Fulani Page 13 Hausa Novel
Kamar ta dauki kawar tata ta goya haka ta ji dan dadi, da sauri taje ta bulbula ruwan ta cika bokinta ta kai gida ta sake dawowa ta kara wasu har sai da tai bokiti uku sannan ta hankalinta ya kwanta. Bayan ta aje bokitin a mazauninsa ta nufo kofar dakin Tumba kamar mai labe ta tsaya daga bakin kofa murya can kasa tace.
“Ga ruwan nan na debo”
“To Allah yai miki albarka Fulani ya baki miji na gari”
Tumba ta fada da far’arta, Falmata dai bata ce komai ba dan tasan ba da zuciya daya tai mata addu’ar ba sai dan ganin mahaifinta yana nan, daman can haka take mata a gaban idon jama’a ko kuma a gaban mahaifinta. Dukawa tai ta dauki takardar tsiren ta nufi hanyar dakinsu tana lasar yajin dake jiki, hakan be gamsar da ita ba sai da ta cire wani sashe a takardar dake da mai da yaji ta saka a baki ta tauna ta tsotse ruwan tass sannan ta jefar ta shige dakinsu.
Wani tsohon zanen gado ta dauka ta shinfida saman gadon karar da take bachi sannan ta kashe kyandir din ta kwanta tana karanto addu’o’i kamar yadda ta saba, Naja kam tuni tai nisa da bachin.
Asubar fari Falmata ta fito daga dakin ta dora alwala ta shiga ta fara nafila kamin ta gabatar da sallah Asuba, ta saba da wannan dabi’ar ta yin nafila kamin asuba da kuma addu’o’in safe da maraice da na bachi tun tana karama, duk da kasancewar tana da kananan shekaru hakan be saka ta watsar da koyarwar mahaifiyarta ba, ko kadan Falmata bata wasa da addu’a da kuma sallah akan lokacin komai take zata aje taje tai sallah, idan kuma lokacin addu’ar yamma yayi ko aiki take haka zata rika karanta addu’inta, abun har ya zame mata jiki idan ba tai ba sai ta ji bata cikin natsuwa.
Sai da rana ta fito sannan ta fito daga dakin ta fito harabar gidan ta tattara kayan wanke wanke ta wanke komai tas ta share gidan sannan ta cika karamin bokiti da ruwa ta nufi bandaki, sai ta ta tube tufafin jikinta sannan ta daga wani karamin dutse ta dauko ragowar amon da tai wanka jiya ta saka a soson ta soma wankanta.
Bayan ta gama ta fito tana ta tsanda domin ban dakin a kasa kasa ce ba suminti ba idan kana wanka ruwan dake sauka yana tartsatsin yana sa kafar bandakin ta watso maka a kafafuwa.
Gindin biyar ta nufa ta zauna ta saka dutsen gugar kafafuwa ta goge kafafuwanta tas ta sake wanke su sannan ta shiga dakinsu, bata ɓata lokaci ba gurin shiryawa sanin inda zata je gashi rana ya soma takewa.
Duk da irin saurin da take hakan be hana ta kwaliya ba sannan ta saka atamfa tare da Hijab ta fito cikin sauri tana saka talkaminta na roba.
“Fulani zo ga abincin ki”
Cewar Umma daga gindin murhu da take zaune tana kallon Falmata, abun ka da mai neman sai ga Falmata ta karaso cikin sauri ta cire hijab dinta ta rataya a igiya sannan ta tsuguna taja kwanon da Umma ke nuna mata mai dauke da dumamen tuwo masara.
“Fara shan wannan tukuna”
Umma ta mika mata wani ruwan rubutu dake karamin kofi, jiki a sanyaye Falmata ta mika hannu ta karba tai Bismillah da muryar da tasan Umma ba ta ji ba ta shanye, inda sabo da saba da shan magani daga hannun Umma wani lokacin ma a cikin kunu ko madara take kada mata ta mika mata kuma ta karba ta sha, sai dai bata taba mantawa da Bismillah idan zata ci abunda yafi komai batawa Umma rai kenan wani lokacin har hana ta take idan ta ji.