Fulani Page 10 Hausa Novel
Ta fada da yaren Fulatanci tana haki kukan kuma ya ki ya tsaya mata. Da sauri mahaifiyarta ta aje tasar nonon da take ta nufo inda take ta rikata.
“Yau ko mun shiga uku da wannan lamari haka kullum za yi tai zama? Tafi ki fada ma Malam yana gonarsa”
Ta amsa masa ta yaren da suka fi gwarewa, a take Fadime ta tashi da gudu ya fice daga gidan zuwa gonar mahaifinta, Inna Amo ce ta fito daga bandakin lullube da bakin gane ta nufo tsakar gidan tana.
“Inna Fadime lafiya kike?”
“Nagge ce ta sake faduwa da sannu naggen Malam sai karewa suke Amo
“Allah ya kyauta”
Shine abunda ta fada ta nufi bukkatarta tana koda tsatsagar hakora.
Ko da Fadime ta isa ta fadawa Mahaifinta ya tafi tare da mutunensa da suke aiki tare sun isa a kuraren lokaci domin kuwa tuni saniyar ta mutu sauran kuma na tsaye suna kiwonsu. Faduwa Fadime tai ta dafe kai tana kuka, har sai da Mahaifinta ya tasheta tsaye.
“Haba Fulani komai ai na Allah ne? Ki daina wannan kukan”
“Bappa kullum fa idan na fita kiwo sai Nagge ta mutu, ni kadai take ma haka”
“A a daman can haka Allah ya rubutu”
Ya amsa mata cike da karfin hali, sai daya daga cikin mutanen da suka zo tare da shi dayan ya ce.
“Malam da dai ka daina barinta tana fita kiwo da su”
Malam Jauro yayi murmushi yana girgiza kai.
“A a babu abunda za a fasa, idan mutanen gari sun canfa ta ni ai be kamata na yarda a matsayi ne na mahaifinta, idan Fulani bata ji dadi a gurin iyayenta ba a gurin wa zata ji? Ko da duka sanu na za su kare ba Fulani ba zata daina zuwa da su kiwo ba”
“To Allah Hukkumo sa’a”
Dayan ya fada cikin jin haushin be dauki shawararsa ba. Malam ya dafa kan Fulani ya ce.
“Ki cigaba da kiwon idan yamma ta yi sai ki dawo da su gida, annani?”
“Iyyiye”
Ta amsa masa tana gyara kai har lokacin bata daina hawaye ba, kuma bata san ranar dainawar ba domin wannan matsalar ta shiga cikin jininta ta zauna ta hanata sukuni da walwala duk kuwa da irin ficen da tai a cikin kauye na amsa sunan yarinya daya tilo wacce ta iya turanci kuma ta iya rubutu da karatu a kauyen.
Sai dai wannan abun yasa mutane na tsoronta ga rashin farin jinin da yake damun mahaifiyarta, tun tasowarta har ta girma ta kawo yanzu babu namijin da ya taba nuna yana ra’ayinta balle har ya furta yana sonta, ko irin zuwa dandalin da take sai dai taje wani lokacin dan ta kai sana’arta wani lokacin kuma dan tai kallo, domin ko da ta shiga tai rawa babu namijin da zai mata kari, sai dai tai wasa da yan ‘uwanta mata duk kuwa da irin kyau da Fadime take da shi.
Haka ta zauna a gurin tana kula da shanun har rana ta raba sannan ta nufi sandarta ta dauka ta kora shanun suka nufi hanyar gida tana tafi tana rare wakarsu ta fulani kamar ba ita ce ta gama kuka dazun ba.
Ita ta kanta ta saka shanun a gurin zamansu sannan ta daure ko wanne ta dauki abun shan ruwansu ta debo musu ruwa ta kawo musu sannan ta fita daga wajen.
Bukkarsu ta nufa ta shiga ciki tana cigaba da rera wakar da take tun da ta turo shanun har ta kawo gida, tufafin Fulanin dake jikinta ta cire ta daura zane ta fito tsakar gidan ta dauki wata karamar roba ta nufi tukuyar ruwansu ta debo ruwa a ciki ta nufi bandaki, sai da ta tube tufafinta sannan ta lura da kadangaran dake leke da windin da aka zagaye akai bandaki da shi suna a kai suna kallonta, bayan mutane abu na biyu data tsana yana kallonta kadangaru ne, dan ta lura har wani kada kai suke idan suna kallonta, abun haushi ma kallonta suke ba kakkautawa ko dauke ido basa yi.