka a gaba ɗaya falon kalar blue. Basu da kuɗi, amma mahaifiyarsa mace ce mai tsananin tsafta da cikar kamala, tanada haƙuri sosai, sai dai bata son raini ko kaɗan ita, dan kana shiga sabgarta zata tabbatar maka da ita ɗin jinin zazzagawa ce.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button