Daudar Gora Book 2 Page 46
Bayan ta idar da sallar azhar ta fito domin zuwa gaida Jaddah da Malikat Bushirat da ya kasance dole tayi. Sai lokacin ta fahimci yanda masarautar ke cike. Ashe dole ne duk wani Tajwar a sauran jihohi sai yazo a yau din yayma Shahan-shan barka da shan ruwa, Hakama manyan attajirat da masu fada ajin kasar da dattijai. Zasuci abincin salla da Shahan-shan su kuma tattauna matsalolin kasa da shawarwarin magancewa. Gaba daya sai Iffah taji ta Kara tausaya masa. Dan lallai mulki ba wasa ba, yanda ta sanshi bal son hayaniyar nan yana can cikin takura ne.
Sashen Mallkat Bushirat ta fara nufa yau tawagarta zagaye da ita. Kowa ya kalleta sai ya sake kallo dan kyawun da tai cikin walliyar sallar tata mai tsananin kayatarwa da daukar idanun mat kallo. Ga kyawu da cikin jikinta ya sake sakatayi kamar ka saceta ka gudu. Tako ina hadimar da jami’an tsaron masarautar gaisuwa kawai suke mikawa. Itako fuskarta kawace da murmushi mai sanyi da ke sake saka kaunarta a zukatan talakawan nata masu jin yanzu kam babu kamarta a cikin masarautar bayan Malikat Haseenat da itama ta kasance adalar shugaba
Cike Iffah ta samu sashen Malikat Bushirat da danginta da sukazo mata Barka da salla. Hakan ya mata dadi, dan duk wani wanda ke da alaka da Tajwar Eshaan a rayuwa tana ganinsa da kima da mutunci. Cikin mutuntawa suka tarbeta, dan sakonta da na Tajwar Eshaan yaje garesu har gida a jiya. Duk da suma sun kasance mafi yawansu basu nema komai na rayuwa sun rasaba. Amma alheri dadine da shi, musamman da ya kasance wani abu bai taba zuwa garesu ba ace daga dan yar war tasu kuma Shugabansu. Abinda ya basu mamaki da tabbatar da an samu sauyi yar uwar tasu ma sai da suka zo yanzu duk suke mata godiya har tasan Tajwar Eshaan din wai ya musu aike suma. Murmushin yake kawai ta musu, dan tun jiya dama a tunzure take da abinda Iffah’r tayi. Koda Iffah’r ma ta gaisheta cikin yake ta amsa gain yan uwanta duk sun zuba mata ido.Amma zuciyarta tafasa take da yanda suke ta sanya albarka da yaba abinda Iffah’r tayi, tare da tabbatar da shugabansu kuma dansu yayi dace da mace ta gari mai buda masa hanyar alkairi. Sukam suna farin cikin shigowarta cikin ahalinsu. Wasunsu harda kiranta gagara badau wadda tafi karfin duk wani shedanci a azzaluman masarautar.
Iffah da mur mushi kawal ta dingayi kasa-kasa. Tayi zaman kamar awa guda sannan tai musu sallama akan zuwa anjima zata aiko azo da su su gashe da Shahan-shan. Wannan zance nata na karshe ta sakasu sake shiga jin dadi, dan a cikinsu ma akwai wanda rabonsu da Tajwar Eshaan din tun kan a bar kasar da shi, Kuma uwa daya uba daya suke da Malikat Bushirat din, Sun baje babin hira da sanya albarka ga Iffah Jasrah ha kara basu labarinta. Babbar yayar su Malikat, Bushirat din da suke kira Akia Badiha cikin nuna jin dad) ta furta, “Al ni babban abinda ma ya sakani farin ciki fiye da komai wannan cikin na jikinta, dan zamu samu tsatson alkairi a zuri’armu, ALLAH dai ya raba lafiya”.
Kusan a tare duk suka dubeta. Malikat Bushirat da ke kishingide tana shakar iska da fesarwa harda zabura. Jasrah ce tai karfin halin fadin, “Akia wal waye mai cikin? Kin samu a rudan!” Baki ta Kara washewa, cikin barkwanci ta ce, “Aw to tunda baku ramfo ba ku bada goron albishir tukkanna. Kudi sabbi kal-kal Jasrah ta sauke cikin tafin hannun Akia Badiha, cike da zumudi ta ce, “Muna saurarenki”.
“Uhm wadan nan din ma babu laifi, sai dai da kanku ma zaku karo idan kunji. Insha ALLAHU muna gab da samun Miran, ko Daneen a wannan masarautar. Dan da alama Zawjata-almilk tana tare da shigar ciki”.