Daudar Gora Book 2 Page 73
Karan sigarin hannunsa ya ajiye a ƙyakykyawan ƙaramin bowl ɗin gabansa na glass “Ya akai banyi wannan tunanin ba, ya ALLAH”. Yay maganar yana miƙewa hannunsa duka kan sumarsa ya shiga cakuɗata. Shi dama akwai ruɗewa idan
abubuwa suka masa yawa. Harara Ameera Haifah ta balla masa tana faɗin, (Kai dama ai jaki ba komai kake fahimta ba, shegu biyu burina na cika na kawar da shegen yaron nan kuma bazaku sha ba ai, kubar ganin da taimakonku na shigo masarautar nan, bazaku sha da ga maidani abinda na za na yanzun). A zahiri kam sai ta saki murmushin yaudara. “Kaga zauna Shahan-shan ɗin gobe, kai daɗina da kai ruɗiyar masifa”.
“Bazaki gane ba Haifah, duk yanda kike zato da tsammanin hatsabibanci shegen yaron nan ya wuce nan. Wlhy yace ubansa bai iya komai ba akan taurin kai da shegen kaifi”.
“Duk kaifinsa da taurinsa mune ajalinsa shi da wannan ƴar iskar yarinyar mai bakin reza. Na rasa gidan ubanda suka samota sai kace ƴar ifiritan aljanu”. (Iffah 😂).
“To dama micece inba ƴar ifiritan aljanun ba. Kina gani har yanzu iya bincikenmu mun gagara gano inda tsinannun mutanen nan suke. Wai mu Barrister Akeem zaici ma amana bayan mun yarda da shi”.
“Nifa gaskiya bana tunanin haka, nasan waye Barrister Akeem batun yanzu ba, zaka tabbatar da yana da hujjar ɓoye kansa shima a duk randa ya bayyana kansa garemu. Ai tunda har ya bamu haɗin kan salwantar da iyalan Barrister Abdallah Aas da yake abokinsa dolene ya bada ƙafa. Kai dai mu cigaba da jiransa ɗin, Ni yanzu duk bama wannan ke gabana ba, wannan haukan yayan naka ne, sai kuma ita waccan kuna bibiyar lamarinta da gaske har yanzu shegen bakin nata na kulle dai ko?”.
Nannauyan numfashi Miran Arshaan ya saki, “Boka Barbushi baya aiki ya warware sai in da kansa ya warwaresa, amma duk da haka Inaga zan jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Zan ziyarce a safiyar gobe da safe”.
“Hakan ma yayi, ni bara na wuce dan naga asuba ma na gabatowa.” ɗan riƙota ya sakeyi yana wani ɗan murmushin da kai hancinsa jikinta, murya can ƙasan maƙoshi ya ce, “Ki ɗan ƙaramin lokaci mana, kwana nawa bamma sakaki a idona ba”.
Baki ta ɗan taɓe da janye jikinta tana cigaba da maida kayanta. Cike da muryar yaudara tace, “Nima ina kewar taka ai, sai dai lokacin barina nan ɗin yayi. Kaje ga wawuyar matarka can nasan ta kasa barci saboda kai ƴar wahalar”.
Haka kawai sai yaji zuciyarsa ta ɗan sosu da zagin da akaima Jasrahn yau, duk da ba yau ne karo na farko da Ameera Haifah ke zaginta ba. Baice komai ba ya koma ya kwanta yana ƙoƙarin sake kunna karan sigari. Itama tsaf ta gama kimtsawa cikin kayan ɓadda kamarta, gabansa tazo ta ɗan kamo hanunsa mai riƙe da sigarin ta zuƙa, a fuskarsa ta bulbula hayaƙin, hannu ya kai zai cafkota ta zille tana ƴar dariya ta fice….
(Humm, na san dai masu karatu basu mance wacece Ameera Haifah ba. Itace amaryar Tajwar Haysam mahaifin Tajwar Eshaan kenan. Bari na baku a buɗe. Ameera Haifah dai itace su Miran Arshaan ke yawan ambata da matar nan. Sun santa ko nace Miran Jasim ya santa tun kafin ta shigo masarautar. Dan karuwarsa ce, ko nace shine ya maidata karuwar🤦 . Dan da farko tazo neman taimakonsa ne ya shige mata gaba ta auri mahaifin Tajwar Eshaan marigayi Tajwar Haysam kenan saboda sonsa da take na masifa. Ita kuma ɗiyar wani shahararren mai kuɗi ne Anwarus-sadat, ƴar gata ce ta gaske a gidansu, ta fara son Tajwar Haysam ne lokacin data rako mahaifinta sukai masa gaisuwar salla. Tunda ta gansa ta rikice itafa sai shi, shiko bai taɓa bi takanta ba, a wajen mahaifinta ta amshi number sa, ta dinga takura masa da sakwanni shiko ya share. Iya haukacewa tayi kansa har mahaifinta ya tunkari Tajwar Haysam a lokacin amma ya bashi haƙuri kasancewar Ameera Haifah bata wuce sa’ar Tajwar Eshaan ba ma, acewarsa tayi ƙarama a duk cikin matansa, dan ko Ameera Danish-Ara ta girmeta sosai. Kamar ta haƙura sai kuma ta kasa a wata haɗuwa da sukai da Miran Jasim cikin jirgi, shi da ya ganta sonta yake a lokacin, sai dai kuma ita kafin ya furta sai tazo masa da batun yayansa, wannan abu yay masa zafi, amma da yake shegen kansa ne sai yay mata alƙawarin mallakar Tajwar Haysam amma ta yarda da shi. Masifaffen son ganin ta zama matar Shahan-shan Haysam ya sata amincewa. Kasancewarta ƴar gata babu ƙwaɓa a cikin gidansu ya fara lalata mata rayuwa. Tun kamar za’ai ɗaya a haƙura har ya maidata kamar wata matarsa😭, sai dai da ga ƙarshe yaci nasarar cika mata burinta na zama matar Shahan-shan Haysam da taimakon Miran Arshaan daya shige gaba wajen Malikat Haseenat kasancewar shi ɗan ɗakinta ne. Tunda Ameera Haifah ta auri Tajwar Haysam bata sake yarda da Miran Jasim ba duk da yana mata nacin hakan, ga shi kuma taƙi samun soyayyar Tajwar Haysam shi kuma, baya wulaƙantata amma kuma babu ruwansa da ita, dan takai kusan wata bakwai kafin ya yarda ya kusanceta dan gudun kar UBANGIJI ya kamashi da laifin tauye mata hakki. Duk matansa babu wadda bata kawo masa mutuncinta ba, hakan ya bada gudunmawar jin ya ƙara tsanar Ameera Haifah saboda yanda ya sameta. Da ga nan fa ya tattarata ya watsar ko kallo bata ishesa ba. Itako tarayya da ita da yay sau ɗayan nan taji ta sake haukacewa a kansa. Zamansu sam babu daɗi a tsahon shekara bakwai da suka kasance tare, dan sai tayi da gaske yake haɗa shimfiɗa da ita. Farin ciki kam babu tsakaninsu, dan ko murmushi sai dai taga yanayi amma ba ita ba har ALLAH ya ɗauke abinsa. Bayan barinsa duniya ta koma cikinsu Miran Arshaan a dalilin jin sirrinsu da tayi, a nan ne itama take sanar da su burinta na rama duk abinda Tajwar Haysam yay mata akan Tajwar Eshaan. Daga nanne kuma Miran Jasim ya koma nemanta, a ɓoye kuma tana tarayya da Miran Arshaan shima. Wannan kenan ALLAH yasa dai kun gane dan nidai na zayyano babu ruwana🥱).