Daudar Gora Book 2 Page 33
Kasancewar tsirarun mutane da Tajwar Eshaan ne kawai suka sami damar yin sallar asubahin ya bada mamaki har Tajwar Eshaan ɗin yasa akai tambayar ko wani abu na faruwa ne haka?. Waɗanda suke a masallacin duk basu sani ba, dan haka suka tabbatar da babu komai, sai dai ko makarace ta kawo hakan. Baiji ya gamsu ba, amma sai bai musa ba ya miƙe ya fito Sayeed Fayzul-haq da ya zama kamar amintaccensa yanzu biye da shi. A falo Sayeed ya dakata, shi kuma ya nufi bedroom domin shiryawa ya shiga grm. Dai-dai nan kiran waya ya shigo ta landline. Tsayawa yay cak, dan duk kiran da zai iya shiga a wannan wayar direct dole mai muhimmanci ne da shi ya shafa, kuma kai tsaye ake bukatar magana da shi. Tana gab da tsinkewa ya juyo, idanunsa ya sauke akan sayeed, cike da ƙasaita yay masa nuni da wayar alamar ya ɗaga. Cikin bin umarni sayeed ya ɗaga wayar, shiru kusan na minti ɗaya ya janye a ɗan zabure yana kife wayar. “ALLAH ya ƙarama shugaban sarakuna da al’ummar ƙasar ruman baki ɗaya lafiya da tsohon rai mai albarka. Kirane da ga shugaban jami’an tsaro. An samu accident ne a cikin swimming pool ɗin babban garden, mace ce kuma, ana kyautata zaton bata cikin hadimai, gashi tana buƙatar taimakon gaggawa da basu da hurumin taɓata su”.
Ƙirjinsa ne yay wata irin mummunar bugawa, mafarkinsa na gabanin asubahi da har yasa shi ƴar makara ya shiga maimaita kansa a kwanyarsa. Ƙoƙarin basarwa yay kamar yanda ya saba, sai dai zuciyarsa taƙi bashi goyon bayan bada umarnin waninsa yaje. Har ya daga ƙafarsa da niyyar cigaba da tafiya hakan ya gagara, idonsa ya rumtse da ɗan ƙarfi ya buɗe, batare da yace uffan ba ya nufi ɓoyayyar hanyar da zata sadashi da babban garden ɗin. Sosai mamaki ya kama Sayeed Fayzul-haq, sai dai bashi da hurumin tambaya dan haka ya take masa baya da sassarfa…
★Cikin rawar jiki hadiman wajen suka shiga zubewa bisa gwiwunsu ganin mai ruman ɗin ne fa da kansa. Yayinda jami’an suma duk suka risinar da kawuna. Taku yake a nutse cike da ƙasaitar da ke tabbatar da kasancewarsa bajimin namiji da ko a cikin jaruman gwarazo ne. A ƙirjinsa bugu yake kamar zai hantsilo waje, a zahirinsa kuwa babu mai iya fahimtar komai koda daga fuskarsa ne. A hankali matan da ke zagaye da ita suka dare, dan sune suka sanar cewar Zawjata-almilk ce, shugaban jami’ai ya faɗa a rufe ne saboda shakkar isar da saƙon kai tsaye ga Shahan-shan ɗin. Suma kawunansu duk a rissine suke, cikin rawar murya ɗaya daga cikin matan data kasance amintacciyar hadima mai ƴanci dake da alhakin kaiwa da komowar duk wani abinda ya shafi Shahan-shan da matansa ko makusancinsa (kamar jakadiya a ƙasar hausa) ta ƙarasa zubewa cikin gurfana,
“ALLAH ya huci zuciyar shugaban sarakunan ƙasar ruman da al’ummar cikinta. Umarninka muke jira domin taɓa Zawjata-almilk, dan rayuwarta zata iya salwanta…..”
Idanunsa da ke ma Iffah kallon ƙasa-ƙasa ya ɗan lumshe, cikin jarumtar son danne zillon da zuciyar ke masa ya ɗaga ƙafarsa da ƙyar yay taku ɗaya biyu da ya sake saka matan darewa cikin rawar jiki mamaki na neman halakasu ganin gadan-gadan Iffah ya nufa. Dai-dai yana ƙarasawa ɗaya da ga cikin jami’an wajen da yay wata irin zabura ya sunkuto ɗaya daga kujerun dake a wajen ya dire masa, da sauri aka ɗaura hiramin sayeed Fayzul-haq daya fincike a kansa. A hankali ya kai zaune shanyayyun idanunsa na sake tar-tar a kanta cikin ɗan hasken da garin ya fara. An lulluɓe jikinta da mayafi kasanwar kayanta dake jiƙe zai iya bayyana ainahinta, kallon kusan sakanni biyar yaja numfashi ya fesar yana mai kai yatsunsa biyu saman hancinta, babu alamar numfashi, ɗaukewa yay ya maida a jijiyar wuyanta, nan ma bata harbawa, cikin jarumta da zaburo da sanyin da ke sauka a jijiyoyin jikinsa ya ɗan ɗaga mayafin ya ciro hanunta. A kan tattausan nasa ya ɗaura yana mai ɗaura yatsansa akan jijiyar tsintsiyar hannun ya lumshe ido. Da sauri ya buɗe sai dai ga mai kallo bazai taɓa fahimta ba.
Dan a nitse yake sarrafa hannunsa dake motsi kawai a jikin nasa. Shugaban jami’ai da Sayeed Fayzul-haq dake ɗan satar kallonsa kasancewar duk wani hadimi da sauran jami’an tun zamansa a kujerar duk sun juya bayansu suka ɗan waro ido ganin ya kusanta ƙyaƙyƙyawar fuskarsa da ta Iffah har hancinansu na gogar juna. Ya lumshe idanu tare da sauke tausasan lips ɗinsa kan nata, ai dole suma suka sake rissinar da kawunansu duk da sun san bawani abu zai yi ba illa bata taimakon gaggawa