Fulani Page 14 Hausa Novel
Umma ta mika mata wani ruwan rubutu dake karamin kofi, jiki a sanyaye Falmata ta mika hannu ta karba tai Bismillah da muryar da tasan Umma ba ta ji ba ta shanye, inda sabo da saba da shan magani daga hannun Umma wani lokacin ma a cikin kunu ko madara take kada mata ta mika mata kuma ta karba ta sha, sai dai bata taba mantawa da Bismillah idan zata ci abunda yafi komai batawa Umma rai kenan wani lokacin har hana ta take idan ta ji.
MASARAUTA….
Kowa a dinning din fuskarsa a sake take ana fira ban da Nana wace ta tsuke fuska kamar wata tsohuwa sai wasa take da abincin da ke gabanta.
“Hakan dai be hana ki zuwa makaranta, da ki ci abinci da karki ci duk uwar su daya ubansu daya a gurina, kullum cikin latti kike shiyasa suka aiko suka ce baki zuwa makaranta”
Mama Fulani dake kokarin daukar cup din tea ta kalleta.
“Nana ba ki son makaranta why?”
“Ba makaranta ne bana so ba Mama Fulani auren Sirleem ne bana so”
Murmushi Mama Fulani tai.
“To miya hada aurenki da Sirleem da kuma zancen karatu?”
Ta bata fuska kamar zata fasa kuka bata dai ce komai ba. Shattima ya kalleta kadan ya dauke kai yana kai plantain baki ya ce.
“Gaskiya ne yarinya Wallahi ba ki cancanci auren mawaki ba, yar Sarki Abdallah Umar Jari ace ta auri mawaka ki, abun ai be yi ba”
“Miye matsalar mawaki ne Shattima? Waka ba a sana’a ba ce? Bayan waka kuma ai yana aiki da Unicef ko duk shi din ba aiki bane? He is graduated kasan gaba ina Allah zai kai shi ne? After that yana da restaurant yana da katon Boutique, yana da shagon siyarsa phones and what else kake son ya mallaka kamin a aura masa Nana?”
Ammy na kai aya, Mama Fulani ta wara ido.
“Aa ba laifi gaskiya kuma kin ga yadda yai popular din nan kudi suke samu sosai indai yana da rufin asiri ai ba laifi ta auri abunta”
“Ko dai minene kyaji da shi ba abunda za a fasa idan ka ga an fasa auren nan sai idan shi ne da kansa yace ya janye ba zai aureta ba”
“Haba Ammy sai kace na yi alo ace sai idan shi ne ya fasa Fisabilillahi”
Ta fada tana kara bata fuska. Zainab dake aikin chakuda wainar kwan da ke ba gabanta da fork ta yamutsa fuska tana fadin.
“Matsalar ba wai ta aikinsa ko kudinsa ba ne, matsalar wakar da yake ne be dace ace zuri’ar gidan nan ta auri mawaki ba”
“Daga ke har Shattima wayayyen mutane ne, kin san miye waka ai kina tare da masu yinta, ba photographer ba ce ke miyasa mazan da suke zuwa neman aurenki ba su ce ai ba zasu aureki ba saboda yanayin sana’arki, kuma yarinyar a gaban kowa Mai Martaba ya tsayar da ita ya tambaye ta tana son shi ko irin kunyar da yan mata ke yi ita ba tai ba, tace tana son shi kuma aurenshi za tai, to sai yanzu dan Mai Martaba bashi da lafiya sai ku kitsa mata magana ku ss ta tsane shi ace ni na hana aure? Daman ance ni da yaya mu ke mulki Masarauta, ku dai kawai saboda ba kya son M2 shiyasa kuke wannan abu ita kuma yarinya ce karama duk inda kuka a zata dauka hawa za tai”
“No No Ammy i’m out of this”
Shattima ya fada yana mikewa tsaye tare da ware hannayensa alamar babu ruwansa a ciki ya fita daga dinning are din, Hajiya Karama ma mikewa tai tsaye daman can bata saka komai a bakinta ba tun zamanta gurin.
“Ina da inda zanje ne, ayi breakfast Lafiya”
Daga haka ta bar wajen, sai ya rage daga Nana Sai Ammy da Mama Fulani ne kadai a dinning din.