Fulani Page 7 Hausa Novel
Nana na ganinsa ta mike tsaye rike da Labib da tana jijjigashi ta nufi gurinsa. Cike da kulawa da tausayi da kuma kaunar dansa ya sa hannu biyu ya karbe sa.
“What happened?”
“Ba wanda zai fada maka ga abunda ya faru fa, ina dakin kawai yai kyalowa”
“No karya kike na fada muku a daina barinsu su kadai”
Bata sake unkurin cewa komai ba ta koma ta zauna tana kallonsa.
A kafadarsa ya dorashi yana jijjigashi tare da karanta masa ayatul kursiyu ya tofa masa sannan ya nufi hanyar dake kusa da dinning da kansa ya bude kofar ya shiga, yana shafa bayan Labib a hankali yana kallon abunda ke gudana a kasa.
Ta kofar farko Hajiya Karama ya fito ta nufo inda yake tsaye.
Ta karbe shi tana jijjigashi cike da kulawa domin ita ma kanta tana kaunar yaran.
“Nana tace kyallowa yai, na fada musu a daina bar min yara su kadai, if not zan dauke su daga gidan nan”
Ya fada yana juyawa ya kalli wata harabar dabam kana ya aje numfashin da sautin da ke nuna ba da wasa yake ba, biyoshi tai tana girgiza kai.
“Nono Ammy ba zata jidadi ba, am samu mai kula da dakinsu fa, na ce a barta ta kula da su Iya tace bata yarda da ita ba”
Be amsa ta ba ya juya ya fice daga gurin ya barta rike da Labib din a kafadarta.
Murmushi tai tana kara kallon kanta, dogon wando ne da wata riga mai guntun hannu wacce ta tsaya iya kwankwasonta, ba laifi kayan sun matse ta sai dai ba irin matsuwa can can sosai ba, a gurinta hakan normal ne ko ba komai tana jindadin yadda hankalin maza yake tashi idan sun yi arba da irin halittar da Allah yai mata, hakan na mata dadi sosai wai sai dai a gani a hade yawu babu yadda za’ayi da ita.
Bin bayansa tai ta kofar da ya shiga tana cigaba da murmushi, a kujerar da ke kusa da kofar ta zauna ta sa dayan hannunta tana gyara yar karamar jar hular da ke kanta.
“Yayi shiru?”
Nana ta tambaya tana nufo inda Zainab din take zaune.
“Yeah i think yayi bachi”
Ta taba jikinsa sai ta ji shi da dan zafi za tai magana Zainab ta mike tsaye tana kallon Doc Deen wanda ya shigo rike da dan karamin akwatin magani, fuskarsa sanye da farin gilashi.
“Yaushe ka dawo?”
“Jiya….
Ya amsa mata a takaice duk kuwa da kasancewar yana a cikin yanayin da baya son magana, amman ba zai iya kin amsa ta ba, babu abunda Zainab zata bukata ya kasa mata, bayan girman da tai a kusa da shi ta bude ido, kusan ta fi shakuwa da shi fiye da kowa, tana jin maganarsa kamar yadda shi ma yake saurarenta yana girmamata a ciki har da sunan mahaifiyarsa da ta ci, wanda hakan yasa ake mata lakabi da Hajiya Karama, gashi tana da sirri idan ya fada mata A babu mai ji sai idan shi ya umarce ta data fada, babu abunda za tai ba da saninsa ba, babu abunda take boye masa ita da shi abokai ne kuma shakikai.
“Wannan shi ne karo na biyu da ka sauka wani guri ba Masarautar nan ba, and i don’t think hakan zai mana dadi”
A hankali ya busar da iskar bakinsa ya zuba hannyensa aljihu yana cigaba da kallon dokin ta cikin gilashin falon ya ce.
“Abubuwan gidan nan basa min dadi”
“Yeah amman some time muna bukatar shawararka, ko bukatar wani abu kusan kai ne Sarki a gidanan tun da Mai Martaba bashi da Lafiya, be kamata ace kana nisa da gida ba, and the way you act Ammy ba zata jidadi ba”